← Book details Uncle Ne Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 40 OF 87

Sashe 40

Uncle Ne Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Mama ta kalli Abbou tace "eyee haka akai bani da labari Kabeeru?, yaushe kai ma ka zama sallamamme wanda bai son laifin yaransa? Fisabilillahi ace samari manya kuma ƙarti a gidanka amma kaƙi aurar dasu, a'a wlh wannan sangarta ce ban taɓa ganin inda akai wannan abun kunyar ba,da ƙauye ne duk suna da yara ƴan dugui dugui gwanin sha'awa"
Kafin Abbou yace komai Mameey tace
"Eyee! mata aka samawa yaron namu babu labari Abbou Jalal?"
Da ido Abbou ya kalleta ba tare kuma daya bata amsar maganarta ba ya kalli Mama yace
"Kiyi haƙuri in sha Allah da zarar komai ya lafa duk zasu lalubu matan auren"
Taɓe baki Mama tayi tace
"Dadai yafi,amma shi wancan basa mudan ai sai dai a sama masa,dan naga alama kamar ma tsoran matan yake,bazai iya tsayawa da mace har yace yana sonta ba,oh ohhh ohhhh banda ma zamani ina zaka kalli indon mutum kace kana sonsa kuma ya tsaya ai sai gudu,amma yanzu abin naga kamar wani gasa ne,haka jiya a talabijin naji ana ta faÉ—ar wani abu kai abindai sai dai su, hadda runguma fa"
Ta faɗa tana ɗan saka hannunta a haɓarta alamar mamaki
Murmushi Mummy tayi a zcyarta tace
"Tsofa labari"
A fili kuma tace
"Mama wannan ai ɗari'arsu ce haka,kinga Film ɗin hausawanmu babu haka,so ko wanne yare aƙwai al'adar su da kuma ɗabi'ar su,da ga Kennywood ɗin zuwa India duk daban daban ne"
Mama ta ya tsuna fuska tace
"Tirr da wannan É—abi'ar mutane kamar tsirara" kafin ta kuma kallon Abbou tace
"Yawwa! Nace wacce mata ka zaɓawa Jalalun?"
Miƙewa Abbou yay ganin lokacin masallaci ya kusa yace
"Wata ce,soon za kiji komai ai"
Mama ta kwaɓe fuska tace
"Meya suun kuma?"
Aryan yay dry mai yawwa kafin yace
"Wai da wuri,ai Abbou daka faÉ—a mana domin mu fara shirin ganin Antyn tamu wacce tayi dacen samun zan kaÉ—eÉ—en saurayi irin yaya"
Abbou bai ƙara magana ba sai kallon Jalal da yay wanda ko inda suke bai kala ba bare su saka ran zai tanka maganarsu yace
"Muhammad lokacin masallaci yayi fa"
Idanunsa ya buɗe tare da saukesu akan Abbou bai ce komai ya miƙe tare da nufar part ɗinsa, Mama tace
"Allah É—aya gari babban"
Sarai yaji maganarta amma yay gaba abunsa, Aryan ma miƙewa yay tare da shigewa nasa part ɗin ya rage daga Mama sai Mummy da Mameey, Mameey tace "Mummyn Jalal me za'ai a gidanne yau?"
Mummy tace
"Haba Mameey duk abinda kikai dai-dai ne,tunda yau friday duk samarin gidan suna nan"
Kai Mameey ta É—aga tace
"Bari naje wajan Laure idan yaso taje anjima ta shigo,kin san indai tasa hannu to Jalal da Abbou Jalal baza su ci ba"
Tana faÉ—in hakan ta nufi hanyar kitchen Mummy kuma tayi upstairs part É—in su Jalilerh.
Jalal na shiga part ɗinsa ya nufa cikin bedroom kai tsaye ya shige cikin bathroom yana zare ƴar ƙaramar singlet ɗin jikinsa da kuma wando three gaiter daya saka, shower ya sakarwa kansa yana mai lumshe idanunsa,maganar Abbou ce ta faɗo masa,mai yasa har yanzu babu wanda yake ƙoƙarin fahimtar abinda yake damunsa ne? Mene yasa har yanzu babu wanda zai iya tararsa ya tambaye sa dalilin yasa bai son yin aure? Ko kuma hakan da akai masa yana nuni da suna son suga hankalinsa ne? Wa zai aura? Zata iya fahimtar sa kamar yadda ya fahimci kansa? Zata iya zama dashi a haka? Ko kuma ba zata iya ba? Wanne kallo zatai masa idan ta san bazai iya biya mata buƙata ba?zata raina sa ko kuma zata tausaya masa ne?mene dalilin daya sanya za'a takura rayuwarsa akan yay wani aure ne?
Yana da tabbacin sun san shi ba yaro bane indai yana buƙatar aure zaiyi ba tare da an takurasa ba
Babu wanda ya isa ya sanya shi yin aure ba tare da yay niyya ba,
Koda an tilasta shi yay auren, tabbas matar zata zama kayan wanki ne wanda basu da ranar wanke wa,
Iska ya fesar mai zafi ta cikin bakin lokacin guda yanayinsa ya sauya, shower ya kashe,tare da yin brush ya ɗaura alwala,yana fitowa ya nufi dressing mirror lotion ya shafa mai ɗan sauƙin zafi, tare da fesa body spray a saman fresh skin ɗinsa,wajan wardrobe ya nufa wata shadda majic ya ɗauka mai kalar sky blue tare hula mai kalar light blue,cikin sauri yake komai sbd ganin lokacin na neman yanke masa,black half shoe ya sanya,tare da ɗaukan paryaer mat ya fita a ɗakin
Yana fita parlour yaga babu kowa kai tsaye ya shige part ɗin Mama zaune ya sameta tana faman daka goro, a kanta ya tsaya tare dayin shuru yana tunanin ta inda zai fara,dan idan yace cikin ɓacin rai zai magana za'a iya samun matsala sbd gaba ɗayansa jinsa yake a sama zcyarsa banda tafasa babu abinda take,ba yajin a yanzu zai iya control kansa amma ya zame masa wajibi daya saita kansa, Mama ta taɓe baki tace
"Ayee mama ayeee mama mayeee iyeee,ayeee mama labu labu mama yeee iyeee"
Haɗe rai shima yay kafin yay ƙasa da murya yace
"Ina yini"
Cikin ƙufula Mama tace
"Kaji ance bani da lafiya ne Muhammad? Da ban yini da lafiya ba aida ka samu labari wajan ubanka"
Cije lips yay kana ya zamu daga saman sofa yace
"Haba matar,laifin me mijin yayi ne"
Taɓe baki tayi tare da watsa dakakken goran a baki tace
"Uhmm duniyyanci kenan,Ni za'ai wa sanabe"
Zamuwa yay daga saman sofar gaba ɗaya ya ƙarasa inda take zaunan ya cire hular kansa tare da ɗura kan a saman cinyarta,shuru tayi tana ɗan sauke ajjiyar kafin tasa tafin hannunta a saman sumar kansa ta shafa a hankali tace
"Nayi kewar jikana kuma mijina"
ÆŠago kai yay tare da zubawa Mama Idanu wajan 3minutes yace
"Mama mene yasa kikeson dole sai nayi aure ne?"
Washe baki tayi tace
"Kai ɗaya kai ne jikana na miji,sai ƙaramar ƙanwarka Ina son naga ka sama min yara,ina da burin naga ka tara zuri'a masu yawan gaske kuma masu albarka,bana son yadda ban tara iyali ba ace kaima haka tara ba,wannan dalilin ya sanya nake burin naga kayi aure kafin ƙasa ta rufe idona,kullum cikin mafarkai nake wanda bana gane kansu ina jin tsoro dan ban san dalilin wannan mafarkan ba,kaji dalili nason naga ka ajjiye zuri'a"
Ɗago jajayen idanunsa yay yana mai kallon Mama, lokacin guda zuciyarsa ta bada sauti damm Tabbas asiri sa yana gaf da tunuwa, rauninsa yana shirin bai yana abinda ko a mafarki baya fatan ace hakan ya kansace,abinda bashi da ikon faruwarsa haka kuma bashi da ikon hana faruwarsa, ƙaddara juyi juyi ce tana maida mai ƙyau ya zama mara ƙyau ko kuma ta mayar da mara ƙyau ya zama mai ƙyau,yana da yaƙi nin tasa ƙaddarar zata juya daga mara ƙyau ta dawo mai ƙyau,yaushe? Da wanne lokacin? Shine abinda bai sani ba,runtsa idanunsa yayi yana sauraran bugun zcyarsa dake fita da sauri da sauri wayarsa take cikin aljihu ce ta fara ƙara, miƙewa yayi sbd yasan kiran daga wane kai tsaye ya fice daga ɗakin idanunsa rufe, Mama ta bisa da kallo tare da tafa hannayenta tace
"Ohhh ni Abu ina za'a biyewa wannan yaron,dole sai an nema masa taimako ƙilan wata baƙar aljanarce ta aureshi..,"
Sai kuma tasa hannu da sauri ta rufe bakinsa tana juyawa tare da ƙare wa ɗakin kallo tamkar wacce taga aljanar a gabanta.

A main parlour ya samu Abbou tsaye shida samarin gidan,kamar haÉ—in baki duk shadda iri É—aya suka saka babu bambanci hadda Abbou.

Imran yace
"Abbou lokaci na tafiya" gaba Abbou yayi Irfan da Imran suka take masa baya sai kuma Aryan na ukunsu,har suka fice daga cikin gidan Jalal na tsaye yana kallon su, Irfan ya kula Jalal bai taho ba ya juya baya a hankali ya hangesa yana tafiya lokacin daya iso wajan har sun shiga mota, Aryan a motar sa da Imran a gaba sai Irfan a bayan motar, Jalal shi kuma ya nufi motar da Abbou ya shiga ya zauna a back seat kusa Abbou,sai kuma motar securities ɗinsa ta rufa masu baya,misalin 1:30 suka isa harabar babban masallacin juma'ar jama'a sai ɗagawa motar Jalal hannu suke, yana daga cikin motar yake kallon kowa ɗai-ɗai har suka ƙarasa wajan parking,sahun farko Jalal ne tsaye bayansa kuma ƴan uwansa gefensa kuma Mahaifinsa a haka sukai sallar har aka idar,ana idarwa kowa ya fara tashi, Abbou hannun Jalal yaja suka nufi ƙofar baya sabida dubban jama'ar da suka tare ƙofa suna jiran fitowar sa,a haka suka ƙarasa wajan motocin su ba tare da angansu ba,kai tsaye suka nufi gida,tun a hanya aka fara sakin breaking news a gidan t.v da gida redio akan

_Governor Muhammad Jalal Kabeer bobo mai neman takarar kujerar Gwamna a jam'iyyar D.R.P ya hallarci sallar juma'a shida danginsa_

A ka rubuta hakan tare da photonan sa dana ƴan uku, da yawanci photonan wasu ne sukai masa a wajan,duk halin da yake na ƙunci da rashin sukuni bai hana shi yin wani lafiyayyan murmushi ba,hannu yasa yaja sajen fuskarsa kana yayi baya tare da lafewa jikin kujerar yana sauke ajjiyar zcy.
Chapter 40 · 0% Book details