← Book details Uncle Ne Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 66 OF 87

Sashe 66

Uncle Ne Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*Nimcyluv* 7/22/21, 8:02 AM - Buhainat: _96-97_ Zanyi mulki cikin jajircewa da kuma zaƙwaƙuranci,nayi al'ƙawari da littafin Ubangiji cewa babu wani rai da zanci ZARAFI ko kuma na tauye masa haƙƙinsa,nayi al'ƙawari kuma zancika alfarmar Annabi da Kur'ani"gaba ɗaya wajan aka sanya tafi wasu kuma sukayi kabbara, lumshe idanunsa yay yana jin wani mai girma ya hau kansa,yasan rantsuwarsa bazai taɓa sanyawa yaci abinda yay al'ƙawari ba,sai dai kawai ya roƙi Ubangiji akan ya taimake sa,ya bashi ikon cika al'ƙawarin daya ɗauka akan talakawan sa, Cheap joji ne ya amshi Kur'ani ya miƙawa wani,kana ya rataya wa Jalal wani abu a wuya daga nan aka shiga ɗaukan photonan,gidan TV kuma suka shiga ɗaukan vedio,gidan redio kuma suka shiga ɗanar recording na abinda ake,bayan nan wajan bawa Jalal key ɗin office a tafi,sabbin securities,sabbin motocin,sabbin ma'aikata,sabon gida a cikin gidan gwamnati,sosai akai shagali,kana taro ya watse su Abbou suka dawo gida cike da farin ciki,hakama Jafar da ƴan Uku zana dawowa gida aka fara shirin dinner ɗin da Jafar ya shirya domin taya Jalal murna,sai dare za'a gabatar da dinner ɗin a babban event, shirye-shirye su Mameey suka fara, shigowar ta kenan ta samu Laure ita da Mama da kuma sauran mutane da suka zo tayasu murna,suna zaune sai cin abinci take, Mameey ta kalli Laure tace "Jalilerh ta sauko kowa?"Laure tace "wlh hajia bata sauko ba,sau biyu ina zuwa dubata sai naga ƙofar a rufe"kafin Mameey tai magana Mama tayi saurin faɗin "mu dai har yanzu bamu gama sanin zuciyar yarinyar nan ba,banda baƙin ciki yarinyar ƙirmishishi kije wannan taron nan amma ta murzawa idanunta toka, meye wannan da tayi?yaya sunansa? a'a wlh baƙin ciki kawai takewa Jalalu,yaro ɗan marayan Allah ya ɗauki rimi² domin gyara gobenki,amma ki watsa masa ƙasa a idonu,to Wlh nidai babu ruwana,idan ba baƙin ciki take gwamma musani tun yanzu ko ba haka ba?"Mameey tace "ayyya ba haka bace Mama,kinsan bata jin daɗi ne shiyasa"wani kallo taiwa Mameey sheƙeƙe kafin ta yatsuna fuskarta tace "au haba?" Mameey tace "eh wlh,sai amai take ga zazzaɓi" nama ta tura a bakinta kafin ta haɗiye da ƙyar tace "banda kema kin zama sallamammiya ina ke ina biyewa wannan Salamatu?wlh fita a idona tun tuni na rufe,yanzo dan waye ya kejin daɗi a wannan rayuwar ta yauma ta komu? to ai shikenan nan tunda kema kin zama sakarya,yarinya baƙin hali fal zuciya,ga shegu aljanu irin na gado kai ita dai abu goma da ashirin,bai laifi kuma tana da ƙyau abinta shiru² da ita gwanin sha'awa,to waya sani ko ƙyan ɗan maciji ne?"ita Mameey ba tace komai ba ganin abin na Mama ya fara zama shiririta yasa ta haura sama tana ƙunshe dryar dake cinta,da wani kallo Mama ta bita kafin ta juyo wajan wata ƙawarta tun ta yarinta tace "to ga ta nan dai Asabe,kinga tun daga haihuwar ƴan ukun nan shikenan haihuwar ya tsaya,kila juya da Za'ai sai Allah ya taimaka" tsohuwar da aka kira da Asabe ta ajjiye ƙashin da take ta faman tsotsa tace "na sai wani kallon tara saura take mana ai.." Mama ta miƙe tsaye tace "a'a wlh kedai anyi natsoraciya,me yasa baki gayan ba sai da ta tafi,nidai banji daɗi ba,meye nata da zata yi maki harara?bayan itama aurota a kai,ai anjima ƴan uwanta zaso sauka akan su zan rama maki" haka dai sukaci gaba da surutai irin nasu na rikitattun tsofaffi,kafin su sanya Laure ta kawo masu farfesun kan ragon da akai, Mameey na shiga part ɗin su Jalilerh ta tura ƙofar a hankali,a ƙwance ta sameta ta kifa kanta cikin pillow tana sauke ajjiyar zuciya,jin alamun mutun yasa tayi saurin ɓoye photon Jalal dake hannunta,kana tai lamo kamar mai bacci, ƙarasawa cikin bedroom ɗin Mameey tayi tace "daughter har yanzo jikin ne?"shiru Jalilerh tai mata tai kamar bacci take, ganin haka yasa Mameey taja mata ƙofar ta,tana fita Jalilerh ta sauke ajjiyar zuciya tare da lumshe idanunta wasu hawaye Masu zafi suka shiga fita daga cikin idanunta,a hankali kuma ta zaro photon Jalal wanda ta ɓoye a ƙasan pillow,gaba ɗaya a ɗan kwanakin nan ta rasa mene yake damuwa da ita,bata da aiki sai tunaninsa,a duk sanda kuma akai maganar sai yaji zuciyarta ya buga da ƙarfi,kullum cikin damuwa take,duk sanda ta matsa zuciyarta domin ta gane abinda yake damunta da kuma abinda ta keso,sai taji zuciyarta kamar zata fito waje,abu ɗaya yake sanyawa taji daɗi idan taga photon Jalal, zuciyarta nayin daɗi taji damuwarta ta yaye,tana nan ƙwance lamo har Nihila ta shigo, da sauri ta ɓoye photon tare da lumshe idanunta,kallonta Nihila tai sai kuma ta taɓe bakinta ta nufi cikin bathroom domin sake sabon wanka,sai wajan biyar na yamma sannan motocin Jalal dana securities ɗinsa sukai parking a harabar gidan, buɗe masa ƙofa akai ya fito yana tafe yana baza babbar rigar jikinsa yana ɗan haɗe ƙafafuwan sa,kansa a ƙasa bai yadda sun haɗa idanu da kowa ba,a main parlour ya samu Mama da wasu tsofaffi,kamar bazai magana ba sai kuma yace "sannunku" Mama take faman jan dafaffiyar ganda tace "mene kuma sannu?a gadon asibiti ka ganmu?ko kuma labari ka samu bamu da lafiya? a'a wlh wannan ai gaisuwar raini ce,meye sannu ana zaman lafiya,kama rasa a ina zakimin wulaƙanci sai gaban ƙawaye ne?to uwarka salamutu ita kaiwa bamu ba"Asabe ce tai saurin zungurar Mama tace "a'a wlh babu ruwana yanzu saiya saka a kullemu a bayan sel babu ruwansa,ba gwamna bane?" Shiru Mama tai tana rarraba idanu tace "to me nace kuma? Allah ya baka hqr kada ka ƙullace ni faɗa na nema ba"girgiza kai kawai yay yana shigewa cikin part ɗinsa,yana barin wajan Mama tai ƙasa da Murya tace "yanzu Asabe duk yadda muke da Jalalu sai ya saka a kamani?kinga fa nina haifi uwarsa,uwarsa kuma ta haifesa ai na huce cin mutuncin a wajansa" Asabe tace "kedai bar yaran zamani,yooo ko uwarsa tayi ba dai-dai baya kulleta ba,bare ke kakarsa, Gwamna fa akace maki ba kansila ba"shiru Mama tayi kafin tace "to dai Allah ya basa hqr,Ni banyi da wata manufar ba wlh"Jalal na shiga part ɗinsa ya shiga zame kayan jikinsa na ajjiye su cikin wardrobe a wani side na datti clothes,ya rage daga shi sai boxer,wajan fridge ya ƙarasa ya ɗauki malt, harya juya sai kuma ya koma ya ajjiye sbd tunawa da azumin da yake, parlour ya dawo ya zauna tare da miƙar da ƙafafuwansa,lumshe idanunsa yay lokacin da sanyin a.c ɗin ya rasa cikin saman farar fatarsa, hannunsa yasa ya ɗauki remote kana ya kunna cenema ɗin dake ɗakin, series ɗin Joda &Akbar wanda ake haskawa a zee world,idan kagansa zaka ɗauka da gaske kallon yake, amma a zahirance tunani ne fal cikin zuciyarsa,ya rasa me yake damunsa,duk iya kacan rayuwarsa bai taɓa jin sha'awar kasan cewa da mace ba,bai taɓa damuwa da zama da mace a matsayin mata ba,sbd abinda ake so a auran shi kuma bashi da lafiyar yinsa,tunda yake sha'awa bata taɓa damunsa, sai dai yaji Jafar na faɗa, kasancewar shine kaɗai abokinsa,kuma amininsa bashi da wani sama dashi,amma gashi yau shine yake son kasacewa da mace, yasubuhanallah! Wannan wanne irin abune ya samesa?wacce kalar masifa face haka? kumshe idanunsa yay yana taune lips ɗinsa,yana nan zaune har lokacin magrib ya kusanto,tashi yayi tare da kashe kallon ya nufi cikin bedroom ɗinsa,yana shiga ya huce bathroom ya sakarwa kansa shower,wanka sosai yay tare da ɗaura alwala, fitowa yay sanye da bathrobe a jikinsa,wajan dressing mirror ya tsaya,ya shiga gyara jikinsa sai da ya gama shafa lotion mai ɗan ƙamshi kana ya fesa parfume,comp ya ɗauka ya gyara sumar kansa ta kwanta sosai gwanin sha'awa,ganin yana da sauran lokaci kafin dinner ɗin yasa ya ɗauki farar jallabiya mai ƙyau kuma mai ƙaramin hannu, Wannan ko hiramin da yake sanyawa bai sa ba,haka ya fita daga part ɗinsa yana zabga ƙamshi,a parlour'n ya tarar da Abbou da ƴan uku,kallon parlour'n yay yaga tsaf sai ƙamshi yake a juna borner turare na fita ta cikinta kamar ba wanda su Mama sukaiwa kaca-kaca,kansa a ƙasa ba tare kuma da yay magana ba yabi bayan Abbou ganin yay gaba,suma ƴan uwansa suka mara masu baya,suna zuwa Masallaci Jalal ya tsaya sahun farko mai makon ya ƙarasa wajan da yake tsaiyawa wanda aka tana da domin liman,kallonsa kawai Abbou har zai magana sai kuma ya fasa,wanda yay magana har wani magidancin mutum yazo wajan ya tada sallah,bayan an idar da Sallah kowa ya ƙara taya Jalal murna tare sayi masa addu'a na tsari da kuma fatan alkairi,murmushin dole yake yana amsawa da "Ameen" bai tsaya karatun da yake masu ba yace suyi masa uzuri,suma basu takurasa ba haka ya tsallake su Abbou ya nufi cikin gida,a parlour ya samu Mameey tana ganinsa ta saki Murmushi tace "ur excellence Barka da shan ruwa" ɗan kwaɓe fuska yay ba tare kuma da yace komai ba, Murmushi ta ƙarayi tace "yanzu na kammala yi maka abun buɗe baki,nan zaka tsaya ko part ɗin ka za'a kawo maka?"girgiza kai yay yace "no bada a kawo min" tace "okey!amma baby bata nan,wai taje makeup ne, nace ta bari na kira har gida ai mata daga nan aiwa daughter amma tace a'a"lumshe idanunsa yay kafin ya buɗe yace "no wahala,bawa wacce kike magana ta kawo min" kallonsa tai tace "wa kenan?" Ɗan juya idanunsa yay sbd ciwon da mararsa take masa kafin ya fesar da numfashi yace "ina ba baby ce ɗaya a gidan ba?"Murmushi kawai tai masa kafin tace "daughter bata ta jin daɗi,domin ko dinner tace ba zata ba,kuma yanzo tailor ya kawo masa ɗinkin su"juyawa yay bai ƙara magana ba,har yaje ƙarshe ya tsaya yace "ki bata ta kawo min" yana faɗin haka ya shige cikin part ɗinsa, Mameey upstairs ta haura tana zuwa ta shige part ɗin su Nihila,a a zaune ta sameta tana goge dugun gashin kanta,da alama fitowar ta daga wanka kenan, kallonta kawai Mameey keyi tana mamakin tsarin halitta mai ƙyau da ɗaukan hankali irin na Jalilerh,ko ita da take babba baza ta taɓa nuna mata hips mai ƙyau da girman brest ba, komai nata mai ƙyau ne,ganin yadda take abu a sanyaye yasa ta ƙarasa wajanta tare da amsar handrayer ɗin,da sauri ta juya sbd tsoran da taji, ajjiyar zuciya ta sauke tare da sunkuyar da kanta kuma bai tace komai ba,
Chapter 66 · 0% Book details