← Book details Uncle Ne Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 53 OF 87

Sashe 53

Uncle Ne Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

By
NIMCYLUV
7/6/21, 8:52 AM - Buhainat: UCL NE
_80-81_
A gsky lamarin aƙwai abun dubawa,ina yare na haifi ɗa a kirasa da shege,nikam ba zan iya wannan ɗan yan aikin ba,cin amana ido biyu"zubewa nayi a ƙasa tare da dafa ƙafafunsa ina kuka kamar raina zai fita nace "ka taimake ni,kayi min rai babu wanda zan iya tunkara da buƙata ta sai kai,kai ne ka cancanta da kazama uba ga ɗan da zan haifa,bana da wani ƙata kuma burina bai huce ɗan da zan haifa ya samu kyakkyawar mu'amala a wajan Jalal ba,a yanzu burina bai huce na sama yarinya mace ma wacce zan haɗa ta Jalal domin ya zama garkuwa gareta,ina da tabbacin bazai taɓa bari jinina ya hulaƙanta ba sai iya rasa komai akan ya rasa ɗan dana haifa,kaga idan har Jalal na raye Lamir bazai taɓa samun nasarar cutar da ita ko shi ba,dan Allah ka taimaka min Please" na ƙare maganar ina ƙara sautin kuka na,shuru Alhaji khamal yay,ban san mene yake tunani ba sai kawai naji yace ya "amince amma bisa sharaɗi guda"da sauri nace masa "sharaɗin mene?" Kallonta yaga da gaske take buƙatar abinda take mgn shi gaba ɗaya abun kamar almara,sai kuma yace "idan har kin samu yarinya mace dole ne ki haɗa auranta da Jalal,domin kin san idan ba shi ba,babu yadda za'ai wani ya AURETA musamman idan aka tabbatar shegiya ce...,"shuru yay yana jin kalmar nayi masa zafi a ransa kafin ya ɗura da "idan kuma namiji aka haifa dole ki bawa Jalal riƙon sa domin ni bazan iya ba"banyi tunanin komai ba nace na amince,shuru Mummy tayi da bada labarin idanun na janyewa wata farar kumfa ta fara fita daga cikin bakinta alamar dafara mutuwa tazo gangara, Jalal rasa abin cewa yay sai kallon Nihila yake wacce take ta zabga kuka tare da ihu Mameey ta riƙe ta,runtsa idanunsa yayi zuciyarsa nayi masa zafi komai na kansa ya kunce yana rasa tudun dafawa,da sauri ya buɗe idanunsa sabida wata miƙa da Mummy tayi ta ƙanƙame Jalal,da sauri ya riƙe ta idanunsa ya kaɗa yay jajirrr,cikin sarƙewar numfashi Mummy tace "tun daga wannan ranar muka fara mu'amala da Alhaji khamal,idan ba zaka manta ba ina ce maka zani asibiti to a zahirin gsky bawai asibitin nake zuwa ba, lokacin dana fahimci ina juna biyu sai na sanarwa da Alh khamal kuma tun daga ranar na ɗauke ƙafata ban ƙara zuwa inda yake ba kamar yadda shima bai neme ni ba,cikina yana da wata baƙwai nayi scanning aka tabbatar da mace zan haifa sbd murna sai da nayi sadaka,bayan haka da sati guda wata rana nace gida na samu Lamir a cikin bedroom yana faɗin _ni dai burina bai huce naga na samu kuɗi masu yawa wanda za'a dinga ƙwatance dani ba,shuru naji yayi kafin yace okey idan wannan ne babu matsala dama na taɓa gaya maka tana da ciki yanzu haka gaf take da haihuwa kuma naji ance mace zata haifa kaga abun yazo mana a dai-dai,ni kuma zanta jira har yarinyar ta girma wannan shine kawai_ bayan naji haka da sauri nabar gidan gabana na faɗuwa domin ban san wanne abu ya shiryawa ɗan ciki na ba,kullum cikin fargaba nake da zullumi haka dai naita addu'a ina neman tsari har na haifi baby a ranar dana haifeta ne kuma naje wajan boka domin ya ƙara rufe min bakinka sbd kada ka tambayi yaya akai na samu ciki bayan bamu taɓa tarayya dakai ba,bayan Jalal ya dawo a kuma airport mgnarsa ta farko inda yake cewa _dama za'a bani aurenta_ shi kaɗai ya tabbatar da cewa Jalal yana son baby kuma na ƙara godewa daya bani shi a matsayin ɗan ƴar uwata,tun kuma daga ranar na fara rashin lfy bana faɗawa komai koda naje asibiti aka shaida min Zcyarta ta kamu da ciwo banyi mamaki ba domin yadda damuwa tayi min yawa kullum cikin kuka nake da tunani nasan hakan zai iya faruwa dani" kallon Jalal tayi kafin ta kama hannunsa ta riƙe sannan ta kalli Nihila tayi mata alama da tazo da sauri ta zame jikinta daga na Mameey ta ƙarasa wajan gadon kusa da ita ta zauna,hannunta ta riƙe kana ta sanya cikin na Jalal ta haɗe hannayensu waje guda tace "Wannan amanace gareka ko bayan babu raina,ina fatan zaka ƙarasa cikamin burina ta hanyar auran Nihila,nasan zaka zama inuwarta zaka zame mata Garkuwa,zaka bata dukkan kulawan daya dace,ina da tabbacin ba zaka taɓa barinta tayi kuka ba,nasan ba zaka taɓa bari wata halitta ta cutar da ita ba indai kana raye,dan Allah dan Annabi Jalal ka auri Nihila ka zama nagartaccen miji gareta ina fatan zaka cikamin wannan burin nawa ka kareta daga sharrin maƙiyanmu" wata zuface ta shiga karyowa Abbou kansa ya shiga sarawa,abu goma da ashirin suka taro waje guda sukai masa yawa,da rashin asalin da yake dashi ko kuma da cin amanar da Mummy tayi masa?ko kuma da rashin mahaifiyar Jalal wanda rashinta yake damunsa a yanzu,wato wannan dalilin ya sanya Alhaji khamal yake ƙin haɗa idanu dashi, wannan dalilin yasa sanda yake masa da tasa buƙatar ya tsaya yana masa wani surutai akan hakan bai dace ba,ya tsaya zuwa wani lokaci,da sauri ya juya sbd jin abinda Mummy tace "Bana da bakin da zanyi maka mgn,sannan bana da bakin da zan nemi hafiyarka,amma tun a sali ban aureka domin ina sonka ba,haka kuma bana jin tsanarka a Zcyarta,dan Allah kaji tausayina ka yafemin nasan ni me laifi ce a GAREKU,amma babu yadda na iya garin ceton wasu rayukan nima na jefa kaina ga halaka,dan Allah Abbou Jalal ka yafe min kace ka yafemin kada na tafi lahira da haƙƙinka a kaina,yafiyarka nake nema" kasa cewa komai Abbou sai kuma ya ɗaga kai ya kalli Jalal shima kallonsa yay yana son yaji abinda zai ce,ganin bashi da niyyar magana yasa ya langwaɓar dakai tare da ɗan haɗe hannayensa alamar roƙo, ɗauke kai Abbou yay idanunsa na kawo ruwa yace "babu komai Allah ya yafe mana baki ɗaya Ubangiji ya baki lfy"Murmushi jin daɗi tayi kafin ta kalli Nihila tace "am so sorry my blood,na maki laifi na samar dake ta hanyar da bai dace ace an samu dukkan wata yarinya ko yaro ba,amma zanan ƙaddararki ne haka kuma Ubangiji ya nufa ta haka za kizo,ina neman alfarmarki da kiyafewa mahaifiyarki ko zata samu sauƙin tafiya lahira" cikin kuka Nihila ta riƙe hannun Mummy tace "dan Allah Mummy ki dana faɗin haka ni ba kiyimin komai ba,dan Allah ki tashi haka mutafi gida"ta ƙare maganar tana sakin wani sabon kuka,hannu Aryan yasa ya ɗauke ta daga jikin Mummy, numfashinta ne ya fara fita idan ya fita kuma baya dawowa cikin ƙasa da murya Jalal yace "fita da ita" jin haka yasa Nihila ta ƙara fasa wani kukan tana kiran sunan Mummy,hannun Jalal Mummy ta ƙara riƙe wa tace "idan Allah ya nufa mahaifiyarka na raye kuma Ubangiji ya ƙaddara saduwarku ina son ka nemar min yafiyarta"tana faɗin hakan ta fara miƙa idanunta ya shiga ƙafewa,da sauri Jalal ya shiga faɗin "La'ilaha illallah Muhammad Rasulullah S.w.a³" gaba ɗaya mutanan room ɗin suka shiga maimaita hakan lokacin hankalinta ya fara ficewa sai faɗin "Jalal ga Nihila,bobo Nihila ga baby nan" murza hannunta ya shiga yi yana ɗan ƙara sautin muryarsa cikin sarƙewar numfashi itama ta fara ambaton kalmar shahada kafin tace "Muhammad Rasulullah s.w.a..La'ilaha illallah..," cak numfashinta ya tsaya yayinda computer itama tai shuru da kukan da take sai kuma wani gudan jini daya fita ta cikin hancinta,runtsa idanunsa yayi tare da kifa kansa a ƙirjin Mummy ya shiga sauke numfashi tare da sauke wasu tagwayen ajjiyar zcya, Mameey ce ta saka kuka ta kiran sunan Allah tare dayin sallati Abbou kallon Mummy yake yana ganin mutuwar kamar almara,gaba aka rasa mai ƙwaƙƙwaran mutsi a cikinsu, Jalal kowa har yanzu yana ƙwance jikin Mummy yana ta ajjiyar zcya,ganin babu wani lokaci yasa Abbou ya ƙarfafa zuciyarsa ya miƙe tsaye tare da ƙarasawa inda Jalal yake zaune ganin yadda ya ƙanƙame gawar Mummy yay a hankali ya saka hannu tare da kama Jalal ya miƙar dashi tsaye, idanunsa a rufe ya nufi hanyar ficewa daga room ɗin yana gaf da ficewa ya yanke jiki ya faɗi a wajan babu numfashi,da sauri Imran ya ƙarasu wajan Mameey kuma tayi waje da gudu tana ƙwalawa Dr kira,wasu likitoci ne wajan guda 4 suka fito lokaci guda kana sukai ɗakin da gudu ganin Jalal yashe a ƙasa yasa suka ƙamashi tare da ɗura sa a kan wani gadon daban, Abbou wani farin abu yasa ya rufe Mummy dashi bayan ya rufe mata idanunta,kallon Dr yay yace "kun gama komai zamu kaita gida ai mata suttura" Dr ya kalli Abbou cike da tausayi yace "eh zaku iya tafiya da ita,amma yallaɓai sai zuwa gobe" jinjina kai Abbou yay kana ya kalli yaran nasa a hankali kuma aka tura gawar Mummy zuwa waje har cikin ambulance aka sanya gawar kana Abbou ya shiga motarsa Imran ya zauna driver Aryan shima motarsa ya shiga ya ɗauki Mameey da Nihila suka marawa motar ambulance ɗin baya, Irfan kuma ya koma wajan Jalal.

_How to subscribe you can 300 naira only 600 for vip, send the money to my account 0116886423 sulaiman Naima s union bank evidence of payment 08419237616🌚🌚Habibaties Uncle ne na kuɗi ne dan Allah ki biyi before you read my book ok dear tnx for the love and care_
Chapter 53 · 0% Book details