Sashe 8
Tsuron Tsirin Tsandauri Part 1 Complete Hausa Novel · about 2 min read
na fita dan zuchiya sai take cemun in shaƙeshi ya mutu duk mu rasa amman dake ni na mallaki zuchiyata ba ita ta mallakeni ba saina fita, da'ace zuchiyata ke da ni da tuni na ƙarashe mijinyawa. Azgar zamu wuce gida sai gobe, ga abincinan ya isheku, ku kuma ku kwashe kayannan muje." Mijinyawane yace. "To Inna duk ku ɗunguma muje in kaiku wasu su shiga motar Hindu maza in sauke ku in dawo. Haka ko akayi Inna Duduwa da Inna Dubu suka shiga motata muka dawo iyakarsu dani a tsakar gida dama a ɓarayin Uwatale suka saba sauka. Ina shiga cikin falona na mayar da sakata. Kuje ku kwanta, in kuma zaku ci abincine ku girka kuci" "Ammi kefa kinci abincinne" Murmushi nayi ganin yadda Asama'u ta damu. Akwai kayan shayi a ɗakina zansha in kwanta kar ku damu" Ina shiga ɗaki nanma na saka sakata. Wanka nayo na zura rigar baccina doguwa, na ɗan dafa shayi a butar zamani mai aiki da wutar lantarki, na sha zallan shayin na kwanta nayi lamo a gado, inata tubkewa da warwarar yadda zan ɓulloma wannan babban Al'amarin daya tunkaroni, da wasa bazan taɓa iya tunkarar wani ko wata da wannan maganar ba, dole in ci in cinye tare da ɗaukar matakin daya dace ni kaɗai dama ni ba mai faɗar sirri ko matsalar gidana bace, ni da kaina nake yanke hukunci da kaina bana buƙatar shawarar kowa. Sai kawai na tsinci kaina da son yin bidiyo mai ɗauke da sassanyar magana ga matan da suka tsinci kawukansu a irin halin da nake ciki. Nayi bidiyo mai zafi da tasiri dake ina cikin zafin abun, na fesar da maganganu cikin ilimi sosai. Editin ɗinshi nayi da kyau na ɗaurashi a youtube chanal ɗina da shafina na Facebook. Ajjiyar zuchiya na sauke na kwanta. Na dai fi awa guda ina juyi daga baya bacci ya ɗaukeni. Washegari takwas a asibiti tayi mun ni kaɗai na tawo na dai shiga ɓarayin uwatale a gurguje na gaishe da su Inna Duduwa na fito na wuce asibiti. Sabira ta wuce makaranta, Asama'u kuma sai tara take da lakca. Ina isa Asibiti na tadda mijinyawa ya farka shayi ma Azgar yake bashi a hankali. Hmmm mutumin naku fa ya farka bai mutu ba. Mrs Bukharihttps://chat.whatsapp.com/JI1IGIBFHYm64hr6IfVfqR