← Book details Tsuron Tsirin Tsandauri Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 77

Sashe 3

Tsuron Tsirin Tsandauri Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ne. To sai nazo dai" Ya datse wayarshi. Cikin ƙasa da minti talatin sai ga Ado ya ƙaraso ƙaninsu Mijinyawane amman ba Nanno bace ta haifeshi ba kishiyarta ce ta haifeshi, gidanmu ɗaya tare da iyalanshi shima. Jigum_jigum dai muka yi daga ni har Ado, can sai ga Mijinyawa Babba da Gambonsu shima tare muke a gida ɗaya da iyalanshi. "Yana ciki har yanzu ba'ai kiranki ba? " Cewar Mijinyawa Babba da duk ya shiga damuwa. Basu kirani ba, nafi awa ɗaya a zaune anan dan Allah ka shiga ka dubo shi" Ai bamma rufe baki ba ya kutsa kanshi cikin ɗakin dan wata iriyar shaƙuwace mai ƙarfi a tsakankaninsu, damma Matarshi nason kassara zumuncin nasu. Bai jima da shiga ba sai gashi sun fito tare da likitan. "Gambo ka shiga ka zauna tare da Mijinyawa Ƙarami, Hinduwa ke kuma muje" Da sauri na miƙe na bisu har ofishin likitan. "To a gaskiya ya samu mummunan haɗari, sai dai da taimakon jama'ar gari da taimakon ƴan sanda an kawoshi akan kari. A binciken da muka yi a kanshi, ya samu raunuka da yawa irinsu kujewa daujewa, sai gilashi daya ratsa tsakiyar cinyarshi ya lume, wannan ne dai sai anyi mishi ƙaramar tiyata kana ya zubar da kusan rabin jinin dake jikinshi, abinda ya zama mai sauƙi babu buguwa a kanshi ko wani rauni mai tsanani da zai zama barazana, sai kunnenshi daya tsaye shima za'a ɗinke mishi in sha Allah. Motar tashi gaskiya tayi kwatsa_kwatsa a yadda su ƴan sandan suka nuna mana a waya sai dai muce ya auna arziki dan bakwa ce mutum mai rai zai iya fitowa a motar ba" Jin irin hali da raunukan da Mijinyawa ya samu ya firgitamun lissafina, sai dai babu hawaye, na rasa kuma kalmar da zance sai Allah kawai nake ambato, lokaci guda idanuna duk suka farfaɗa. "To Dr yaushe za'ayi mishi aikin, sannan a halin yanzu me ake buƙata? " "Aikin sai zuwa gobe za'ayi mishi, babban abinda ake buƙata a halin yanzu bazai wuce jini ba. A yanzu dai yau muna buƙatar kamar leda huɗu da za'a soma saka mishi, sai kuɗin allurannan muna buƙatar a biya, da kuma shi kanshi kuɗin aikin za'a rubuta muku takadda kuje ku biya gobe sai a shiga dashi ɗakin tiyata" Takaddun biyu yasa hannu ya amsa. "To yanzu Dr akwai ƙannena za'a iya ɗaukar jininmu ayi mishi amfani dashi a shirye muke" "To babu damuwa sai kuje lap a auna aga lafiya da dacewar jinin, in yayi falillahi hamdu" Mijinyawa Babba, bani takaddun ni sai inje in biya ku kuje lab ɗin" Shiru yayi, nasan ba lallai bane in yana da kuɗin da zai iya biya ba, rayuwar dai ƙarfin haline zuchiya dai garesu ba dukiya ba. Bashi da tsumi bare dabara dole ya miƙa mun. Da sauri duk naje na biya na dawo na ba Dr. Lokacin dana shigo naga Mijinyawa Babba da ƴan sanda a tsaye suna tattaunawa akan zasu je inda haɗarin ya afku. Dr zan iya shiga in ganshi ko? " "Madam zaki iya in kika daure kika ƙarfafa zuchiyarki dan yana cikin wani hali. Sannan ga wayarshi sai ki riƙe a hannunki, sauran abubuwan da suke motar yana hannun ƴan sanda tukunna." Godiya nayi mishi na fito zuwa ɗakin da mijinyawa yake ciki. Daga nesa na hangoshi a kwance a gado, gefen fuskarshi ya kumbura ta wajen kunnenshi daya yage, ga bandeji a kunnen, cinyarshi ma an rufe da wani farin saƙa, ga ciwuka duk an wanke mishi. Fuskarshi na ƙurama idanu sai lokacin naji naji rauni sosai ya shigeni ganin irin yadda lokaci guda halittar Mijinyawa ta sauya tamkar bashi ba kundukukina na shafa ina nazari da girmama ƙudurar Allah. Na ja doguwar kujera na zauna, babu ko riga fa a jikinshi, wandoma gajerene kawai shi yasa aka katange gadon da labule. Numfashinshi yana hawa da sauka a hankali. Wayata ce ta soma ruri da sauri na ciro Azgar babban yarona ɗan jami'a ke kirana. Azgar ya akayi kana ina?" "Ammi da gaske wai Abbanmu ya samu haɗari kuna asibitin Malam Aminu Kano? " Idanu na lumshe nace. Hakane Azgar sai dai kuyi ta ma Abbanku adda'a. Kazo ka sameni a asibiti, su Asama'u da Sabira su zauna a gida kada suje ko'ina" Sai naji duk Azgar ya kiɗime duk da dai dama ba jarumi bane sam. Sai lokacin na tuno ai ya kamata in faɗa a gidanmu nima. Yaya Saratu babbar yarmu na kira na sanar mata halin da ake ciki. Ki sanar ma su Inna da Baba Soja Yaya Saratu" Itama duk sai hankalinta ya tashi. Ina zaune ga marasa lafiya iri_iri wani inka kalleshi ma wallahi ba zaka sake ba, in kaga halin da mijin wata, uban wasu, ɗan wasu, wan wasu, ƙanin wasu ke ciki, sai kaga majinyacinka shi kamar ma lafiyarshi ƙalau. Tunani na shiga yi zuzzurfa. Azgar ne ya dafa mun kafaɗata sai zuchiyata ta tsinke dana ɗago na kalleshi naga ya toshe baki hawaye na sauka a kundukukinshi. Murmushi nayi. Azgar banda kuka adda'a zaka yi mishi. Allah ga kayanka kai kasan yadda zaka yi dashi, zauna ga kujera kaji ko?" Zama yayi tare da share hawayenshi mukai jigum_jigum har Mijinyawa Babba yazo dashi da Uwatale matarshi da basket na abinci, harda su fulo da tabarma. Suna isowa Yaya Saratu suka iso ita da Akarami shima wanane ɗakinmu ɗaya. "Abinda ya faru kenan? Ɗan adam ba'a bakin komai yake ba" Cewar Yaya Saratu kenan tana jinjina kanta. "Am dan Allah kuje daga waje mutum ɗaya ya zauna dashi ba lokacin ziyara bane yanzu" Faɗin wata ma'ailaciyar jinya. Ajjiye kayayyakin da suka zo dashi Uwatale tayi, Yaya Saratu ma sun tawo da abinci itama ta ajjiye "Ammi kije sai in zauna ni" A_a Azgar kuje kawai kaji? " Akarami ya riƙe hannunshi suka fita dukkansu. Wayar Mijinyawa dake jakata ta shiga ruri, bani da lokacin amsa wayar koma waye zaro wayar da nayi da zummar sakata a shiru ta yadda ko an kira bazai dami mutane ba nayi. Sunan da yake yawo a kan wayar ne yasa na kalla da kyau. Sweet L naga an rubuta harda jan zanen zuchiya a gaban L ɗin. Gabanane naji ya yanke ya faɗi. Sweet L kuma a wayar Mijinyawan? Kai ina idanuna ne suka samu matsala gaskiya, in kuwa hakan na gani to tabbas ƙila lambar Nanno ce, ko lambar mijinyawa Babba. Tuni na saka waya a shiru na mayar jakata naci gaba da kallon hawa da saukan numfashin Mijinyawana. Kamar wasa sunan dana ga ya kira wayar nafa kasa mancewa sai canki cankar wanda ya dace a saka ma sunan nake yi, sai zuchiyata taƙi kwanciya. Ni gashi ba ɗabi'ata bace bin diddigi da son ji ko ganin ƙwaƙwaf ba, sai naji zuchiyata na jana ala dole ya kamata in san waye Sweet L ɗinnan. Tsintar kaina nayi a bisa bin umarnin zuchiyata ta hanyar zaro wayar wanda yayi daidai da shigowar saƙo a manhajar whatApp kuma duka daga wannan Sweet L ne saƙon. Wajen kira na soma shiga ta kirashi sau takwas, kafin ya kirani ƙarfe ɗayan rana. Ya kirata kun kai minti arba'in suna waya. Zuchiyata na rawa ina gangarawa ina duba tarihin waɗanda yake kira da waɗanda suke kiranshi har na tsawon sati guda. A cikin sati gudannan a rana yana kiranta fin sau bakwai, kuma suna daɗewa, jiya ma ƙarfe biyun dare sun kai awa guda suna waya. Sai naji kaina ya ɗaure zuchiyata ta buɗe iska na shigata takota ina wallahi kunji na rantse. Ina daga cikin matan da basu taɓa ɗaukar wayar miji da sunan bincike kamar yadda matan wannan zamanin suke yi ba. Ina ganin wallen masu yi da mamakin abinda ke ɗarsa musu rashin yadda da mazajensu da har suke bincika musu wayarsu. A matsayina ta ma'aikaciyar gidan rediyo wacce ta karanci aikin jarida tabbas nasan wayar mutum sirrinshi ce. Ni da Mijinyawa muna da wani irin yadda da junanmu na ƙin ƙarawa, ƙarewar yadda yasan nawane tarina a asusun bankina, nasan tarinshi a asusun bankinshi, babu bashi a tsakaninmu ko nawane zai iya cira daga asusuna ya kashe ba tare dana tambayeshi me yayi dasu ba haka nima ina iyayin yadda naso da dukiyarshi. Babu shiri na kori shaiɗan ta hanyar cewa A'uzubullahi minal shaiɗanun rajin. Na jefa wayar a ajjihuna tare da kyautata zatona akan lambar. Ina zaune shiru ashe har magriba tayi ni ko ko la'asar banyi ba. Jini wata ma'aikaciyar jinya ta zo ta ɗaura mishi tace dani. "Amman bake zaki zauna dashi ku kwana ba ko? Kinga nan ward ɗin mazane mazane masu jinyarsu" E nasani yaronshi zai zauna dashi" "To ya kamata ki soma shirin tafiya gida magriba harma ta wuce zance tunda an fito daga masallaci." Da sauri na miƙe tare da surar jakata. Na matsa daf kuskar mijinyawa nace. Allah ya baka lafiya Mijinyawana Allah ya tashi kafaɗunka, kayi haƙuri gobe shidan asuba anan zata yi mun" Kamar yana jina haka nake magana. Haka na juya na fita. Su Azgar suna zaune dashi da Mijinyawa Babba, sai Yaya Saratu da Akarami. "Yauwa kin fito ba? Dama yanzu nake so inje in miki magana ya kamata ki koma gida. Ni da Azgar zamu zauna dashi. Ungo nan Atm ɗinshi ne da ƴan sanda suka bani, na'urarshi da sauran tarkacen kayayyakinshi suna gida an kai." Karɓa kawai nayi bance komai ba. Su Akarami sukai musu sallama muka fita. Akarami ne ya ja motata suka mayar dani har gida har ɗaki, Yaya Saratu kuma ita ta jawo motar Akarami tana biye damu a baya har gida. Yaya Saratu ta kaini ɗakina. Bata tafi ba saida nayi wanka na rama sallolina tasa Asama'u ta kawo mun shayi da tuwo ta tusani a gaba saida naci dan dole ba dan daɗi ba." "To zamu tafi Duwaf. Ku kuma Asama'u sai ku dinga leƙo Umman taku, kui tama Abbanku Adda'ar Allah ya tashi kafaɗarshi, Hindu aita adda'a da kai lamura wajen rabbil izzati shine sarki ɗaya da zai share miki hawayenki. A rungumi ƙaddara" Tai ta bani kalma daga ƙarshe sukai mun sallama suka tafi. Yara suka zauna dani har wajen goman dare kafin nace suje su kwanta ƙarfe ɗaya su tashi suyi sallah su roƙama mahaifinsu samun waraka Allah yasa ayi
Chapter 3 · 0% Book details