Sashe 37
Tsuron Tsirin Tsandauri Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read
amman in sun riga sun soma sun yi nisa kaga ba zasu hana ba. Kamar dai yadda akayi dasu Saratu gashi Sunci gaba da karatunsu ga goyo ma abinsu wannan shekarar zasu kammala. Ni kar azo ana rikici dani da surukaine dan wallahi kunji na rantse wallahi sai sun yi karatu kuma sai sun yi aiki. Gara ku sani tun wuri fa" Hannu Baba Nagoɗi ya ɗaga mishi. "A_a kaga waɗannan sunfi su Saratu girma da rawar kai Hinduwace kaɗai bata wannan farfar irin nasu gara a Aurar dasu karatun sayi a ɗakin mijinsu, duk wanda yaƙi amincewa sai ya tafi wani yazo ai sharaɗi za'ayi" "Ai ko ya Aureta daga baya yaƙi karatunta sai dai su rabu bazan zuba idanu a danne musu hakkinsu a dankwafar da rayuwarsu daga ɗaki sai tsakar gida ba. Ina kai ai ya waye sosai yaushe zan ɗauki wannan iskancin ni" Kai kawai su Baba Nagoɗi suke ta girgizawa dan basa tare da irin ra'ayin Baba Sojanmu na tsaurin karatu da kallon wanda baiyi karatu ba a matsayin ba mutum ba. Da sunyi magana yace dan basu san daɗin karatun bane. "Ku tashi kuje an sallameku, ke Hindu banda ke Qazzafi a shirye yake tuni ya gama haɗa kayan akwatinshi ma" Take idanu suka dawo kaina, girar sama da ƙasa na haɗe baka isa gane yanayin da nake ciki ba. Nasan babu wanda zaimun Auren dole Ƴaƴan maƙotama da za'ayi musu Baba Sojanmu yayi uwa yayi makarɓiya yasa a fasa bare kuma ɗiyarshi? Duk bazawara a unguwa da aurenta ya mutu zai ɗauketa ya maidata makaranta yace tayi ilimi tafi ƙarfin wulaƙanci zata fi daraja. Gaskiya yana ƙoƙari ina girmama ƙoƙarinshi sosai. Yaran unguwa da yaga yaro na gararanba sai ya sashi a makaranta yana alfarmomi a wajeje da dama. In saurayine kuwa to soja sai jefa mutum yayi tirenin shikenan. Zaurawa unguwa da sun gama idda zasu zo har gida su sameshi, sai mayar dasu kamaranta, ya nema musu aikin yi. Kuma cikin ikon Allah sai su yi aurensu rayuwa tayi musu kyau. Ya sauya rayuwar al umma da yawa. Madallah da tsayayyen uba. Washegari Gawata na zuwa na sanar dashi saƙon ana nemanshi, zuchiyarshi cike da murna tawa cike da fargaba dan nasan matakin karatunshi shine zai haifar da matsala, ni kuma akan wannan bazan canja ra'ayina ba tunda dai ni zan zauna dashi ba kowa ba, kuma yayi saukar Qur'ani shi ba jahili bane. Ranar da aka yi kiransu wasu sun iso kafin isha wasu kuma sai bayan isha suka ƙaraso. Kusan dukka samarin tara ko wanne ya mallaki abun hawa kasancewar ƴan bokone aiki suke yi Gawata ne kaɗai yazo a Bus. Duk suka hallara a babban falon Baba Nagoɗi, Baba Sojanmu har da littafi da biro sabida yaji daɗin rubuta abinda za'ayi. Tun jiya yake ta rubuta tambayoyin da zai yi musu da sharuɗa. Ni dai ina ɗaki a kwance ina jiran sakamako. Mra BukhariFollow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/F5JwhdwbtCQ6qdo4LA4kyE