Sashe 15
Tsuron Tsirin Tsandauri Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
nake yi mishi baya mun irin wannan son yana dai yin irin nashi, amman nasan shima yana matuƙar sona sosai kuma yana tsaya mun a ko wanne hali. Leƙawar da zan kuma yi naga Mijinyawa baya falon ya shiga ɗaki. Hmm sai ga Asama'u saɗab_saɗab ta fito daga ɗakinsu ta nufi turakar mijinyawa har tana sake waigowa ta tabbatar babu wanda ya ganta. Kaina sai naji yana juya mini ohh dama tana kai mishi ziyarane ɗakinshi ban sani ba, aina zaci a waya kawai suke iya neman junansu, sai kuma inda suka san suna haɗuwa. To amman ni ai ko da yaushe ina ɗakin mijinyawa, sai dai shi nakan farka inga baya kusa dani kuma baya banɗaki, cikin hukuncin Ubangiji ban taɓa fitowa nemanshi ba, kafin ya shigo sabida gajiya ma tuni na koma baccina, kuma bana zargin komai a cikin kaina. Zuchiyata dake dokawa da ƙarfi inaji numfashina yana karkatsewa kamar mai asma. Sai take nabi umarnin zuchiyata na fito nima saɗab _saɗab naje daidai bakin tagar turakar na tsaya. Ba ganinsu nake yi ba jinsu nake yi. Wani irin yanayi Asama'u take ciki sosai duk ta fita hayyacinta, sau biyu a kunnena naji mijinyawa yayi wani numfashi daya saba yi in muna tare cikin aminci da ni'imar dake cikin Aure. "Bani insha ƴan biyuna nafi kewarsu sosai, kinsan na Hindu a zube suke kuma babu tsoka haka irin wannan, ni kuma Allah ya jarabceni da son ƴan biyu" Ya faɗa da wata iriyar murya mai cike da shauƙi. "Wai daka tursasani nazo in ta zo ni ya zaka yi dani Sikari?" "Yanzu zan sallameki inje wajenta kewarki ce ta isheni kema ai naga yadda kika yi kewata." Ina jiyo yanda yake ma jikinta sai sambatu yake yi ita kuma tana wani irin sauti. "Da ace duk mata haka suke kamarki da maza sun more Sweet L komai naki mai kyau da kwalitine, mata sunansu ne kaɗai iri ɗaya." Sai naji shiru suna musayar sumba. Ji nayi sun yi shiru sai wani abu da nake jiyowa. Barin wajen zuwa ɗakina nayi ruf da ciki tare da yin shiru ina sauraren zuchiyata dake dokawa da dukkan rassan jikina dake wani irin ɓari. Yarinyar da Mijinyawa shi ya sai ragon sunanta shi ya raɗa mata suna. Tun tana ƴar shekara biyu take bacci akan faffaɗan ƙirjinshi, tayi kuka ya rarrasheta, wai yau da ita suke wannan abun har yake cewa ta bashi.. ya sha nawa a zube suke. Lallai maza da yawa babu ɗigon kunya da halacci da amana a tattare dasu. Babban abinda yake baƙanta mun raina shine ace wai yarinyar dana riƙeta na raineta tun tana shekara biyu ace itace take aibata halittar jikina. Shi kuma mijinyawa mutumin banza babu kunya babu tsoron Allah tattare dashi subhanallahi. Ina jin tsananin zafin mijinyawa da azabar ƙyamarshi mai cakuɗe da mikin tsanarshi a zuchiyata. Idanuna na ɗaga sama nace. Allah ga kayanka nan kai kasan yadda zaka yi dashi Allah ka ɗauke mun son Mijinyawa cak a rayuwata ya Allah ka kawo mun ɗauki" Turo ƙofa yayi ya shigo da sanda yake dogarowa har zuwa bakin gadona ya zauna har yana wash sabida ciwon dake cinyarshi tafiyarma da ƙyar yake yi fa. Hannunshi ya ɗaura a mazaunaina da suke tafiya da nutsuwarshi amman fa ada kenan, banda yanzu da yake matsa na ɗanyen jini. Hannunshi sai naji kamar garwashin wuta wallahi, ko wata narkakkiyar dalma. "Tutar so ta Mijinyawa baccinki ma kika yi kika barni ni kaɗai inata jiranki?" Idanuna na buɗe tare da juyowa muka fuskanci juna idanuna ina jinsu suna mun mugun yaji babu ko ɗigon ruwa a cikinsu. Kallon mamaki nake yi mishi mai ɗauke da faɗuwarshi ƙasa warwas. Shi kuma kallon yaudara yake yi mun wanda ada yake sawa inji kamar nafi duk matan duniya dace. "Menene ya ɓata miki ranki Yaya jamila da maganganunta ne ni na sani. Kiyi haƙuri tun farko na faɗa musu mota da kuɗinki kika siya yarda ne basu yi ba. Amman zan sake ma Nanno bayani. Naga tunda kika shiga ciki baki fito ba. Hankalina yana kanki amman Yaya Jamila ta hanani tasowa sai hira suke yi mun" Ajjiyar zuchiya na sauke wani ɗaci na tasomun. Babu damuwa yaya jikin naka to?" "Jikin da sauƙi ƙafar dai ko da sandar gaskiya tana mun tsananin ciwo amman Alhamdullahi. Ya semina ta kasance? " Wayancewa nayi da zubo hamma. Bacci nake ji sosai Mijinyawa duk jikina ciwo kawai yake yi mini" "To taso muje ɗakina inji ɗuminki da nake ta kewa anya zan jure jinki a jikina ba tare da munje gona ba kuwa? " Murmushi nayi a zahiri a baɗini kuma nace. Ni da kai zuwa gona har gaba da abada ai ba'a garin gaɓa_gaɓa muke ba. Kai dai ka warke tsab tukunna. Miƙewa nayi tsaye na nufi sib dan ɗakko hijabina, a hankali ya samu ya tashi tsaye muka fito tare. Daga Kitchen Asama'u ta fito. "Ammi sannu da fitowa Abba sannu da jikin" Hmmm kallon Mijinyawa nayi naga wani irin kallon kar ta san kar da sukaima junansu wayyo suna mun kallon biri ina musu kallon ayaba. Yauwa Asama'u me kike yi da har yanzu baki yi bacci ba? " "Farkawa nayi inajin ƙishi shine na fito nasha ruwa" Kai kawai na gyaɗa mata muka wuce muka barta makirar yarinyarnan tana tsaye bata wuce ba. Nina soma shigewata ciki dan in bashi dama ya kalleta ta sanyaya mishi ruhinshi. Ilai kuwa ina shigewa na juyo shi kuma ya juya harda ɗaga mata hannu. Juyawa nayi na haye gadon ina jin zafi da ƙyamar ɗakin ma baki ɗaya. Harna kwanta sai naji ƙamshi turarenta da halamun yadda ya tumurmusheta da gudu na duro ina ambaton Allah tare da runtse idandunana. Riƙeni yayi da kyau. "Lafiya menene a gadon Tutar so? " Da ƙyar nunfashina ya dawo daidai saida na saisaita kaina. Ɗakina zan koma mijinyawa in zaka biyo ni muje, in ba zaka biyoni ba ni kam saida safe" Ina gama faɗin haka na fito sai naga kamar gilmawar mutum da sauri bazai wuce Asama'u ba. Bata da laifi ga gona_gonan mai laifi mijinyawa yaci amanar yarinya yaci amanar abokantaka yau da Abdulƙadiri mahaifin Asama'u da ranshi yaya zaiji ace Mijinyawa da kanshi ya lalata mishi ɗiya wanda ya dace ace sai inda ƙarfinshi ya ƙare akan ganin tarbiyyar yarannan ta ginu. Ina shiga ɗaki ya biyoni yana ta tambayata a mugun tsarge yake hakan yasa na aro nitsuwa na yafa. A kusa dani yazo ya kwanta da dabara muna fuskantar juna. "Nace wani abunne a kan gadon Tutar so ko mutanen naki ne suka dawo miki ne? Kinsan makarai ba'a alƙawari dasu" To babu mamaki su ɗinne dan ji nayi kamar na hau ƙaya" Da haka na manna mishi hauka shine harda kunna karatun Qur'ani a ɗakin, ya dinga mun tofe_tofe daga ƙarshe ma idanduna na rufe da nake jinsu tsabaragen bushewa kamar zasu tsattsage wallahi. Ya jima yana mun tofi kafin daga bisani ya kwanta. Sai can da dare ya shura na buɗe idandunana na sauke su akan murɗaɗɗen faffaɗan ƙirjinshi wanda yana daga cikin abinda ke fusgata a jikinshi. Kafin muyi Aure ƙirjin nashi bai kai haka buɗewa ba sanin inasone yasa ya dage ya ƙaramun faɗinshi, ko kallo muke yi na irin fina_ finan amurka haka nafi son ganin jarumin shirin murɗaɗɗe mai kama da namijin gaske, bana son ganin namiji babu faɗin ƙirji ko da ba'a murɗe yake ba. Wannan ra'ayinane tun ina budurwa dana mallaki hankalin kaina nake sha'awar maza masu ƙatti_ƙattin ƙirji. Hasaso Asama'u nake yi a lulluɓe a wannan faffaɗan ƙirjin da ya ke a matsayin duniyata. Yanzu shikenan kimata ta zube a idanun Asama'u kallona kawai take yi tasan babban sirrina shikenan. Bakinshi na kalla ina hasaso jikinta da yace zaisha a bakin nashi. Tunowa nayi da mai ɗungurungun ɗin kuma Idanuna na runtse jijiyoyin kaina suka amsa. Ina mamakin yadda akayi har aka soma wannan alaƙar tasu, waye ya soma neman wani a tsakaninsu? Sakewar da Asama'u tayi da Mijinyawa abun yayi yawa na kuma yi mamaki. Yarinyar dana ci alwashin haɗata Aure da azgar gashi Mijinyawa ya lalatata ya buɗe mata idanu. Tunda na kulle idanuna na kasa buɗesu adda'a kawai nake yi ƙirjina na curewa tamkar dutse. Sai wajajen asuba na iya bacci. Da asuba naji Mijinyawa na shafani babu shiri na zabura na miƙe zaune, ji nayi kamar gaushi ya watso mun. "Tashin hankali makarannan su da suka yi alƙawarin sun rabu dake Tutar so dawowa naga suke shirin yi fa" Miƙewa nayi ba tare dana ce uffan ba na shige banɗaki idanuna kamar zasu zazzage sabida bacci da tarin damuwowi. Wanka na soma na fito nayi sallah. Ina zaune akan sallaya Asama'u da Sabira suka shigo sai kallon gadona Asama'u take yi, ƙuri nayi ina kallonta. "Ammi ina kwana ya gajiyar hanya? " Lafiya lau Sabira ya karatun? " Asama'u tace. "Amminmu ina kwana ya gajiyar hanya?" Gajiya tabi lafiya, kuna da lekca ne yau?" "Eh muna dashi amman sai yamma zan shiga ni, Azgar dai yana da lakca da safennan. To yayi kuje ku nemi abinda zaku ci, kuyi da Abbanku ni zan shirya in fita aiki" Miƙewa nayi na isa bakin madubi su kuma suka fita a gaggauce na shirya na fito kamar babu damuwa tattare dani. Ina fitowa falo Mijinyawa na shigowa. "Me zan gani aiki zaki je yauma ashe, aina ɗauka zaki huta na kwana ɗaya kafin ki koma aiki" Murmushi nayi nace. A.a zanje ni na shirya zan wuce saina dawo. Ke kuma Asama'u kafin ki tafi makaranta kiyi girkin dare shinkafa da miya" Sai cewa tayi. "Ammi babu nama kifinma ya ƙare" Ban gane ba, wani abun akayi da namanne nasan dai na bar kifi da nama ai? " Sabira tace. "Inna Jamila ne suka yi girki jiya a Kitchen ɗin muma sanda muka shiga muka ga kwanuka duk anci abinci to inaga su sukayi amfani da naman" Shiru nayi ina girmama girman muguntar Yaya Jamila. Bananan shine zasu shigarmun Kitchen suyi mun girki harma su ɓarnatar mun da nama? To kiyi miyar a haka Asama'u. Wucewata nayi na barsu a gida ko Sabira ban jiraba. Kallon ɓarayin Uwatale banyi ba ina jiyo hayaniyarsu Yaya Jamila. A gaban motata naga Azgar