Sashe 76
Tsuron Tsirin Tsandauri Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
kuka yake yi kamar me. Hawaye kawai ke fita a idanunshi idanunshi jawur. "Abba... " "Shisshshsh.... " Ya ɗaura yatsanshi a laɓɓanshi halamun tayi shiru. Babu shiri ta haɗiye kalamanta. "Azgar, Sabira" Ya kira sunansu murya na rawa. "Na'am Abba" Suka amsa a tare. Azgar jikinshi sai rawa yake yi. Numfashi mijinyawa ya ja tare da lumshe idanunshi. Ya kallesu da kyau. Ya jima yana ƙare musu kallo kana yace. "Kuyi haƙuri ku yafe mun da zafi da baƙin cikin dana yi muku silarshi, da kuma zumuncin dana rushe muku da ƴar uwarku da kuka taso a gaban Amminku tare. Dan Allah ku yafe mini kuma kada ku riƙeni. Banyi dan cin zarafinku, ko dan ɓata muku zuchiyarku ba. Nanno ce ta tursasamun akan in aureta, biyayya nayi mata. Amminku tayi fishi mai girma dani. Tsawon shekara ɗaya cur banji ko da muryarta bane, ta toshe duk ƙofar da zan iya jin muryarta. Amman da dabara ku taya ni bikonta. Da ace ina da damar iya kallon Hindu da tuni Hindu ta ganni a landan to bani ƙarfin guiwa ne. Kuyi haƙuri kunji? " Kayukansu du su biyun suna ƙasa Azgar ne ya ɗaga ya dubi uban nasu, bayan ya share hawayenshi yace. "Babu komai Abba. Ciwo kam munji shi marar misalin misaltuwa. Amman tunda kace zaka kawo ƙarshen abun ai shikenan Abba mun yafe matsawar zaka kawo ƙarshen komai, ka dawo mana da farin cikinmu, mu zama kamar yadda muke da" Sabira tace. "Hakane Abba mun yafe in dai komai zai dawo kamar da. Duk da abinda ya faru ba abu bane wanda za'ace ya shuɗe a tarihin rayuwarmu ba. Abba hatta maƙota abun yayi musu zafi, su Innah uwatale ne kaɗai suke murna da Goggo Jamila. Suma dan basa son ganin farin ciki da walwalar Amminmu ne. Kayi haƙuri faɗan da nayi da'ita bazan sake ba, amman dan Allah ka saketa mu kam shine kaɗai kwanciyar hankalinmu, kuma shine zai kawo ƙarshen komai" Murmushi yayi guraben idanunshi fal ƙwallar baƙin cikin abubuwan daya damalmala, da ace yayi tsinkaye tare da duba da idanun basira gami da hange irinna girma kan abinda zai haifar, da tun farkon_farko da Asama'u ta soma mishi ƙananun iskanci, da ya maidata hannun uwarta. Wanda sai yanzu yake ganin sanya hannayenta dumu_ dumu akan abinda ya faru. Shi yasa manzon Allah Arrasul S A W yace ka zaɓa ma ƴaƴanka uwa ta gari, bayan jero nasaba, kyawu ya haska cewar mai addini tafi alkhairi. Ina addini tattare da Halima in banda bankaura, dama dai can tubabbiyace ta bariki bata isilama ba. Yana daɗa ganin wautarshi tare da jin haushin kanshi ainun. Abu guda ke ɗan sanya shi jin daɗi tare da saka tsammani akan Hindu. Rashin kwanciyar aure a tsakaninshi da Asama'u. Amman abu mafi girma da ɗaukakar kashe rassan jikinshi, bai shige aibata maman dake ƙirjin Hindu ba da yayi. Duniyar tashi, wajen dabdalar jin daɗinshi, da nutsuwar nashi. Itama kuma abun ya doketa tunda har ta aiko mishi saƙon tuna mishi da kalmar. Idanu ya lumshe. "Ku yi hakuri komai yazo ƙarshe zan gyara ko da bai kai irin na da ba, balle ina fatan yafi na da sosai. Kuyi ƙoƙarin shawo mun kan Hindu in tace hukuncin rabuwane a tsakaninmu, zaku iya rasani a gidan duniyar ma baki ɗayanta." Da sauri yaran suka ɗago suka zuba mishi idanu shi kuma ya gyaɗa musu kai halamun tabbaci. "Ba zata rabu dakai ba Abba. In sha Allah zamu yi ƙoƙarin ganin hakan duk da Ammi an ji mata rauni, irin raunin da baya warkewa, ko ni bana jin zan iya warkewa Abba. Amman dai bama fushi da ƙudurar Ubangiji. Tunda ba haramun bane, babu dai daɗine shi yasa" Cewar Sabira, Azgar kam bazai iya cewa komai akan wannan maganar ba. Mijinyawa ya jima yana rarrashinsu har suka sake dashi amman fa ta ciki na ciki musamman a cikin Azgar, ita Sabira kasantuwarta mace yasa dukan bai mata rauni ba, sabida mata rauni ne linkib a tattare dasu, kuma ita kamar tafi son ubanta, shi Azgar na Ammi ne. Sai yamma lis suka fito ya mayar dasu hatta Sallah a ɗakin hotel ɗin suka yi, suka ci abinci tare. Ya tarar da Baba sojanmu ya dawo gidanma, shine yake faɗa mishi ai ya koma zai ɗakkosu, ake cewa basanan. Ita Kuma Asama'u an kaita Asibiti harma an bata gado wai Sabira ce ta doketa. "Nayi mamaki gaya. Taya Sabira zata iya ma Asama'u dukan da zai kaita gadon Asibiti, kana mai ya haɗasu ma, kai kana ina Azgar?" Faɗin Baba Sojanmu dake zaune yana cin tuwo da miyar margi sifeshal ta matan Kanuri. " Saɓanine ya haɗasu har ta kai su ga dambe. Amman nayi ma tubkar hanci. Bamu da masaniyar ma tana asibiti a kwance ni babu wanda ya faɗa mun, kuma gaskiya ni banga abinda ya faru harna kwanciya a asibiti ba" Innarmu tace. "Hmmm Allah ya kyauta. In banda sha'anin yara ina Sabira ina faɗa da matar Babanta? In Hindu taji abinda kika yi zaki sani kuwa" "Ayi haƙuri innarmu kada ta sani, ita Asama'un ce ta soma takalar Sabiran, dama suna yi lokaci zuwa lokaci. Ayi dai haƙuri ni zan wuce" Nan yai musu sallama ya kama hanya yana faman mamakin abinda ya kai Asama'u harda kwanciya a asibiti. Yana daf da gida wayar mijinyawa tai ta shigowa ya ko ƙi ɗagawa sabida haushin matarshi Uwatale na neman ya shafeshi ainun. Yana shiga gidan ya tadda motar Mijinyawa a fake. A ƙofar ɗakinshi suka haɗu. "Ina ka shiga ne Mijinyawa inata kiranka baka ɗaga mun waya ince dai lafiya ka fita da yara tun rana? " "Umm lafiya wani abunne ya faru, ya aikin da gani a gajiye ka dawo? " Ɗan tsaki yayi ya ce. "Shigo daga ciki mu tattauna" Bai jira amsarshi ba ya ja hannunshi suka shiga falon Uwatale. "Uwatale bata nanne?" "Tana can ɗakin matar Gambo haihuwa zata yi" Sai su ka yi shiru na ɗan lokaci, can mijinyawa Babba yace dashi. "Mijinyawa menene dalilinka na auren Asama'u tun farkon fari ne, ince kai kaje ma da Nanno batun aurenta, ba wani bane ya tursasaka ba, naga kai ka nuna kana mutuwar sonta harma Nanno ta amince maka. Shin ko dan Hindu ta tafi ta barka ne shi yasa ka kasa sukunin da zaka kula da ƴar mutane, kullum ranka a ɓace kabi ka sauya sai rama kake yi. Menene matsalar ne, ba ji kayi kana sonta bane shi yasa kukai Aure ba? Uwatale tace dani a gabanka Sabira ta kayar da'ita tai ta jibgarta. Kuma bacin an gama hakan kayi ficewarka da yaranka, ita kuma Uwatale ta runtuma da'ita Asibiti. Sunce sun kira wayarka yafi sau a ƙirga baka ɗauka. Nima na kiraka kaƙi ɗauka har Halima na ikrarin zata zo gobe ta tafi da ɗiyarta ita ta gaji, tunda kana gani ɗiyarka zata kashe mata ɗiya. Ni dai na shiga na kashe zancan. A nanne ma nake ji wai baka taɓa kwanciya da ita Asama'un ba ma. Halima ce fa babu kunya take faɗamun maganarnan. Yanzu ya dace ace ni ta faɗamun haka? Shiru mijinyawa kawai yayi ya rasa abinda zaice. Sai can yace. "Babu damuwa mijinyawa Babba zan yima tubkar hanci in sha Allah komai yazo ƙarshe. Sannan ka dena biye kunji_kunjin mata, Hindu fa aiki ta samu na kwantiragi da Bbc Hausa tana landan kamar yadda nayi maka bayani a baya, da zaran ta kammala zata dawo ɗakinta. Su uwatale ke cancana zancan". "Na fahimci uwatale ke ririta wannan lamarin ita kanta zan maganinta gudun kar ta aikata abinda zai tarwatsa ahalinnan. Kaje ciki Asama'un tana ciki an sallamota mun dawo da'ita gida" Godiya yayi mishi ya fita izuwa ɓarayin Asama'u. A ciki ya tadda Uwatale tana mata wasu huɗubobi marasa kyau akan su Azgar. Girgiza kai yayi kawai tare da yin sallama. Da sauri Uwatale ta fito tana dariyar munafurci ta fita. Shiru yayi yabi bayanta da idanu. Ya jima a wajen har sai da Asama'u ta leƙo taga yana wajen kana ya tattaka ya sameta a bakin gado tana wash_wash ɗinta. Yayi mamakin huɗubobin Uwatale da irin maganganun bakinta akan Hindu. Duk Asama'u ta yaɗa shi ita ba'a kwanta da'ita ba, Allah mai iko. Ajjiyar zuchiya ya sauke kawai. "Damben da kuka yi kenan har ya kai a baki gado a asibiti Asama'u? Allah ya kyauta ki shirya suturunki kaf ɗinsu kar ki bar ko silifas akwai inda zamu je gobe" Daga haka bai ce komai ba. Asama'u tai ta haɗa kaya wasu a akwati, wasu a buhu, wasu a jakunkuna saida ta kammala fitar da komai. A daren ya dinga loda kayan cikin mota ba tare da kowa ya ganshi ba saida ya saka komai a motar, ya dawo yayi wanka ya sha ruwan bunu ya kwanta. A daren Qasimu ya iso daga Jama'are yana kwance a ɗakin Azgar, an buɗe mishi. Washegari da wurwuri yasa ta shirya tsab shima ya shirya suka fito harda Qasimu. Sai da ta shiga ɗakin uwatale suka jima kafin ta fito. Shi kuma suna tsaye da mijinyawa babba da Gambo, da Qasimu a wajen mota suna gaisawa tare da shaida musu zasu yi tafiya. Ta iso wajen ta gaishesu ya buɗe mata mota ta shiga. Sun ɗan jima suna tattaunawa al'amuran yau da kullum kafin su ka shiga motar yaja suka fice a gidan. Ta fahimci kamar garin mahaifiyarta zasu je da taga hanyar da aka miƙa. Sai jikinta ya sake sanyi gashi ya zame mata dodo tsoronshi take ji sosai. Tana son tambayarshi me yasa zasu je babu fuska, ya ɗaureta tamau. A tunaninta tunda har ya iya wasa da sassan jikinta bazai iya mata irin abubuwan da yake yi mata a yanzu ba. Aure shekara guda amman ta kaɗa ta raya wata mu'amala ma ta haɗasu. An yi tafiya mai nisa kawai ya tsayar da motar a gaban gidan mai. "Qasimu ka tuƙamu mu ƙarasa juwa nake ji" Canjen waje suka yi, Qasimu ya ja suka wuce. A haka dai suka isa ilai garin mahaifiyarta suka je. "Kinsan gidan da take Aure Halima ko?" "Eh na sani, amman... " Hannu ya ɗaga mata dole tayi shiru. "Ki dinga nuna mun hanyar ance sun sake sabon gida, cewar Qasimu" Turyan_turyan ta dinga