Sashe 65
Tsuron Tsirin Tsandauri Part 1 Complete Hausa Novel · about 2 min read
da kayan miya, sabulun wanka sabulun wanki, harda omo nayi wanka da tafiya tayi tafiya. Bikin luba ma naso zuwa Allah baiyi ba babu kuɗi a lokacin dole na haƙura. Bani na sake zuwa gida ba saida na kuma shekara guda kafin na sake komawa ganin gida. A lokacin naje na tarar da su Yaya Saratu duk ƴan gidanmu babu wanda bai haihu ba harda matan su Qazzafi. Can gida jama'are ma dukkan facalolina sun haihu har Uwatale ma ta sake haihuwar ɗiyarta mace. A zuwana gida na biyu hatta su Innah mairamu saida suka yar mun da magana, kuma akan matsalarnan har asibitin cikin Bauchi saida mijinyawa ya ɗaukeni ya kaini. Amman babu ta inda aka ga wata matsala a jikina ko jikinshi sai dai likita ya ɗauramu akan magani da zasu taimaka harna Hausa dana matsa mijinyawa ya barni ni da Baraka muka je muka karɓo na dinga sha amman shiru kake ji. Baba sojanmu ma saida ya tambayi Innarmu akan ko naje asibiti akan matsalar haihuwan kuwa? Lokacin kwanana biyu da zuwa gida. Naje asibitin Bauchi Baba Sojanmu" "Kuma to me suka ce ciwon me yake damunki akace, ko daga shine matsalar? " A'a dukanmu lafiya akace har magunguna aka ɗauramu akai amman babu canji nasha na hausa ma dukka dai shiru" Na ƙarashe maganar ina haɗiyar zuchiya damma ni ba mai saurin kuka bace a duk wannan son haihuwar da gorance gorancen da akeyi mun a gaban idona da bayan idona ma bai taɓa sani kuka ba sai dai ya sakani a damuwa kawai shima da mijinyawa ya rarrasheni shikenan zan mance da komai." Harna gama ganin gida zuchiyata sam babu daɗi. Haka na dawo jama'are abubuwa suka sake ɗaure mana sosai.