Sashe 2
Tsuron Tsirin Tsandauri Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ranar litinin wanda yayi dai_dai da ɗaya ga watan ɗaya a lissafin nasara. Masu iya magana sukan kira ranar litinin da tushen aiki wanda ko bature ke tsoronta. Ni macece mai ra'ayi sosai Zan iya cewa tsattsauran ra'ayi to, amman ina da sauƙin sha'ani gaya. Sannan duk inda na shiga burina in dishashen taurarin kowa ya zama nawane yake da ƙarfin haske sama dana kowa. Ni macece Ƴar gyaye da ƙwalisa tamkar Maigogul ne ya haifeni wajen bama ado da kwalliya muhimmancinsa, duk abinda zan saka a jikina nafi son ya kasance mai tsada wato daraja. Dan ko ankone aka fitar babbar atampar nake zuwa in nemo, ko in tura samfurin har garin Lagos sai an nemo mun. Kuma tun ina budurwa haka nake, saina kasance ta daban cikin ƙawaye, ta daban kuma a cikin dangina, harma da dangin mijina. Na kasance mace mai guruka masu yawan gaske, gani da naci da ƙwallafa abu a raina, inna kafe ina da taurin kai musamman akan hanyar cimma gurina. Bana damuwa da wahala, ko barazana wajen cimma guri hakan yasa na kasance mace jajirtacciya, jaruma, mai kama da mikiya wajen fita ta nemo da kanta. Ita mikiya fita take yi ta farauto naman ƴan uwanta tsintsaye dashi take kalaci, bata da tsoro sam, kuma tafi son tayi da kanta ba dai ta ƙarashe aikin wani ba. Ba ungulu mai jiran a mutu ta zo ta cacciki naman mutum ba. marar tsoro kuma kona misƙala zarratin. Ni ɗinnan ina alfahari da kaina gaya. Ina da kama mutuncin kaina da kiyaye abinda zai zubar mun da kimata, hakan yasa ko magana zan furta sai nayi jim tare da nazari kafin in furta. Domin a furuci ake gane nauyin ƙwaƙwalwar mutum, da harshe mutum ka iya samun daraja, da harshe mutum ka iya furta abinda zai zubar mishi da kima abadan. Amman ƴan gidanmu dama gama garin jama'a suna mun kallon mai shegen girman kan tsiya, dangin miji, da maƙotana duk haka suke mun kallo, sai dai duk wannan baya damuna, nasan mutum ba'a taɓa iya mishi, a yayin da ka burge mutum ɗari, haƙiƙa sai mutum ɗari biyu da hamsin sun sokeka. Na kasance baƙace ni ba fara ba dan ko a sahun wankan tarwaɗa bazan fito ba, ni ɓakace mai lallausan fata. Ina da hancina daidai gwargwado amman bashi da tsayi kamar biro. Abu mafi kyayu a fuskata shine idanuna da siraran shiryayyun haƙorana masu ɗauke da tsagun wushirya sama da ƙasa. A ɗakinmu nafi kowa gashi sabida irin nacina da kuma ɗaukar gashi da mahimmanci da nayi, duk wani mai na gashi duk tsadarshi saina tara kuɗina na siya, yadda nake mutunta gashina ko fatata bana gatantata haka sabida Innarmu takance damu shi gashi rabin kyan mace ne, sai na ɗauki wannan kalmar na azata bisa kaina. Har bafulatana mai nono a bakin layinmu ta shaidani dan duk satin duniya saina sai manshanu ɗanye na mulke gashina dashi tsabar inason gashi, Alhamdullahi gashin ya samu, ko ina nake a cikin taron mata zan iya buɗe kaina in yi shafar kai hankali kwance. Sannan in kitso zanyi bana manyan kitso ƙananu nake yi sosai wanda a ƙalla zasu kai guda ɗari da hamsin zuwa ɗari biyu, kuma kullum da lalle a tafukan hannayena da tafukan ƙafafuna. Bani da tsayi can ɗinnan gaskiya ni gajerace ƴar dandaɓasa mai faɗin ƙugu da mazaunai masha Allah. Kun gane Fati Baffa ƴar wasan hausa tsohuwar jarumar da suka yi zamani dasu Abida Muhammad? To tsayinmu zai yi ɗaya kunga ai kuwa gajera ce ni ko? Sai dai kash bani da girman nono, ƴan mamunana basu shige na bera ba, su dai banyi gigin cewa zan ƙarasu ba naji ina da ra'ayin barinsu a hakan. Ina da tumbi cikina ba'a shafe yake ba ko ba gaskiya ba dan tumbina yana iya fitowa ta cikin riga ana hangowa, yatsun hannuna dana ƙafafuna gajerune kamar yadda nake gajera Hindu duwaf ƙawayena ma da muka taso tare suke kirana har ƴan gidanmu suma suka kama anfi cewa duwaf ɗin ma, kuma ina amsawa domin ban ɗauki hakan a matsayin rauni ba sam. Sai dai mu gajeru Allah yana yi mana baiwa ta diri fiye da dogayen mata. Ku lura da kyau da wuya kuga gajerar mace wacce bata da diri, shi yasa ko gajerun mutane waɗanda ake kiransu da wada Allah yayi musu diri da mazaunai. Amman dogayen mata kafin kiga mai diri goma kinga hamsin babu cinya babu sharaɓa ko ba gaskiya bane?" ( bafa ni nace ba Hindu duwaf ce take magana) Ina ɗaya daga cikin ma'aikatan gidan rediyon Kano ni edita ce, wani sa'in ina yin labarai musamman na yamma. Amman a aikin gidan Rediyo nafi sha'awar aikin fita ba na zama a ofis ba, sai dai ita rayuwa ba duk abinda kake so kake iya samu ba. Yauma ni na karanto labaran yamma fitowata daga cikin ɗakin watsa labarai kenan sai naga wayata nata rauji. Da sauri na duba wayar kafin in ɗauko ta tsinke. Mijinyawa ke kirana kuma ya kirani fin sau goma. Take naji gabana ya faɗi dan tabbas ba lafiya ba. Mijinyawa baya kiran waya sau uku ma, biyu kawai yake yi ya haƙura sabida yasan yanayin aikina ba ko da yaushe yake bani damar amsa waya ba, wani sa'inma kasheta baki ɗaya nake yi. Kafin in gama tunanin da nake yi wayarshi ta sake shigowa a karo na goma sha ɗaya. A sanyaye na ɗauka tare da sallama da sassauƙar murya. Ilai kuwa sai naji muryar wani daban ba mijinyawa ba. "Assalamu Alaikum madam sunana Aminu Jibrilu in babu damuwa muna buƙatar ganinki a asibitin malam Aminu Kano" Take naji hantar cikina tana kaɗawa tare da duk tsokokin jikina. Lafiya meya samu me wayar dan Allah? " "Ki kwantar da hankalinki ɗan abinda ya sameshi ba mai yawa bane. Kuma a wajen kiran wayarshi munga har dake kuka yi waya dashi da misalin ƙarfe ɗaya, kuma da halama ke iyalinshice shi yasa muka kiraki. In kin shigo ki tambaya ward ɗin maza manya ɓangaren ƴan haɗari na taimakon gaggawa. Amman ki kwantar da hankalinki baima wani ji rauni sosai ba." Da sauri na zame wayar a kunnena na suri jakata dake ajjiye akan teburin aikina. Luba zanje Asibiti Mijinyawa ya samu haɗari kya sanar ma oga" A guje na fita zuwa harabar gidan rediyon. Motata na hau illahirin jikina babu inda baya kakkarwa, bama a cikin hayyacina nake tuƙin ba, daga gidan Rediyon Kano zuwa malam Aminu Kano sai naga yayi mun wani irin nisa gaban mamaki. A guje motata ta shiga cikin asibitin, in tsaya in pakata da kyau wallahi na kasa. Da sauri_sauri gudu_gudu naita kutsa kaina ina tafe dake nasan ward ɗin mazan nan da nan na ƙarasa. Mutane sai darewa suke yi suna bani hanya duk wanda yaga saurin da nake yi yasan bana lafiya bane sam. Wasu ma har dakatawa suke suna kallona. Dana isa cikin babban falon ward ɗin maza saina rasa inda zan nufa ga dai marasa lafiya da yawa a kwance a ɗakin ɓangaren ƴan hatsarine subhanallahi Ubangiji Allah yai mana rowar ciwo. Wayata na ciro da sauri na kira lambar mijinyawa, sai na jiyo raujinta daga can ƙarshen ɗakin a wajen wani gado da aka rufe da labule halamun ana dubashi kenan. Saina ga likitan ya fito. A guje naje gabanshi. Nice wacce muke waya dakai ɗazu. Dr dan Allah wanne hali Mijinyawa yake ciki kace ciwon nashi babu yawa ko?" Ajjiyar zuchiya ya sauke yace. "Kiyi haƙuri yanzu muna kan aikinmu ne, ɗaki ma za'a sake mishi tukunna. Zaki iya jiranmu a waje, ƴan sandan da suka kawo mana shi sunje zasu dawo yanzu. Yana dai fil ko kati tare damu ne? " Kai kawai na girgiza Halamun A_a. "To ga Sista ki bita duk abinda ya dace ayi" Wata ma'aikaciyar jinya nabi har zuwa bakin wani taga anan na cike komai jikina da hannuna sai kakkarwa suke yi duk da jarumtata. Ina zaune shiru a kan dogon bencin dake kallon ward ɗin, nan aka zo aka wuce da wani magidanci ya ƙone har kanshi, sai wani irin ƙara yake yi. Ai take zuchiyata ta kuma tsinkewa, to ko shi mijinyawa a cikin wanne hali yake oho, ya Allah ga bawanka kai kasan yadda zaka yi dashi. Wayata na zaro na daddanna sunan wan Mijinyawa Hassan ɗinshi kenan mai suna Nawata, shi kuma Mijinyawa ana kiranshi Gawata. Sunayene na ƴan biyu wanda a ƙasar hausa a da ake sanyama tagwaye. Anyi tagwaye sakaruna a shekarun baya a Kano ta dabo NAWATA DA GAWATA. Nawata da Gawata sune sarakunan kano daga alif dubu ɗaya da ɗari ɗaya da talatin da huɗu zuwa alif dubu ɗaya da ɗari ɗaya da talatin da shida. Sarakunan tagwayen sunyi Sarautar Kano a tare har sai da ɗaya daga cikinsu wanda littafin tarihin Kano bai ambaci wanene daga cikinsu ya rasu ba. Ya rasu watanni bakwai bayan hawansu kan karagar sarautar. Ɗayan tagwayen ya rasu a shekara ta alif dubu ɗaya da ɗari ɗaya da talatin da shida bayan yayi mulki shi kaɗai na watanni goma sha bakwai. Tagwayen Ƴaƴan Gijimasu da Munsada ne. A yanzu sunan ya ɓata gaskiya, ba kasafai ake samun tagwaye masu irin sunan ba, inma an samu zaku ga yawanci dattijaine. Shi kuma mijinyawa da ake cewa dasu, Nawata shine Mijinyawa Babba, Gawata mijina kenan shi kuma mijinyawa ƙarami ake kiransu harma sunayensu ya ɓace ɓat. Asalin waɗanda ake kira da mijinyawa yaron da aka haifa kakanninshi dukka suna raye na wajen uwa da uba musamman ma matan, to waɗannan yara su ake kira da Mijinyawa. Bansan ya ɗauki wayar ba sai jin sallamarshi nayi a kunnena. A sanyaye na amsa. Dama Mijinyawane ya samu hatsari yanzu haka ma ina asibitin malam Aminu Kano, ko ganinshi ba'a bari nayi ba." Duk wannan abunfa babu ɗigon hawaye a idanuna sabida gaskiya ni macece mai dakiya sosai ba komai ke sani kuka ba, kuma duk ƙwaƙwarka baka iya gane logona. "Subhanallahi ganinan zuwa yanzu. Kafin in ƙaraso Ado zai zo tunda ya fini kusa, kin sanarma su Nanno? " A_a ban faɗama kowa ba. Naga ba jin daɗin jikinta take yi ba, ba a faɗa mata ba " Sai yayi jim kafin can kuma yace. "Gaskiya