Sashe 50
Tsuron Tsirin Tsandauri Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
basaso Gawata ko kuma daga yau ka zama mijinyawa kamar yadda naji ana faɗa maka" Murmushi yayi mun yace dani. "Nima iyayena ba so suke yi ba ansha dambarwa Tutar so mai yawa. Zamane bamu samu yi ba bare in labarta miki halin dana shiga nima" Nan ya labartamun duk abinda ya faru bai rufe mun komai ba ya ɗaura da cewa. "Amman yanzu komai ya wuce mun samu nasarar kasancewa da juna. Yanzu dai ki tashi muje muyi alwala mu gabatar da nafila sai mu dawo ko?" Kunyace naji ta kamani sosai miƙewa yayi ya riƙe hannayena na miƙe tsaye nima a tare muka ɗaura alwala muka fito shi ya ja mana sallar mukai raka'a biyu yai mun ƴan tambayoyi game da addinina na bashi amsar ko wanne, abinda ya ƙara faranta mishi ranshi kenan. "To muje muci nama wallahi tsire muka samu kazar taƙi samuwa fur kuɗaɗenmu duk sun ƙare akan biyan masu mota kiyi haƙuri a bini bashin wannan kazar dole zaki ci." Ai da kayi mun magana akwai kuɗi a hannuna sai in baka ka siyo bana son abinda zai ɓata mana tarihin wannan daren mai tarihi daren da shi zai mai damu mu cure mu zama ɗaya" Dariya yayi mun. "To shikenan ki aramun dubu biyu inje in siyo zan dawo miki dashi da zaran na samu" Kunji fa a daren farko Dubu biyar na miƙa mishi nace. Ragowar ka barsu a ajjihunka" Nan da nan ya fita, kafin ya dawo na sanya doguwar rigar bacci marar nauyi na zauna a bakin gado ina murmusawa tare da ƙarema ɗakin kallo. Haka ya dawo ya taddani muka baje muka ci kazarmu muka haɗe da tsiren muka cinye tas muka sha mirinda. Bayan mun wanke bakunanmu lamura dadaɗa masu tsaiwa a rai suka shiga wakana. A iyakar karance karancen littattafaina anan na gano gwarzantakar Gawata da irin yadda ya bini a hankali har komai ya wakana cikin aminci. Sai dai mamakina ɗaya duka duka da komai minti talatin akayi ruwan aka ɗauke saɓanin yadda marubuta suke zuzuta lamarin wannan daren ta hanyar nuna mana an kwana ana abu guda, an suma, an cika gida da kiran umma da Abba. An kasa tashi da sauran surutai masu tarin yawa da tsaiwa a zukatan ƴan mata sababbin yankan rage. (Marubuta saifa mun gyara wallahi. Ko ƙirƙirarren labarine a ƙirƙireshi daidai da mizanin da hankali zai ɗauka. Allah ya bamu ikon gyarawa) Sai gashi da mamaki da asuba ni da kaina na dafa mana ruwan wanka nakai banɗaki na sirka mana Gawata yayi nashi wankan ya fita masallaci ya dai tambayeni zan iya sabida inna haɗe ƙafafuna ina jin zafi tafiyata ta ɗan taɓu ba sosai ba fa ehe. Nace dashi zan iya sai yai mun sallama ya tafi masallaci. Ina gargasa jikina na dawo garau sai ɗan zafi da kumburi wanda bai wuce misali ba. Kwalliya nayi na saka doguwar rigar lesiri mai ruwan hoda sabone fil na bi jikina da humrori. Tsakar gidan na fita na ɗakko gawayi na saka a shiro ya ruru na bangama gidana turare na sake gyara komai. Wanke wanke na fita tsakar gida nayi, na share gidan na wanke shi tas na fito da naman kannan na shanya a katanga. Yau Gawata zai shigo bashi ya shigo ba sai takwas da rabi. Tare da wata yarinya suka shigo tana riƙe da kwano shi kuma riƙe da kofi. "Masha Allah a gaskiya kinyi kyau sosai Tutar so. Kuluwa ajjiye kwanon maza kije ko? " Ajjiye kwanon yarinyar daya kira kuluwa tayi ta gaisheni ta fita abinta. Miƙewa nayi naje na dakko mana kofuna da filet na zuba mana kokko na juye ɗumamen a filet tuwon masara miyar kuɓewa bushasshiya sai warin kalwa koriya fatau babu mai babu halamun kayan miya shine abun karin Amarya. "Kiyi haƙuri nayi yinƙurin siyo mana kayan shayi Nanno taƙi jiya ma wai kinyi girki an miki gargaɗi akan kada ki kuma Tutar so kiyi haƙuri zama da iyaye sai haƙuri." Wani ƙwallone yaje maƙoshina ya tokareni amman sai nayi murmushi nace dashi. Babu komai muci yinwa nake ji" Muna ci muna ɗan taɓa hira jifa jifa ni dai turawa kawai nake yi, wani irin ƙaurin kalwa miyar take yi kawai. Tunowa nayi da su Yaya Saratu har farfesu innarmu ta dafa aka aika musu har kwana uku ana kai musu. Da kalaman soyayya da ƙauna da labaran kasancewar darenmu na jiya Gawata ya ja hankalina har muka cinye tuwonnan bamu sani ba wallahi. Shi ya wanke kwanukan yace in saka mayafi muje mu gaishe da Nanno da Mijinyawa Babba. Tare muka fito matan gidan surukan gidan kenan duk suna tsakar gida anata aikace_aikacen yau da kullum Masu wanki nayi, masu wanke wanke nayi, masu shara nayi, masu kitso nayi, masu karyawa nayi, gidan dai cike da mata da yara. Suna hangomu aka soma tsogumi Yaya Shafa ce tace. "Kaga ango kasha ƙamshi Amarya sai yanzu aka fito kenan? " Ina kwananku an tashi lafiya? " Na faɗa ina murmushi, ashe su a ƙa'ida saina rufe fuskata na nuna jin kunyata sabida miji ya kwana a ɗakina kwanan farko. Sai suka ga saɓanin haka kunji wannan? Gawata na cikin gaggaisawa da surukan gidan su Mijinyawa Babba suka ƙaraso sai yau Allah yasa muka haɗu kamarsu harta ɓaci bambamcinsu ɗayane Mijinyawa yafi Babban faɗin ƙirji da murɗewar jiki sai haske kaɗan daya ɗarashi. Uwatale tana rufe ruf a mayafi ba'a ko ganin fuskarta. Gaishe da mijinyawa Babba nayi ya amsamun da fara'a cike da kulawa. "Kaga amare masu kunya ba irin matar mijinyawa ƙarami ba ƴan binni" Kallon Yaya Shafa nayi kawai Mijinyawa nawa ya dubeni baiji daɗi ba. Rankayawa muka yi zuwa ɓarayin su Nanno inata mamaki Sai da muka gaishe da kishiyoyinta da suke tasu hada hadar a tsakar gidansu, idanuna a buɗe ina kallon kowa Uwatale kuwa kirif da'ita. Ɗakin Nanno muka shiga da sallama a ƙasa na zaune gefen gadonta duk suma sauran suka zube a ƙasa. "Sai yanzu kusan goma saura ne zaku zo gaisuwa ku da yanzu ya kamata ace bakwa gidanma sun fita sabida mata nan da anjima zasu shiga sunturin zuwa ganin Amare" "Zamu fita yanzu Nanno ina kwana? " Mijinyawa ya katse mata maganar tata da fara'a ta amsa mijinyawa Babba da uwatale suka gaisheta ta sake faɗaɗa murmushinta. Ina kwana Nanno an tashi lafiya? " "Lafiya" Iyakar abinda tace kenan shima a gimtse ni ko ko a kwalar rigata nasan babu yadda dai suka iya dani aurene dai an riga an ɗaura Ina zaune suna ta hirarsu ni dai dake nice bare ina saurarene kawai. "To ina ganin ku ku koma ɓarayinku ko, ku kuma ku zauna zamu tattauna" Ni nama riga Uwatale yima Nanno sallama na fita abuna. Ina shiga ɓarayina na sauke ajjiyar zuchiya kawai. Kitchen na shiga na duba sai naga wannan nama dana tafasa ya so yayi tsami ɗaurawa nayi a wuta na ɗumama kawai saina tsiyayi mai na hau suya. Wallahi ko kaskon farko ban sauke ba Nanno da kanta ta shigo sai ganinta nayi a ƙofar Kitchen tace. "Ke wai wanne irin taurin kai da rashin kunyane dake jiya Ladi bata faɗa miki cewar mu anan sai an kwana bakwai ake girki bane? " Kiyi haƙuri Nanno namanne zai lalace in ban soya ba, kuma naga da kuɗi aka siya" "Nama waya siyo miki wannan naman mai mugun yawa ba dai Gawata ba dai ko? " Da sauri nace. "Dangin Innatane suka siya mun to tun jiya na tafasa harma ya soma lalacewa" Gawata ne ya shigo da sallamarshi. "Yauwa gara da Allah yasa ka shigo kuma a gabanka za'ayi. Yarinyarnan daga namanannan kada ta kuskura ta sake ko da dafa ruwan shayi ne in ba haka ba zan saɓa maka, zan muku babu daɗi" "Kiyi haƙuri Nanno ba zata sake ba" Ta saka kai ta fita, ya kalleni nima na dubeshi muka sakarma juna murmushi. "Ina muka samu nama haka cikin babbar tukunya haka? " Wallahi Innah Yahanasu ce ta siyo mun ga kan rago can ma shima zan soya sai in barshi ya bushe." "To ni kam zan fita sai da daddare zan dawo akwai abinda kike buƙatane zamu shiga Bauchi ni da Qasimu da Abdulƙadiri? " Ɗan shagwaɓewa nayi nace. Kuma sai yaushe kenan zaka dawo? " Ba shiri ya jawoni na fito a Kitchen ɗin ya kama ƙuguna dukka biyun yace. "Ba daɗewa zanyi ba kafin la'asarma mun dawo in sha Allahu. Ki kula mun da kanki sosai in kin gama ki kwanta ki huta bai kamata kina aikinnan ba dan Allah kinji? " Kai kawai na ɗaga mishi nayi mishi adda'a na rakashi har bakin ƙofar fita kana na dawo naci gaba da suyana har kan ragon saida na soya na mayar faranti na baza shi. Leda na samu na ɗebama Nanno cikin leda ƙarama na zuba ma uwatale nata. Yarane da suka shigo na basu suka kakkai na sake ƙullawa a leda nace a kaima Yaya Shafa ta raba musu, suma yaran na daddanƙa musu a hannu. Maƙota mata da yara sukaita shigowa bani na samu kaina ba sai Magrib cincin naita loda musu. Na gyara gidana fes na kunna turaren wuta wani mix ne na gabgab da sandal lamba wan da farce dolar da kajiji wannan in kika haɗesu kika ƙona akwai wasu surruka masu yawa tattare dasu Akwai mix ɗin a wajen mrs Bukhari 15k kacal zaki samu mix ɗin dukka itatuwan turarennan hajiyata. Saida na fito wanka na yi sallah na zauna na tsantsara kwalliya na saka doguwar rigar materiyal mai laushi ina fesa turare naji yo sallama ƙofar falona ina leƙowa naga uwatale ce a tsaye tun kayan dake jikinta da safe suɗinne a jikinta. "Dama nazo ne in faɗa miki Nanno tace zamu dinga cin abinci tare to an kawo abincin wajena in mijinyawa yadawo sai ki shigo muci" To shikenan sai mun shigo" Na faɗa ina murmushi a baɗini naji zafi sosai kuma naji damuwa sai dai dake mai shanye ɓacin raice saina nuna babu damuwa. Ko da bayan isha Mijinyawa yazo bayan mun gaisa na yanka mana kankanar daya shigo mana dashi nake ce mai. Muje ɓarayin mijinyawa Babba acan zamu ci abinci yau. Muje ko? " Haɗe rai yayi na fahimci