← Book details Tsuron Tsirin Tsandauri Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 77

Sashe 31

Tsuron Tsirin Tsandauri Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

TSURON TSIRIN...
TSANDAURI...
LITTAFIN BADIAT IBRAHIM MRS BUKHARI GIDAN ƘAMSHI

LAMBA TA TARA

*Bojuwa herbs*
*By*
*Surayya Dee.*
*08032773332.*

*Sanyi flusher!*
*Yana wanko dukkan sanyin mara, mahaifa Har ma da jijiya.*
*Tasirin da karfin maganin sanyinmu ya wuce misali don kuwa duk wacce ta siya sai ta dawo ko ta turo wasu*.
*Alhamdulillahi Allah ne ya yi mana.*

*Tightening set na hade mace ta dawo zamzam tamkar yar budurwa, kuma babu na insert a cikin park din*.

*Tasirin magani idan andafa tamkar yankan wuka ne shiyasa kazar sababi da ciccibin garari na Surayya halin yau suke da kyau da tasirin gaske a jikin mace.*

*Muna da gimbiyar zabuwa da tattabarun alheri.*
*Akwia packages na mussaman ga amare, uwargida, zawarawa da masu jego.*
*Tuntubeta a wannan lambar*
*08032773332*
*Don samun ingantattun kayan gyara da babu algush.*
*Nation wide delivery*.

"Qasimu bazan iya zaman Aure da Asama'u ba. Kasan Allah in shiga inda take ma bazan iyaba, na kuma kasa. Kaga kayana nan nazo nake nufin tarewa, to amman nasan dole akwai buƙatar in koma gida komai daren daɗewa. Jiya kaɗai da ban shiga ɗakin yarinyarnan ba saida ta kira Nanno ta faɗa mata, Mijinyawa Babba ma yasan halin da ake ciki bare matarshi. Qasimu wai yaya zanyi ne dan Allah kaimun mafita. Sannan ya zanyi da Hindu? Ni dai bazan iya zama da Asama'u ya ƙare tsakaninmu. Ni tsoro ma yarinyar take bani wallahi. Kuma kasan uwarta ke zigata, ina da tabbacin ita ta rusa duk ginin tarbiyyar da Hindu tayi mata. Ta koma maras kunya, maras mutumci, yarinya yadda kasan zatai mun fyaɗe fa"
"Zauna Gawata muyi magana ta fahimta dan Allah, zauna kaji"
Zama yayi suka fuskanci juna.
"Ita Asama'un ka dena sonta ne ko ko dama can sha'awarta kake ji ne? "
"Bazan iya tantancewa ba. Daga lokacin da Hindu ta turo mun waɗannan saƙwannin daga lokacin naji bana son Asama'u kuma ko kusa bazan iya haɗa jikina da nata ba"
"Inna fahimceka da kana sonta kenan ko sha'awarta kake ji? "
"Wallahi Allah Qasimu bazan iya cewa ga haƙiƙanin abinda ke zuchiyata dangane da yarinyar ba, sai dai daga lokacin da muka soma haɗa jiki na dena iya mallakar kaina muddin muka keɓe."
"To Hindu ka samu damar magana da'ita ne, ko dai ta dawo ne? "
Nan ya kwashe labarin tafiyarta landan ya labarta mishi da komawar yara gidansu.
" Tabb Landan fa?
Gawata bazan rufeka ba ka kwabsa ba ɗan kaɗan ba. Hindu tayi halacci nine shaidar hakan. Ka duba irin rayuwar da kuka gudanar a jama'are bafa rayuwa bace mai daɗi duka tako ta ina Hindu ta karɓeshi a wajen danginka, amman a haka ta jure ta kawar da kanta ta shanye harya wuce.
Ka duba ragamar ɗawainiyar gida da ɗawainiyarka data yara da Hindu bata jin ƙyuya sam. Gawata Hindu tayi maka rana a lokacin da kake biɗar inuwa, ta soka a lokacin da matan Jama'are suke ganin ba zasu iya baka ɗiya ka Aura ba, bazan mance sanda Nanno taje ta tambayo maka Auren Uwatale ba. Amman aka ƙi fur duk da dangantakarku, kuma yadda zaka gane farin jinine baka dashi ana cewa a ba Nawata a guje aka bashi, yau ga Uwatale nan ta haɗa garken yara. A haka Hindu ita kuma ta soka, ta ɗaga darajarka. Hindu bawai matar Aurenka bace kaɗai ba. Itace koman ka"
Hindu ta riƙe Asama'u tamfar ita ta haifeta. A lokacin da mahaifin Asama'u Amininmu kenan ya rasu matarshi ta shiga wani hali, nina soma tunanin ɗaukar Asama'u in kaima mai ɗakina Baraka dan a lokacin ita shayarwa take yi Hindu kuma ta riga ta Yaye Azgar tuni. Mai ɗakina kwana muka yi muna rikici akan ita tunda mahaifiyar Asama'u na da ranta ba zata shayar da'ita ba.
(Ina fatan karatun nazari kuke yi ba karatun jin daÉ—in rai ba? Wannan littafin ban yishi dan nufin daÉ—i ba, ku nutsu ku saurara har na kai ga manufar domin anan ribar take)
Haka na haƙura washegari nazo Asibiti kake labartamun ka amshi Asama'u ni dakai muka kaima Hindu Asama' u a farin tsumma bazan manta ba. Hindu ta saka hannu ta amsheta ta rungumeta tsam a ƙirjinta.
Ba tare da ka nemi shawararta ba, ta riƙeta da zuchiya ɗaya ta sota sosai, gashi ta jima bata samu cikin Sabira ba Asama'u ta jima a saman cinya da kafaɗun Hindu. Babu irin siratsin rayuwar da baku tsallake kai da Hindu ba, Gawata babu shi.
Amman kash bayan shafe duk wannan tarihin ace da Asama'u za'aima Hindu kishiya. Ba kishiyar tafi ɗaga mun hankali ba halin da aka tsinci kai kafin Auren. Gawata tunda ka bani labarinnan ranar ɗaurin Aure nake tubkewa da warwarewa. Hindu fa ta barka har abada ko ta dawo Landan ba zata taɓa dawowa gidanka ba bare ta sake samun gogewar aiki da buɗewar idanun rayuwa, kuma kaima ka sani Hindu ta fika wayewa nesa ba kusa ba. Soyayyace kawai ta zargeku kaida a ƙauye ka kasa Auruwa Gawata"
"Ya isa Qasimu ya kake neman tayarmun da hawan jinine dan Allah? Ni na kiraka domin kaimun mafita kai kuma kana neman tarwatsamun zuchiyata. Qasimu inaso in sallami Asama'u ta koma gidan mahaifiyarta da zama. Ko zan samu salama. Na aikata babban laifi, naci Amanar Hindu, na zubar da darajata, na saɓama mahaliccina, kana naci amanar Abdulƙadiri. Kaicona Qasimu kaico"
"Gawata ka nutsa da kyau tukunna kada ka daddama lamura da yawa mana, sannan abinda nake faÉ—a ai duk gaskiya ne. Yanzu inka saketa ka kirama kanka ruwa wallahi. Ka daure ko wata biyar tayi saika sallameta. Amman fa ka shirya shiga tashin hankali, sannan saika zama kurma makaho. Amman tabbas sakin Asama'u zai rage kaso ashirin bisa É—ari na fishin da Hindu take yi da kai, sai dai fa ba zata zauna da kai ba.
Amman dai kayi haƙuri a ɗan miƙa tukunna gudun rikici kaga in Sabirace akai Aurenta kwana biyu miji ya sakota ta dawo duk rashin gaskiyarta baza ku taɓa jin daɗi ba. Gani zaku yi kamar an tozartaku ne ma, to sai ka daure Gawata. Jarabawace taku kuma a haka tazo, da tsantsar son zuchiyata, da son kai, da rashin jin tsoron Allah bare abinda kaje kazo.
Kayi haƙuri da kalmomina ni Qasimu nine zan iya tsage maka gaskiyar data dace.
Amman matarka Hindu tana sonka so mai tsamari, ka sani, nima na sani Gawata, in ka waiwaya baya.
Ni damuwata mata zasu É—aukeka su kafa hujja akan wannan kalma da suke jaddadawa ta namiji ba É—an goyo bane.
Kuma sun canfa cewar duk namijin da akaima halacci, sai yayi butulci. Kuma mata ku dena waÉ—annan kalmomin wallahi bamu taru mun lalace duka haka ba. A ko wacce iriyar al'umma akwai nagari akwai na banza.
"Na sani Qasimu wallahi na sani. Haka Hindu take cewa Mijinyawa anya ba asiri kayi mun ba kuwa sonka kullum ninka kanshi yake yi a zuchiyata. Qasimu da Hindu bata sona da ta tona mun asirina a duniya. Amman wallahi ko iyayenta basu san abinda ke faruwa ba a irin yadda suka ƙi jinina da sun sani inaga Baba Soja da kanshi zai koreni inna shiga gidannan, ko yasa a kulleni a firzin na sojoji.
Ni dai Qasimu landan zani in samu Hindu me kake gani?"
"Landan fa? To kana da kuÉ—ine Gawata da zaka bita. Sannan in ka bita me zaka tarar ka sanine?
Kai dai kayi ƙoƙarin sakin Asama'u da zaran tayi wata biyar zuwa shida.
Kuma kayi ta istigifari wala Allah aurenku ya zauna.
Amman binta Landan bazai haifar da É—a mai ido ba.
Irinsu Hindu in sukai fishi abun babu kyau. Gata da makarai in kaje suka tashi wallahi tsab sai su shaƙeka ka mutu a banza. Ka daure ta dawo kawai"
Sun É—auki lokaci mai tsayi suna tattaunawa sai da Qasimu yasan yayi duk yadda zaiyi ya kwantar ma da Mijinyawa Hankali.
Washegari da safe bayan sun karya sun gama shiryawa Mijinyawa ya nufi wajen aiki Qasimu kuma ya nufi Jama'are.
Kwananshi huÉ—u a É—akin hotel kana ranar Juma'a ya koma gida da yamma.
Har zuwa lokacin bai samu damar magana da Hindu ba, ko da yayi mata magana da number shi daya buÉ—e whatApp saita kulleshi kai tsaye. Sai rubuce rubucenta ne suka zame mishi abokan rayuwa, bidiyoyinta suka zama ababen nishaÉ—inshi sai dai wasu abubuwan in yaji ta furta sai yaji duk ya tsargu sosai dan wallahi dashi take yi.
Chapter 31 · 0% Book details