← Book details Tsuron Tsirin Tsandauri Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 77

Sashe 30

Tsuron Tsirin Tsandauri Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

gaban madubinshi Asama'u ta taso tazo bayanshi ta tsaya baiyi Aune ba ta rungumeshi ta baya, yana jiyo ƴan biyu, sai yaji kamar ta ɗana mishi garwashi yayi saurin zabura ya miƙe nanma ta sake rungumeshi tsam harda saka mishi kuka. Shiru yayi yana sauraren kukan, tare da sauraren zuchiyarshi amman tuno abinda suka aikata kafin auren da kuma tuno fuskar Hindu yasa ya ɓanɓareta da sauri ya rirriƙe hannayenta tare da daka mata tsawa dan sai wani dire_diren shagwaɓa take yi mishi mamanta na rawa na iskanci. "Ki nutsu ina magana dake dan abu ta kazan..." Ya daka mata tsawa. Babu shiri ta nutsu dan tunda take bai taɓa mata tsawaba bama ita kaɗai ba kaf yaranshi. Sai taji ta tsorata. Hannayenta ya sake ya wuce wajen durowarshi ya zaro jallabiya ya zura. "Ɗauki hijabinki ki zura maza ki koma ɓarayinki. Kada ki sake biyoni nan wannan sirrinane ni da Hindu Mamanki" Da mamaki ta dubeshi amman taji haushin abinda ya aikata mata saita fice fuu. "Aikin banza ko menene ribar auren wannan mitsitsiyar yarinyar oho ita ba kyau ba ma. Nayi nadama da dana sani, bazan iya haɗa jikina da wannan yarinyar a matsayin matar Aure ba, wallahi bazan iyaba, bazan iyaba Hindu na tuba." Wata zuchiyar tace mishi. "Yarinya bata fa da laifi kaine ubanta ka fita hankali da sanin abinda ya kamata. Ka dai rushe farin cikin gidanka da kanka. Muddin Asama'u zata ci gaba da wanzuwa cikin rayuwarka a matsayin mata, to tabbas kaida Hindu har gaba da abada" Zama yayi a bakin gadonshi da ƙyar ya haɗiyi maganin ciwon kai ya kwanta shiru yana sauraren zuchiyarshi, dake daka. Haka dai gari ya waye dasu asussubar fari Yaya Jamila tazo akan abinda za'a karya dashi. Firjin Hindu ya buɗe ya basu nama da kayan miya yace ko taliyace su dafa, suka wuce masallaci dasu Qasimu. Suna dawowa aka shiga sha'anin wanka da sake kaya, shida da rabi aka kawo musu taliya da lafiyayyen shayi yaji madara suka karya banda Mijinyawa. Bakwai daidai duk suka fito aka shisshiga mota harda dangin Asama'un duk suka watse gida ya rage daga su Uwatale sai Asama'u. Nanno taƙi fur tayi magana da Mijinyawa har suka tafi. Su Uwatale su suka gyara mata ko'ina harda wanke_wanke. "Kin ji labarin kishiyar taki tayi tafiya bata gidan akayi bikin ko? Sai fa kinyi da gaske kishi da Hindu sai mutum ya shirya gata da kafirin girman kai" Cewar Uwatale, Matar Gambo sai cewa tayi. "Naji fa ana cewa yaji tayi ta tattare yaranta ta tafi dasu, bayan mun dawo Mijinyawa ƙarami ya tafi biko a ruwannan ƙin biyoshi dai tayi kun santa da taurin kai" Uwatale tace. "Zaiyi wuya tayi yaji tunda har ta bari aka ɗaura auren batai rigima ba, nifa na ɗauka saita kusan ƙona gidannan amman dake makirace saita nuna da Asama'u da banza duk ɗaya, kema kinsan tasan meta taka. Kiga ko fenti na ɓarayinta yafi tsada, jibi wasu royal kujeru daya saka mata kota ko ina ɗakinta yafi na Asama'u kyau da girma fa hmm" Asama'u take taji wani ƙwollon kishi ya tsaya mata a zuchiyarta tana kuma jin kota halin ƙaƙa saita mayar da Hindu ba komai ba a wajen Mijinyawa. Wuyarta ya ɗanɗana zumarta dan mahaifiyarta ba ƙaramin shiri na magunguna tasa akayi mata ba. Cire kunya tayi ta koya mata yadda ake ƙwace miji kamar yadda gidan data shiga ta tadda mata biyu ta kwace misu miji take juya mijin yadda take so, yake fifitata tako ta ina. Ga kuma kulawa da tattalin miji, da haƙuri data koya a aikace a wajen Hindu. Sai take ganin ƙwace goriba a hannun kuturu abune mai sauƙi sirrin Hindu a tafin hannunta yake, haka duk abinda mijinyawa yake so ta sani sarai. Murmushin mugunta kawai tabi su Uwatale dashi. A ɓarayinta suka wuni cur, uwatale ta dinga kwance ma Hindu zane. "Asama'u ai ya kamata kije ɗakin kishiyarki kima Mijinyawa magana yayo miki cefane ya kamata ki yi girkin tarbarshi ke a daɗinki ma Allah yasa Hindu ta tafi kenan har gaba da abada, dama ni tun farkon da aka haɗamu kafinma a Auromu ikon Allah jinina da nata sam bai haɗu ba. Tana da iyayi da yawa da girman kan tsiya. Wannan da ace ita kaɗai ke da Digiri a surukan haularnan da an boni." Nan sukaita zuga Asama'u ta shiga ta feffesa turare a jikinta ta gyara ɗaurinta ta nufi ɗakin Hindu. A rufe ƙofar take hakan yasa dole ta shiga ƙwanƙwasawa kamar ba za'a buɗe mata ba dai sai kuma aka buɗe mata. Ranshi a ɗaure yace. "Lafiya me ya kawoki kuma? " "Sikari dama cefane nake son ayo mun inaso zan ɗaura girki" "Ina zuwa" Iyakar abinda yace da'ita kenan ya mayar da ƙofa ya kulle bai jima ba ya fito da basket guda na kayan miya da sukai ƙanƙara harda su nama ya miƙa mata ya kuma kulle ɗakin ya shige. Ji yake yi uwa yayi shekara da shekaru bubu Hindu a rayuwarshi gidan jinshi yake yi tamkar wata babbar katanga ta rushe. Ba Hindu ba yara sai Asama'u a matsayin mata ba'a matsayin ɗiya da take a wajenshi da ba. Idanu ya runtse kawai Haka ya wuni cur a ɗaki cike da kaɗaici sai dai ya fita masallaci ya dawo. Da bayan la'asarne ma yayi wanka ya tafi gidan ɗaya daga cikin abokanshi na wajen aiki sai bayan isha'i ya koma gida ziƙau daga shi sai halinshi. Ɗakin Hindu ya kuma buɗewa ya shiga yayi kwanciyarshi a kujera tare da kunna tv ya nemi tasha ya saka, bama kallon yake yi ba kawai dai ya kunnane. Wayar Hindu ya sake kira bata shiga, ya duba whatApp ko zai ganta saiya fahimci kamar fa ta kulle layinshine a whatApp ɗinta. Zabura yayi nan take ya buɗe sabon WhatApp da ɗayar wayar tashi da number daban. Sannan ya ganta, bata kai amman bata fi awa uku da sauka ba, hakanne ya tabbatar mishi da kulleshi dai tayi. Bugun ƙofar falon ne yasa ya miƙe yana tsaki Yana buɗewa yaga Asama'u a tsaye. "Ashe da gasken dai kaine ka dawo, to ya ka dawo nan ka zauna ga abinci yana jiranka kuma yau ai ranace ta musamman a wajen, ka man... " "Ke bana son fitsara da iya shege kinji ko, wai lafiyarki ƙalau kuwa Asama'u? " Shiru tayi tana ƙunƙunni ƙasa_ƙasa. "Kije ki ci abinci ki yi kwanciyarki kinji ko? " Wannan karon da rarrashi yayi mata maganar saita fashe da kuka ta ruga a guje zuwa ɗakinta. "Allah na tuba, Allah ka yafe mini" Ya faɗa a fili ya koma ciki. Ranar ma a ɗakinshi ya kwana sassafe ya shiga shirin tafiya aiki, ya fito tsab cikin shirin aiki yana kiciniyar rufe ƙofa Mijinyawa Babba yace. "Ohh ashe da gaskenne a ɗakin Hindu ka kwanta kabar ƴar mutane sai kuka take runtumawa ta kira Nanno ta faɗa mata wallahi Nanno tace ka kiyayeta duk abinda kake ciki tace ka kwana a ɗakin matarka yau ni dai saƙo ta bani. " Ƙarata takai kenan Mijinyawa Babba? Bana jin daɗine kwata_kwata fa. Kuma kaga yanzu haka ma tafiyace a gabana an turani first bank na garin kaduna akwai wani abu da zamu gudanar ka ganni a ƙagauce na fito" "Kuma na ganka ba jaka amma? Mijinyawa Babba ya tambaya yana kallon ɗan uwan nashi. "Mancewa nayi bari in shiga in ɗakko" "To Allah ya tsare a dawo lafiya in ka nutsu saika kira Nanno dan ranta ya ɓaci" Mijinyawa yana shiga ya tattaro kaya ya danna a akwati ya fito da sauri. Ɗakin Asama'u ya shiga tana Kitchen tana ɓuruntu kiranta yayi daga tsayen da yake. Da murna ta fito tayi tunanin ya dawo ɓarayinta ne. "Ina kwana? " Fuska babu annuri ya amsa mata. "Zanje Kaduna tafiya ta kamani. Zan turo a kawo miki kayan miya, zan tura miki kuɗi a account ɗinki saina dawo" A sanyaye tace. "Me zai hana mu tafi tare dan Allah, tsoro nake ji wallahi" "Bazai yiwu ba. Kima Uwatale magana ta baki Zainab ta dinga tayaki kwana" A wajen ya barta ya ja akwatinshi ya fice ɗan sahu ya tare ya kaishi babban hotel ya kama ɗaki, yana ajjiye akwatin ya wuce wajen aiki zuchiyarshi cike da tunane_tunane masu yawa. Ba kadunan da zashi ya haɗa ɗaki da Asama'une wai bazai iyaba kimunin. A wajen aikin ya kira Nanno yake faɗa mata tafiyar da yayi saida ta gama faɗanta tayi mishi adda'a kana hankalinshi ya kwanta. Qasimu ya kira a waya. "Qasimu dan Allah inason ganinka inda hali amman bana gida inka shigo Kano ka kirani kuma kada ka faɗama kowa zaka shigo kano" Cike da mamaki Qasimu yace "Allah yasa ba wata matsalar bace ba ko? " Kai tsaye yace. "Itace Qasimu kai dai sai ka iso kawai, ƙila ma kafin ka iso na mutu Qasimu" Saida yayi dariyarshi ma'ishi kana yace. "Duk wanda yace zai yi guga danya ɗebi duniya, ƙarshe ko ya janyo bazai janyo komai ba. Gawata tsalle ɗaya akeyi a shiga rijiya, amman wallahi sai ayi dubu ba'a fito ba. Kasan Allah bacci wannan ɓarawone ya kwasheni. Baraka sai tambayata take yi damuwata amman ina na kasa magana, sabida wannan sirrinkane Aminina." "Ka kasheni kawai ka huta zai fi maka" "Ka kashe kanka dai, ni in kasheka ka rataya a wuyana da wannan zunubin daka aikata? Allah ya kiyaye. " Hmmm" Kaɗai yace. Qasimu yace dashi. "To shikenan saina zo, Allah ya kyauta." Da wannan Mijinyawa ya ajjiye wayarshi ya shiga aiki, amman ina aikin yaƙi samuwa, baya ganewa har lokacin tashin shi a aiki yayi dai. kai tsaye ya wuce Hotel ɗin da ya ya da zango. A ciki yayi sallah, ya yo odar abinci aka kawo mishi tuwon sakwara da miyar Egusi. Ya tusa a gaba kenan Qasimu ya ƙaraso dan ya riga yayi mishi kwatance kuma ya bashi lambar ɗakin. Sakawa yayi aka ƙaro tuwon sakwarar suka ci tare kana sukai sallar isha'i kafin tattaunawarsu ta soma gudana" Mrs Bukhari. To sai mun haɗu ranar Monday kumahttps://chat.whatsapp.com/JI1IGIBFHYm64hr6IfVfqR
Chapter 30 · 0% Book details