Sashe 70
Tsuron Tsirin Tsandauri Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
HINDU:
DAWOWA LABARI:.
Murmushi nayi mai ciwon gaske wannan ranar tana daga cikin ranakun da suke da tarihi baƙi wanda bazan iya mancewa ba abadan. Bari in tsayar da labarin a nan, amman zamu ci gaba, an sha gwagwarmaya mai tarin yawa sosai. A iyakar haka kaɗai zaku iya hanke mana hukunci ni da mijnyawa. Ni dai na riga da na rufe shafinshi a rayuwata. Inna juya ma wuri baya wallahi ko sama da ƙasa zata haɗe bana waige.
Miƙewa nayi na faɗa banɗaki na cire kayana na saki ruwan ɗumi a jikina idanuna a lumshe ina sake kallon wannan ranar kamar yau abun ya faru.
Gashi dai daga ƙarshen ƙarshe mai afkuwa ta afku na bar mijinyawa har gaba da abada yaje ya rayu da Asama'u ta taci gaba da haihuwa mishi tunda na samu haihuwar har yara biyun amman ban tsira ba.
A yanzu bana tunanin akwai abinda zai dameni, ko na misƙala zarratin.
Gaga_gaga_gaga_gaga
Haka rayuwa a landan taci gaba da tafiya yadda ya kamata. Gurbin karatun mastas dana samu ya sake sawa zaman ƙasar yayi mun daɗi sosai.
Sosai na mayar da hankalina haiƙan akan ci gaban rayuwata, na rufe komai da komai na ɗauki lokacina na rabashi gida hudu gashi ɗaya na ibadar Allah da rayuwar Ƴaƴana, kashi na biyu naba aiki na da dangina, kashi na uku na ba karatuna da ci gaban rayuwata, burina in shahara in zama mace mai arziki, da yalwar ilimi, kashi na huɗun shine na ba rubuce_ rubucen wayar dakai da nake yi dan a yanzu nafi samun damar rubuce_ rubucen fiye da yin bidiyo lokaci zuwa lokaci ina yin gajerun bidiyoyi in ɗaura a Facebook. Bayan dogon nazari, da yawan bincike yasa na gano, rubutun yafi saurin isar da saƙwannin da akeson isawarwa. Menene daliki? Sabida ƴan uwa mata sunfi gane manhajar WhatsApp da Facebook sosai, kuma suna son karance_karance A halin yanzu ina da tarin mabiya masu son aiyukana dama masu sukan aikin nawa. Ina samun lokaci ishasshe a duk mako in bibiyi sharhi da yawan masu yaba mun abun mamaki maza ne, matan sunfi ƙarfi wajen aibatani da kirana ƴar kwangilar yahudawa da sunaye marasa daɗi makamantan haka dai. Amman maza in aka kasasu kashi ɗari saba'in a cikinsu yabamun suke yi kaso talatin ke sukana saɓanin mata da kaso mafi tsoka shine na albatawan, bayan duk a kansu nake yin komai amman basa tare dani.
Sai dai dake na faɗa muku ba'a samun cikar guri ta sauƙi kana kwance, dole a hanya akwai gargada da ƙalubale masu tarin yawa a yayin tafiyar, kuma ni cece kuce a kaina baya damuna, yana daga cikin dalilin da yasa nake yin Hajiya Laila Ali othman, da Lubna boƙararriya, duk da nasan a wasu lokuta ra'ayinsu na cin karo da addininmu, amman in aka ɗauke wannan ina yinsu.
Kuma sara da sassaƙa baya gashe gamji. Abu mafi daɗi shine dana saki bidiyo ko rubutu kafin kace wayewar gari abun yayi shurar da ni kaina sai abun ya soma bani tsoro. Dake mafi yawancin saƙwannina da daddarene sune na ƙarshe wanda da nayi nake ajjiye wayar sai kuma gobe. Ɗan ragowar Lokacin dashi nake zumunci da dangina da yarana.
Hankalina a kwance yake sosai sau biyu ina turama da Luba kuÉ—i kuma tana yi mun bidiyon yadda sabon gidana yake ciki, da duk abubuwan data siyo ta zuba mun.
Tafe_tafe da wasa_da _wasa har yau gani shekarata guda cur a landan gani cikin hukuncin Ubangiji nasha ruwan landan fatata ta yi kyau ta murje maina na kamfanin Oriplame dai ban sake shi ba sabida mayukane masu tsada da sirrin kyau duk wata babbar mace mai jin itace zaka ganshi a jakarta ko a gaban madubinta hatta turaren fesawa da nasu nake amfani sai na wajen mrs Bukhari da shima na yadda da ingancinshi in ka fesa har ka wanke kaya yana ƙamshi itama nata, tana da manya _manyan kayan ƙamshi wanda ake musu laƙabi da Luzziri😃kun dai gane turancin ko?
Kamar kullum dawowarmu daga aiki kenan na yada zango a saman kujera ina sauke numfashi na gaji sosai gashi gobe asabar muna da lakca akwai buƙatar in yi karatu ga takaddun mata dana tara fin goma suna jiran amsata tare da basu shawara ni da mabiya shafukana.
Wanka nayo na saka sassauƙar doguwar riga.
Na kwanta nayi bacci sosai sai magriba na tashi na gabatar da Sallah. dake bana jin yinwa sai kawai na dafo shayin ganyen shayin Ahmad ti mai ƙamshin gwaiba. Nazo na zauna a saman kujera tare da shigar da ƙafafuna cinyata na ɗaura laptop ɗina a cinyata na kutsa tsafina na Facebook na ɗan yi dube_dube kafin kuma na shiga whatApp ɗina, yauma Qasimu yayi mun sallama hmm baya gajiya wajen taya abokinshi godona. Ganin sunanne ma yasa na tuno da mijinyawa da Asama'u ƙila yanzu sunanan suna renon ƙani ko ƙanwar Sabira hankalin Nanno da su Yaya Jamila ya kwanta.
Nasan ko ta haihu babu mai faɗamun daga su Yaya Jamila har su Azgar. Tunda na tawo babu wanda ya sake yi mun maganar mijinyawa su Azgar dai suna faɗamun sunje sun dubo Baban nasu a bisa umarnin dana gindaya musu basu taɓa tsallakewa ba, basu taɓa bani labarin halin da Babansu da matar Baban nasu ke ciki ba, sabida ba irin tarbiyyar dana ginasu akai kenan ba. Ni kasancewarmu a gidan gandu yasa duk abinda muka gani har rige_ rigen zuwa faɗa muke yi, iyayen namu suma kuma su biye mana, sabida kowa na son ganin gazawar abokin adawarshine.
To in ka taso ka samu iyayenka sun yi kuskure a tarbiyyar da suka baka ka girma ka mallaki hankalin kanka, bai kamata kaima
Ka sake aikata irin kuskuren akan yaranka ba.
Amman mai hankali kaÉ—ai ke gyara abinda iyayenshi suka rusa ko lalata a tashi tarbiyyar.
Yawanci abinda muka taso muka samu iyayenmu da kakanninmu suna yi muma shi zamu yi. Imma, mai kyau, imma mara kyau.
Wannan tunanin shi ya hallaka su Abu jahal da sauransu masu bin addinin iyaye da kakannin.
Mrs Bukhari.TSURON TSIRIN...
TSANDAURI...
LITTAFIN BADIAT IBRAHIM MRS BUKHARI GIDAN ƘAMSHI
LAMBA TA ASHIRIN
_Idan kika sai littafinnan nawa mai suna TSURON TSIRIN TSANDAURI tamkar kinyi sadakane kai tsaye a asusun marayu._
_Littattafaina kuÉ—insu sadaukarwane ga iyayen marayu har zuwa ranar da zan dena rubutu._
_Ko nawa kika cire kika saka marayu zan yima hidima dashi wallahil azeem ko kuÉ—in Data bana cirewa a kuÉ—in littattafaina, marayu kaÉ—ai nake yima hidima._
_Saima ƙarawa da nake yi da kuɗin kasuwancina akan kuɗin da littafi ya samar mun._
_Kuzo ku siya mu samu ladan marayu tare daku, ga lada, ga karatun littafi Hajiya._
_Wannan link ɗin na ƙasa ɗaya ne daga cikin aikin da nake yi da kuɗin wajen hidimtama marayu, shafin gidan Rediyo, da talabijin na ZINARIYA TV jos ne suka ɗaura domin sun kai ziyara a lokacin da aikin tallafin yake gudana._
_Nayi hankane ba dan riya ba sai dan ina cewa marayu nake ma hidima da kuɗin, amman ku baku taɓa gani ba, shi yasa wannan karon na zaɓi ku gani, daga yanzu kuma zaku dinga ganin dukkan aiyukan da nake yi da kuɗaɗen littattafaina, hakan zai ƙara mana ƙarfin guiwa
__Daga É—ari bakwai zuwa sama yadda kike jin zaki iya zubawa baki faÉ—i ba saima romon lada da zamu samu a tare_
_Mu tausayama marayu wallahi marayu suna cikin wani hali na ni ƴasu, har jari ina tallafama da iyayen marayu jarin ƙananun sana'a domin dogaro da kai_
Nagode sosai son so
https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=pfbid0auC21yurVzFgZB5dArWgYZNDLpSLDWWNyMVfhw5pjfoThFSJepavmiD8NMy2sUmgl&id=100084908716368&mibextid=Nif5oz
*Bojuwa herbs*
*By*
*Surayya Dee.*
*08032773332.*
*Sanyi flusher!*
*Yana wanko dukkan sanyin mara, mahaifa Har ma da jijiya.*
*Tasirin da karfin maganin sanyinmu ya wuce misali don kuwa duk wacce ta siya sai ta dawo ko ta turo wasu*.
*Alhamdulillahi Allah ne ya yi mana.*
*Tightening set na hade mace ta dawo zamzam tamkar yar budurwa, kuma babu na insert a cikin park din*.
*Tasirin magani idan andafa tamkar yankan wuka ne shiyasa kazar sababi da ciccibin garari na Surayya halin yau suke da kyau da tasirin gaske a jikin mace.*
*Muna da gimbiyar zabuwa da tattabarun alheri.*
*Akwia packages na mussaman ga amare, uwargida, zawarawa da masu jego.*
*Tuntubeta a wannan lambar*
*08032773332*
*Don samun ingantattun kayan gyara da babu algush.*
*Nation wide delivery*.