← Book details Tsuron Tsirin Tsandauri Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 77

Sashe 24

Tsuron Tsirin Tsandauri Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

dalilin yasa ban sanarma kowa ba face ke, na siyane sabida su Baba sojanmu. Nasan ko mu jima ko mu daɗe akwai ranar da dole sai gidanmu ya tarwatse kowa ya kama gabanshi, sabida gidan na Baba Nagoɗi ne kinga daga ranar da Allah yayi mishi cikawa zaman gidan gandu ya ƙare. Yayuna maza sojojine rayuwarsu da iyalansu a bariki suke yinta albashin nasu sai godiyar Allah. Kinji da tunanin da na sai gidannan domin iyayena su amfana da dukiyata ba iyakar miji da yarana ba. To kema da kin yi wannan tunanin da yanzu kin huta. Amman bata ɓaci ba, ga gidaje ana ginasu madaidaita wanda zaki bada kaso mai tsoka daga farko duk wata zaki dinga biya a hankali har ki gama. Kuma in kika bayar dana farkonnan zaki iya shiga gidanki takaddune ba za'a baki ba har sai kin gama biya. Inmaa na fili kike so duk anayi. Ki tuntuɓi oga Rashid kiji." Luba taji daɗi shawarata kuma ta yaba. Ina hanyar zuwa ɗakko rahoto mijinyawa ya kirani yana shaidamun ƙarfe huɗu za'a kawo kaya zuwa lokacin na dawo. Eh kawai nace mishi na datse wayata. Su Yaya Saratu na faɗama munyi dasu zamu haɗu a gidan. Ƙarfe uku da ashirin na shiga gidan na tadda basu isoba. Ina shiga suna isowa Sai santin fenti suke yi duk da dai jukkunansu a mace yake sosai. "Labarin aure ya baza gida sai gulme_gulme in faɗa miki akeyi daga gidan muke ma yanzu haka anata yagalgala zancan an samu nayi" Zasu yi su gama wuyarta a ɗaura amarya ta tare." Huɗu da kwata motar kaya ta shigo har harabar gidanmu akaita shiga da kaya su Yaya Saratu na jerasu. Dan kyau kaya sun yi kyau amman ni a wajena asarar kuɗine kawai. A tsanake nake ta tarkace suturuna ni da Luba muna kaiwa gidana muna adanawa na riga na tashi ƴan hayan gidan babu kowa. Ana saura sati guda biki sai ga su Yaya Jamila daga jama'are sun kawo kayan faɗar kishiya dama ya sanarmun zasu zo zasu kawo kaya, saina sanarma su Yaya Zakiya suka tawo. Ni sanda suka zo ma ina hanyar dawowa daga ɗakko rahoto a gidan gwamnati. Na shigo na samu an bubbuɗe akwatuna har biyu da jakarshi. Dangin miji sai kallona suke yi, sun yi mamakin ganina gadagau ba rama ba damuwa sai fara'a ma tare da yi musu sannu da zuwa nice harda godiyata" Washegari suka kama hanya suka koma. Nayi ma Mijinyawa godiyar kayan dannar ƙirji sosai. Ya ɗakko dubu ɗari biyu da hamsin ya bani wai kuɗin ɗinki. Ya waro wasu daban wai na cefane in inaso zanyi tarone. Sabuwar kunyata yake ji sosai baya yadda mu haɗa idanu sam. Abokanshi sai zuwa suke suna mun nasiha da godiya ina ta binsu. Ana jibi ɗaurin aurene nake sanar mishi ina da semina da Bbc a Abuja gobe ya kamata in wuce. Kallona yayi yace. "Amman kinsan jibi gidannan a cike yake ko, ya kuma za'azo ke bakya nan Tutar so? Kiyi haƙuri da Semina ɗin dan Allah. Ki daure a samu a tarbi baƙi bana son ƙananun maganganun su Yaya Jamila". Murmushi kawai nayi mishi nayi shigewata ciki. Naci gaba da haɗa kayana a tunaninshi na haƙura ne sabida baiji nayi gaddama ba, saida na haɗa komai na fito na shiga ɗakin Azgar na sameshi nace ya kirawo mun Sabira, yaje ya kirawota suka zo muka zauna ina kallonsu. Gobe zanyi tafiya zuwa Abuja jibi zamu wuce landan na samu kwantiragi da Bbc Landan zanje inyi shekara biyu in dawo, zanyi amfani da damar zanyi mastas ɗina acan in sha Allah. Amman bana so ko da wasa ku faɗama Abbanku har saina tafi. Sannan inaso in sanar muku wacece Abbanku zai Aura Asama'u ce ta gidannan " Da sauri Azgar ya ɗago muka haɗa idanu idanunshi naga sunyi jawur dasu, Sabira kuwa jikina ta faɗo ta sau kuka. Shima Azhar hawaye yake yi ni kuma ina kukan zuchi. Kuyi haƙuri ai ba haramci bane akwai aure a tsakaninsune. Sannan na horeku da kada ko a labari inji kunyi mata rashin kunya ko wani abun. Ranar da aka gama biki ku tarkata ku koma gidanmu har saina dawo. Kuyi haƙuri kamar yadda nayi. Kai gobe zaku wuce Jama'are ko? " Kai ya ɗaga mun kawai, ya kasa magana amman fa naga jikinshi yana wani irin ɓari gaskiya. To shikenan ke Sabira gobe zan kaiki gida shima in sun dawo jibi sai ya tawo ya sameki. Ku mayar da hankalinku akan karatunku, dana isa na samu nutsuwa zan kiraku" Hannuna Azgar ya riƙe yace. "Ammi amman ba shirin barinmu kike yi baki ɗaya ba ko? . Ammi bazan zauna ba ni dai, ba kuma zani bikin ba gaskiya. Asama'u fa ƙanwata, Asama'u fa Yayar Sabira wacce kika raineta, yarinyar da nake kama hannunta muje miki aika itace za'a kawo miki" Ai sai ya fashe da kuka mai gunji tamkar ba namiji ba har yana dafe ƙirjinshi. Wannan maganar tashi ta matuƙar raunata mun zuchiyata ainun sakamakon wani birnannen mikin daya fama kanshi a zuchiyata.
Chapter 24 · 0% Book details