← Book details Tsuron Tsirin Tsandauri Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 77

Sashe 26

Tsuron Tsirin Tsandauri Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

MIJINYAWA. Jama'are cikin unguwar Dako_Dako cikin Gidan Malam Ibrahim Ɗan Safiyo Ranar ɗaurin Aure. Mijinyawa yana kwance a ɓarayinsu dake cikin gidan nasu ga jeren Hindu tunna Aurensu sanda take Amarya. komai yananan fes dake kafin su iso an share komai an goge komai. Wayar Hindu ya sake bugawa a kashe tun jiya yake ƙoƙarin samunta a waya abun ya faskara ya kuma ci tura. Sai yaji duk komai ya fice mishi a kanshi yana jinshi wani iri kamar a ɗaga Auren yake ji. Tun ranar daya sanar ma Hindu batun biki yake jinshi a cikin yanayi na wasi_wasin Auren sosai Abokan wajen aikinsu ke sake ƙarfafa mishi yuiwa, suna karanto mishi falalar dake cikin Auren yarinya mai ɗanye jini. Tsaki yayi ya kalli babbar rigarshi dake kan kujera wacce ta sha aiki, da ita zai yi amfani wajen ɗaurin Auren. Sai yayi shiru yanata aikin nazarin abinda bashi da wani amfani domin kusan lokaci ai ya ƙure. Yana ta jiyo hayaniyar mata da yadda aketa aikin tuwon ɗaurin Aure. Yaya Jamila da su Yaya Tabawa ne suka yo ayari kusan su biyar duk ƴan ɗakinsune cikin Nannonshi. "Mijinyawa ƙarami kana ciki ashe Hamusu yazo akace mishi baka nan, nifa na ɗauka kana wajen abokinka Ƙasimu ashe kana nan? " Cewar Yaya Jamila kenan. "Ina ciki dake jiya ban samu ishasshen bacci ba shine da safe nayi banma jima da tashi ba. Yaya akayi ne Yaya Jamila? " "To menene ma ba'ayi ba Mijinyawa kayayyakin akwatinnan gaskiya sai yanzu dasu Inna Larai suka isone shine ake ganin kamar yayi kaɗan babu manya_manyan atampopi masu yawa a ciki. Takalma da jakunkunan ma basu da tsada can can ɗinnan kuɗi zaka kawo a yi maza aje kasuwa a ƙaro kafin isowar dangin uwa da uban yarinyar. Kaga kai ka riƙeta zasu iya tsammatan abinda yafi haka daga gareta. Tunda a Aurenka na fari da waccan gajeruwar matar taka bajintar da akayi bata wasa bace duk da su kushewa ma sukaita yi. Ko ba haka ba Tabawa? " "Sosai kuwa mayafai ma sunyi ƙaranci a hakanma Inna Zakiya ta kawo biyu an ƙara. Kaga matarka suturu kake siya mata manya sosai gata da sarƙar gwal damfareriya itama tun wuri ai ya kamata ace an sai mata ko ƙaramace gaskiya da bata wuce dubu ɗari shida ba sabida yanzu inta shiga ba lallai bane fa ta samu ba. Dan wallahi yadda idanun Hindu suke a tsaye ya maman maza ba yadda zata yi a siya ba" "To yanzu dai nawa kuke buƙata in sallameku in samu in bar gidannan in kuna ganina ba zaku dena tatsata ba" "Ai gara mu tatseka wa yasan nawa Hindu ta tatseka tunda taƙi nuna Auren na gabanta ma. Milliyan ɗaya zaka bamu har da kuɗin sarƙar gwal ɗin sai mu shiga Bauchi a gurguje a siyo abinda ya dace kafin ɗaurin Auren mun dawo Ajjiyar zuchiya ya sauke ya lura su Yaya Jamila wani hanyar cin kuɗi suka samu tun jiya ake sakashi ture_ turen kuɗi in ya nuna babu a soko maganar Hindun da kafin yayi mata hidima tayi mai sau goma sha biyar. Kafin ya sai mata sutura ta saima kanta sau ashirin koma fi. "To shikenan zan tura ta asusun bankin ki ni zan shiga wanka" Basu bar ɗakin ba saida ya tura musu. Yana cikin banɗaki yana wanka kanshi ya ɗauki ɗumi sai yake ta jin ƙaran wayarshi harya fito wayar na kiɗa Asama'u ke kiranshi. Zama yayi tare da ɗaukar wayar ya kara a kunnenshi. "Ranki shi daɗe yaya akayi ne? " "Lafiya lau Angon Asama'u yau dai alƙawari zai ciki ko? " Murmushi yayi mata kawai baice komai ba. "Dama kuɗin dinki zaka tura mun zamu je mu karɓo kafin ƙofar gidan ya soma cika da dandazon ƴan ɗaurin Aure. Dubu sittinne" "To shikenan zan tura miki yanzu ranki shi daɗe sweet L" Da haka sukai sallama ko daya duba account ɗinshi dubu ɗari bakwai gareshi kacal, banda dai asusun da yake tari a ciki, su kuma waɗannan kuɗaɗe na cizo ne ajiya yake yi. Dubu saba'in ya tura mata ya shafa mai ya kintsa cikin farar shadda ɗinkin malum_malum yana fesa turare abokanshi na wajen aiki suka kirashi gasu sun iso jama'are. Ai babu shiri ya fito dan zuwa ɗakkosu nan filin gidan yawan ya karaɗe da guda tare da faɗin "Ango kasha ƙamshi. Shi dai yana yaƙe ya fita kin motar Mijinyawa Babba na hannunshi kawai sai suka je suka tattago baƙi mota guda shi da Ƙasimu. A gidansu Ƙasimun aka saukesu anata hada_hadar ɗaurin aure Abokanshi na ƙuruciya duk suma sun taru anata hira ana dariya da yawansu ma ba'a jama'aren suke da iyalansu ba nema yasa duk sun warwatse sai dai sukan shigo bikin Aure ko bukukuwan sallah haka. Ƙarfe ɗaya daidai ƙofar gidan malam Ibrahim Ɗan Safiyo cike dam da Al'umma su Baba Soja dasu Akarami sune a gaba_gaba aka ɗaura Auren Gawata da Amaryarshi Asama'u a bisa sadaki nera dubu Ɗari biyu ha da hamsin. Ta faru ta ƙare wai anyi ma mai zane ɗaya sata. Nan mijinyawa ya soma gaishe_gaishe da jama'a anata yi mishi Allah ya sanya alkhairi yana amsawa tare da dariyar jin daɗi. Baba Soja da Akarami daya gani yaji daɗi sosai kuma yasa an karramasu an saka musu abinci a mota dan sunce juyawa zasu yi, ai kuwa Azgar ya sulale yabi su Baba Soja suka juya zasu je su kwana a Bauchi washegari su wuce Kano. Da ango da abokanshi kuma suka ɗunguma zuwa cikin gidansu Ƙasimu dan anan akaba matar Qasimu kwangilar yi musu girkin biki. Yana duba saƙon Asama'u sai yaga saƙwannin Hindu sunata shigowa ai babu shiri ya fita daga son bama Asam'u amsa ya duba yaga Hindu tayi mishi saƙo fin ɗari nawa. Sai yaji jikinshi ya mutu mus jikinshi ya zare ya nufo gida ya kusa kai ya shiga ɓarayinsu ya kulle ƙofa ya zauna a kan kujera. "To me Hindu take cewa har ɗaruruwa haka, ko dai ta zazzagar mun abinda ke ranta ne? To bari dai in cire fargaba in duba. Buɗe saƙon yayi ya soma da taya shi murna da tayi sai yaga saƙwanninshi shi da Asama'une da duk abinda sukaita cewa da duk bidiyo da hotunan tsaraicin juna da sukaita turama juna. Miƙewa yayi tsaye tare da kama haɓarshi yayi shiru yanata nazari mai zurfi da tsayi. Malum_malum ɗin jikinshi da hula da agogon hannunshi ya cire duk yayi fatali dasu a tsakar ɗakin. Hannayenshi ya goya a bayanshi wayar na riƙe a hannunshi. Haƙiƙa yaji kunya, nadama, damuwa irin wanda bai taɓa shiga ba a rayuwarshi ba. Baya ji ko kusa in zai iya haɗa idanu da Hindu. Kuma duk da yasan son da Hindu take yi mishi ba ɗan ƙarami bane amman ya gasgata tabbas macece mai kawaici da danne damuwa da baƙin ciki. Saiya soma tuno wannan zaburar da tayi a ranar daya shigo da Asama'u turakarshi a karon farko ya tumurmusata akan gado. Kenan ta gansune shi yasa daga ranar bata kuma shiga turakarshi ba kana bata sake bari mu'amalar aure ta kuma shiga tsakaninsu ba? Yanzune ya shiga nazari akan sauye_sauye masu nauyi da girma da yake fuskanta daga wajen Hindu. Tana da dukka wannan hotunan da bidiyon baiwar Allah amman take iya bacci taje aiki harma tayi ma Mijinyawa murmushi yayi magana ta bashi amsa? Wayar ya jefar akan gado ya ɗaura hannayenshi a ka yana jin jiri na neman kwashe ƙafafunshi ya nanashi da ƙasa. Yanzu yaya zaiyi ya gyara tunda shine ya ɓata? Yasan Hindu da riƙo da taurin kai, gata da ra'ayin riƙau yanzu ta wacce hanya zai gyara komai ya zaiyi Hindu ta mance da duk abinda taji ko ta gani? Wata zuchiyar tace. "Ai har abada bazata mance ba. Kuma har abada ka rasa yadda da zallan tausayi a wajen Hindu. Kuma har abada mutuncinka bazai dawo ba" Ai sai yaji jiri ya jefashi kan kujera ba tare daya shiryama hakan ba. Shiru yayi a kujerar yana tunanin to tun farko shi kuwa meye abinda ma ya ruɗu dashi a jikin Asama'une tunda yasan babu abinda ta isa ta nuna ma Hindu sai ƙuruciya kaɗai. Mema yasa harya biye mata a matsayinshi na uba suka shiga aikin ashsha, ya Auri ɗiyar da matarshi ta riƙe ta raina taci wahalarta. Shi kuwa ya dace ace ya aureta ko da tafi kowa kyau a duniya? Sai yanzune fa duk yake waɗannan tunanin a lokacin da tunanin bashi da amfani sam, a lokacin da komai ya damalmale ya rugusa farin cikin da suka shekara sama da ashirin suna ginawa. Wannan na daga cikin illolin da muke samu. Yana da kyau kafin kayi komai a rayuwa ka duba abinda zaije ya dawo ba masalahar kanka itace kaɗai abar girmamawa ba, masalahar iyalinka shima abun dubawane. "Yanzu da gaske duk ni na aikata wannan charts ɗin da Ɗiyata wacce bata da bambanci dasu Azgar a wajena, ni nake buɗe tsaraicina nake nuna mata, itama ta buɗe nata ta nuna mun, in kaita hotel in sha komai na jikinta? Ya subhanallahi ya subhanallahi Allah na tuba ka yafe mini Allah ka yafe mini. Aminina ka yafe mini na lalata maka yarinya. Wanda nayi imani in kaine yarana suke hannunka ba zaka aikata wannan aikin ba. Hindu ki yafe mun ki gafarta mun Hindu" Lokaci guda Mijinyawa ya zama majinuni na dole inya tashi saiya zauna. A yaune ya gane irin illata rayuwarshi da yayi da irin abinda yayi ma haularshi. Ba Hindu ba har su Azgar sai yana jin baisan da wanne idanu zai kallesu ba na Auren Asama'u da yayi duk da ba haramci ya aikata ba, amman a babi na mutuntaka da dattijantaka Azgar ya kamata a haɗa Aure da Asama'u ba wai shi ya Aureta ba, bama auren ne babbar damuwar ba irin biye matan da yayi, shaiɗan ya shagaltar dashi ya biyema kaidin mace yaita aikata abinda bai taɓa aikatawa a rayuwar ƙuruciyarshi ba sai yanzu da girmanshi. Damma Allah yasa duk yadda take mishi magiya da yadda take nuna buƙatuwarta gareshi baisa ya taɓa gigin kwanciya da'itaba sai dai yayi mata wasanni harta samu nutsuwa. Dana sanine ya shigeshi na ɗakko riƙon Asama'u ma tun farko Allah ya sani daya san
Chapter 26 · 0% Book details