Sashe 55
Tsuron Tsirin Tsandauri Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
ne. Nayi miki alƙawarin zaman Ƙauyannan lokacine zan mayar dake burni" Nan na sake muka ci gaba da hirarmu tare muka yi shanyar ya taya ni muka gyara gidan kana ya fita ni kuma na shiga hidimar girki. Gaga_gaga haka rayuwata a Jama'are taci gaba da kasancewa littattafai suna tusa a gaba karatuna nake yi haiƙan kuma inajin daɗi sosai da sosai. Nanno bata taɓa gajiya da ƙorafin rashin fitowata ayi hira dani ba. Haka matan gidan da yaransu kallona suke yi a matsayin baƙuwa kullum ni kaina na kasa sake jikina dasu sam amman kullum zamu gaisa in abun jajene ina leƙawa haka inna taya murnane dani shima akeyi. Amman ina fama da hayaniyar yara, gashi su Shafa sai suita shewa a tsakar gida. Gidan fa wani matattarane na matan ƙauyen Baraka take sanar dani a gidan aka ƙyanƙyashi ƙwai tara tsinana na gulma. A gidan komai na cikin ƙauyen yake fitowa Shafa itace wuman lidar magulmatan garin. Ana cikin haka Zakiya ta haihu ranar suna kuwa muka ɗunguma har da Baraka muka je suna. To a lokacin Uwatale na da cikinta harma ya fito nan Yaya Jamila ta dubi tsabaragen idona tace dani. "Hindu ke kuwa shiru ko ɓatan wata baki taɓa yi ba Aure wata shidda ga Uwatale nan da ciki wata biyar ke kuwa sai dai kici kiyi ƙaton kashi. Allah dai yasa ba juya Mijinyawa ya ɗebo mana ba dan mu kaf zuriyarmu suna haihuwa haka surukan gidanmu babu wacce ta taɓa kaiwa wata shida bayan Aure bata yi ciki ba" Ashe haka matan da basu samu ciki da wuri ba suke ji in akai musu gorin haihuwa? Ranar naga tashin hankali ido da ido. Sabida tsabar ɓacin rai kawai sai na dena ganin kowa kaina naji yana motsawa, duk yadda naso in mallaki kaina ina makatan kainane suka tashi suka bigeni a gidan sunannan suka shaƙo wuyan Yaya Jamila da ƙyar aka ƙwaceta akace, a ranar masu makarai a gidan sunannan sun faɗi har da waɗanda ba'a san ma suna dashi ba sai da suka bigesu. Gidan sunannan ya hautsine sosai, makarai suka karɓe sha'anin sunan baki ɗaya ni dai da ƙyar na dawo haiyacina ina gane inda kaina yake na koma gida bakina alaikum ina shiga da Nanno na soma cin karo labarin duk abinda ya faru a gidan suna duk ya dawo musu. A yanayin data ganni ba arziki ta bani hanya na wuce dan idanuna sun yi jawur sosai kuma sun juya kamar irinna masu harari garke. Da ta yi mun magana da saina fyaɗata da ƙasa, ko in haɗa kanta da danga. Ina zuwa daf rijiya na sake zubewa na shiga burgima da tambotsai suna faɗin ba zasu yadda na ɓata mun rai da akayi ba. Ya akayi ya akayi ni dai na ganni a ɗaki Baraka na kusa dani. "Sannu Hindu Allah yasa dai wannan mutanen sun tafi wahalar tayi yawa" Naji ta faɗi gashi duk jikina ciwo yake yi ko zaune na kasa miƙewa sai daga kwancen nace. Meke faruwane Baraka yaushe kika zo? " "Hmmm labarin da tsayi Hindu yanzu dai ki lallaɓa ki tashi ki ɗan watsa ruwa mijinyawa nasan yau duk inda yake yana hanya tun rana aka tura ɗan aike ya sanar dashi halin da kike ciki, sabida an kasa shawo kan matsalar. Babu wanda bai tsorata da irin yanayin da kika tsinci kanki a ciki ba. Nima dake mahaifiyata ciwonta kenan tun tasowarmu shi yasa na iya zama dake dan bana tsoronsu wahala babu irin wanda mahaifiyarmu bata sha ba" Shiru nayi ina ƙoƙarin tuno abinda ya faru take kuwa na tuno ni dai nasan na baro gidan suna na dawo gida na tadda Nanno a tsakar gida iyakar abinda zan iya tunowa kenan. Sallamar mijinyawa yasa Baraka ta miƙe da sauri. "Maraba ka ƙaraso kenan? Hindu Allah ya ƙara sauƙi" "Na iso Baraka dan Allah in babu damuwa ko zaki faɗamun abinda kika sani dangane da abinda ya jefa Hindu a halin da aka bani labari" Kallona Baraka tayi kana ta dubeshi tace. "Abinda zan faɗama shine Hindu bata da lefin komai bata cakali kowa ba taɓata akayi. To kasan mutanannan in suna tare da mutum ba dama ayi ma mutum abun ɓacin rai sai kaga sun kawo ziyara. Allah ya kiyaye gaba" Ta saka kai ta fita. Shi kuma ya zauna a bakin gadon ya riƙe hannayena du biyun ya kuramun idanu ya kasa cewa komai naga firgici sosai a cikin yanayinshi. "Kiyi haƙuri Tutar so babu inda zan sake zuwa in barki zan kafa sana'ata a jama'are abinda muka samu shi zamu tattala. Ni kaina ina azabtuwa sosai da rashinki. Ki faɗamun abinda ya faru kada ki ɓoye mun komai domun insan wanne matakin zan ɗauka akan Yaya Jamila. Zan iyayin komai a kanki. Ka taimaka mun in watsa ruwa in yi sallah tukunna, kaima kana buƙatar hutu ai." Da kanshi yaimun wankan ya gargasa mun jikina sai wash_wash nake yi sabida ciwon jiki. Agogon dana kalla ne ya tabbatarmun da kwana ɗaya nayi da wuni ɗaya bansan inda kaina yake ba. A zaune na soma rama sallolina ina jiyo ɓuruntun mijinyawa a Kitchen daga baya naji fitarshi. Bayan na gama rama sallolina harda magriba da ake yinta yanzu saina koma na kwanta a kan gado maganganun Yaya Jamila na dukan kaina. Nima sai yanzu na tambayi kaina ni har yanzu ban samu ciki ba, to sai yaushe zan samu nima inji ɗumin jinina, to dai juya ce? Yaya Saratu ce ta faɗo mun ita da kunika ma tayi abunta na sake tuno ƴan gidanmu da akai musu aure lokaci ɗaya da su Yaya Saratu babu wacce ta shekara ba da goyonta ba amma ni gani wata shida cur babu ko ɓatan wata gashi har nima na shiga sahun matan da rayuwarsu take yin tsanani sabida rashin samun rabo kenan? " Da sallama mijinyawa ya shigo ɗauke da tire da pilet cike da taliya da ruwan shayi sai maganin ciwon jiki kati ɗaya. A kan gadon ya dure mun a gabana. "Taso kici abinci kisha magani Tutar so sannu kinji" Nanno ce ta leƙo yana rungume dani. Da sauri ya sakeni, nima na sake shi a firgice" Ji nayi tamkar ƙasa ta dare in faɗa dan kunyar a yanayin data same mu. "Ba shakka zinariya ba lafiya ciwonta ya hana kaje ka dubo Yayarka data shaƙe wuyanta har yanzu bai saɓe ba, ya kumbura. Kai da kace mun bari kaje ka ajjiye ledar kayanka ko? Shine ka ɓige da lallaɓata" Miƙewa nayi a hankali dan takaici na nufi hanyar banɗaki. "Kibi a hankali jikinki babu ƙwari Tutar so" "La'ilaha'illallahu Mijinyawa a gabana, sannan ina maka magana hankalinka na kan juyar matarka" Da sauri na juyo muka haɗa baki wajen maimaita kalmar. "Juya?" "Eh juya ko nima shaƙenin zaki yi kamar yadda kikaima yar mijin naki yarinya sai rashin kunya da taurin kan tsiya kin gama shanye mun yaro. An gama asirceshi a turaren wutan da baki da aiki sai bankashi. Kai kuma ka wuce kaje ka duba ƴar uwarka da baka da kamarta ko yau na faɗi na mutu itace makwafina. Ita kuwa wannan juyar ko yanzu naso saika saketa wallahi" Banɗaki na shiga na tsaya kawai ina murmushi wallahi sai ji nayi na doku da ƙasa tim, wuji_wuji suka yi dani suka danfarani da ƙasa. Kunji fa sabuwar ƙaddarar data sake dirar mana. Ohh ni Hundu ɗiyar Baba sojanmu Mrs Bukhari.TSURON TSIRIN... TSANDAURI...