← Book details Tsuron Tsirin Tsandauri Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 77

Sashe 12

Tsuron Tsirin Tsandauri Part 1 Complete Hausa Novel · about 2 min read

yaran matan ma. Sabida gyaran da nake yi ya ɓoye haƙiƙanin shekaruna. Fuskata na kalla ba'a taɓa cewa ni mummuna bace in ba'a kirani kyakkyawa ba to za'a kirani tsaka tsaki. Rama nagani sosai a fuskata wuyana harya fitar da ɗan ƙashi a cikin kwanakin da basu wuce kwana ashirin da wani abu ba. Namiji kamar bom yake wajen iya tarwatsa rayuwar mace yayi mata dameji. Shafe jikina nayi da mai na bi da humra. Doguwar rigar yadi na saka na shafe kaina da man chebe. Kiran Innarmu nayi na sanar mata zanje Abuja gobe kuma inna dawo gidan zan nufo kai tsaye in ɗakko yara. Saida na gama wayata da'ita na fito na shiga Kitchen duk yaran suna Kitchen ɗin sunata hira suna dariya. Tare muka yi girkin a tukunyar yau muka ci abincin a cikin Kitchen ɗin muka zauna Asama'u ta shinfiɗa mana ƙatuwar tabarma. Kitchen ɗin yana da girma dan yayi falona girma inajin daɗin aiki a ciki sosai, kuma ana sha'awar Kitchen ɗin sosai. Gaga_gaga washegari sassafe muka fito na garƙame ɓarayina, har ƴar ƙofar dake sada mutum da ɓarayin nawa saida na kulle. Dake sassafene ban bi takan matan gidan ba Azgar ya tuƙani zuwa gidan rediyonmu su kuma suka wuce da motar gidanmu. Mota aka bamu da direba ni da Ibrahim yana gaba ni ina baya ni kaɗai muka shiga Abuja wajajen biyun rana. Kai tsaye hotel muka nufa kowa ya shiga ɗakinshi, washegari muka halarci Samenar data kawomu. Naji daɗin ganin Badariyya Tijjani Ƙalarawi mutumiyar kirki ga fara'a gata da kirki, ƴar gaye iya gaye. Dariya da aji ya ƙare a wajen Madina Ɗahiru mai shanu gwanar iya sarrafa harshe gwanata. Mun ƙaru da abubuwa da yawa wanda zai taimaka mana ta fannin aikinmu, munyi hotuna munci mun sha kafin taro ya watse, muka koma Hotel washegari sassafe muka nufo Kano ɗaya da rabi a Kano tayi mana kai tsaye na wuce Na'ibawa. Duk fa wannan bidirin da akeyi ban ɗaga waya na kira mijinyawa ba. Ya dai kirani a ranar da muka tawo yaji ko na isa lafiya. Shigewata nayi cikin gidanmu. GIDAN NAGOƊI SHINE INKIYAR GIDANMU KUMA SHINE INKIYAR FAMILINMU.
Chapter 12 · 0% Book details