Sashe 29
Tsuron Tsirin Tsandauri Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Bata ciki ne Hindun Yaya Jamila? " Cewar Mijinyawa da yake jin faɗuwar gabanshi ya tsananta yana jin juwa na neman kayar dashi. "Bata ciki bugun duniya da muka yi bata ciki. Fisabilillahi mun kwaso yinwa ace ana bikin mijinki guda, ko aikin ta tafi oho dan dai naga Hindu na mutuwar son aikinnan nata. Kuma ba komai bane sa take ta tozartaka a idanun abokai ta nuna musu iyakarka. Ai muddin namiji ya Auri macen data wuce da ajinshi, kuma mai zuwa aiki ta cakuɗu da maza. Wallahi dashi da banza duk ɗaya" Batulu tace. "Yarinya sai girman kai da taurin kai. Da naga ai bata nuna auren ya dameta ba ashe dai ya damentan, da ba tace bata ji ba. Amman dai ta tabka mana tsiya ga ruwa ga dare" Qasimu ne yayi magana. "Yaya Jamila ku je ɓarayin Uwalate ku jira, Nanno kuyi haƙuri. Bari muje a kawo muku abincin da zaku ci kawai. Gawata mujenku" "Au bazai kirata tazo ta bamu abinci ba sai dai ku siyo mana? Hindu ta samu dama taci galaba a kanmu ta wulaƙanta banza? Kaga yadda ruwa ke dukanmu muna tsiyayar ruwa fa" Waje ya kaure da sowar mata, Nanno da kishiyarta dai babu kalma a bakinsu, cika suka yi sukai fam. Hannun Mijinyawa Qasimu yaja abokansu suka biyosu Sai a babban gidan ci da siyar da abinci suka siyo musu soyayyar shinkafa da dafadukan shinkafa sai zoɓo da kunun aya ai kuwa Mijinyawa yaji a ajjihunshi sosai. Basu koma ba saida Qasimu ya siya ma duk abokansu abinci a cikin ci ka yar da abun sha kana ƴan wajen aikinsu sukai musu sallama suka wuce ƴan Jama'are kuma suka koma can gidan mijinyawa Qasimu ya basu abincin, nan ya tarar Nanno tana masifa itace harda kuka wai Hindu taci mutumcinta, ta tozartasu a idanun ƴan Jama'are. Mijinyawa kuma ya saka ɗan mabuɗi ya buɗe musu falon Hindu fes_ fes dashi gwanin sha'awa komai na zaune akan tsari. Ga ƙamshin turarukan wuta na Mrs BUKHARI yana tashi a ko wanne kusurwa, ya cakuɗe da ƙamshin fenti, da ƙamshi sababbin kaya. Ƙoƙarin buɗe ɗakinta yayi sai yaji ɗakin a kulle ya duba duk safaya ki ɗin ƙofofin gidan ya gansu amman banda na ɗakin Hindu kuma yasan yana dashi har a jikin kin ƙofar ɗakinshi ko daya duba bai gani ba, kanshi ya jinjina lallai yasan ya taro mach. Masallaci suka wuce suka yo sallar isha sunyi magriba a hanyarsu ta dawowa daga siyo abinci. Sai da suka dawo kowa ya baje yana cin abinci. Mijinyawa ya zare jikinshi ya shige ɗakinshi ya shiga kai kawo. Wayarshi ya ɗaga ya kira wayar Hindu ya jita a kashe jiki a mace ya sauke wayar zuchiyarshi tana bashi gidan ya kamata yaje ya dawo da'ita zaifi kawai, amman baisan yadda zata kaya ba a gidan. Ga Baba soja da tauri, in kuma ta sanar musu shikenan ya kaɗe har ganyenshi. Amman duk da haka kwanciyar hankalinshi shine zuwan dai. Ai kuwa a ƙagauce ya fito tare da zaran kin mota a ajjihun gaban rigar Qasimu yayi waje da hanzari. Sai ji sukai an wangale mishi get ya fice, haka yai ta tuƙinnan cikin rashin hayyaci. Zuchiyarshi kamar zata tawarwatse a cikin ƙirjinshi haka yake ji, har wani amai ne ke taso mishi kawai. Ajjiyar zuchiya ya sauke ganin motar Hindu a ƙofar gida, hakan yasa ya shiga gidan kai tsaye da ƙarfin guiwa. Bai tsaya gaishe_ gaishe ba kai tsaye a lungun Baba Soja ya tsaya ya shiga yin sallama. Baba Soja ne ya leƙo hannunshi riƙe da jarida ga kakin soja a jikinshi, da hular sojoji mai malama. "Mijinyawa kaine a darennan ga sanyi, kaddai su Azgar kazo ɗauka ne? Shigo daga ciki mana sai kace wani baƙo." Ya riƙo hannunshi suka ratso falon, su Inna Turai da Inna Abida suna falon suna cin abinci a ƙaton tire, Innah Inna Ruwayya kuma littafin turancine a hannunta tana karantawa, ita mai son karance karance littattafan turancice sosai. Tsugunnawa yayi ya gaishe da iyayen mata. Suka amsa tare da taya shi murnar aure. Shi dai da yaƙe aka barshi, kunya kamar zatai ajalinshi. ƙarasawa yayi ya zauna a ƙasa gefen Baba Soja. "Dama nazo in tafi dasu Hindunne naga dare yayi ga ruwa" Baki Baba soja ya buɗe yana kallonshi galala. Inna Ruwayya dafa ta fahimci da matsala saita taso tace. "Muje daga ciki Mijinyawa ganinan shigowa" Miƙewa yayi ya shige cikin falon, Inna da Baba soja suka bishi suka zazzauna. "Hindu bata faɗa maka tafiyar da zata yi bane Mijinyawa, naji kace kazo tafiya dasu, ko Sabira kake nufine?" Ajjiyar zuchiya ya sauke daya tuno ashe semina tace zata tafi fa sabida shi ya mance shaf, idanu ya lumshe yana jin daɗi na ratsashi sosai. "Ta faɗamun na mance ne shaf wallahi, dake nace ta haƙura da tafiyar" "Ta haƙura fa kace? " Suka haɗa baki dukkansu suna tambayarshi. A wulaƙance cike da kallon ƙasƙanci Baba soja yace. "Ta haƙura da tafiya Landan mijinyawa, sabida baka san darajar karatu da ci gababa ko me.? Hindu ai ta daɗe tana mafarkin son yin aiki da Bbc sashen hausa, kuma wannan damar data samu ba kowa ke samun irinta ba ai. Shekara biyu kamar kwanane ai bazai yiwu ma ace ta bar tafiyar ba ina, wannan ai son kai ne da rashin mutumci a gidana za'ayi haka." Inna tace. "Tunda kana da macen da zata kula da kaima ai da sauƙi, wannan yana daga cikin amfanin mace sama da ɗaya a gida, in ɗaya bata nan miji bazai tagaiyaraba. Mu dai mata adda'ar Allah yasa ta gama aikinta a sa'a ta dawo cikin aminci kawai." Shiru yayi kanshi a ɗaure yaji ana maganar Bbc ga maganar shekara biyu, ga maganar Landan, an saka shi a duhu gashi bazai iya musu tambaya ba dole Hindun zaita kira har ya sameta tayi mishi bayani. Amman ji yake yi alƙiyamarshi ta tsaya. A lokacin in aka tsaga jikin mijinyawa ba zata tadda jini ba ya ƙafe tsabar yadda ya hautsine. "Babu damuwa, su yaran fa su fito mu tafi" Baba soja yace. "Ai zamansu anan yafi dacewa tunda dai acan babu mai saka musu idanu. Ita yarinyar daka aura ba zata iya tsawatarwa ba ƙarshenta su ɓige da yi mata fitsara, tunda kaga Azgar ya girme mata, ai zamansu ba gyatumarsu gwarine. Zan fita inje in ji labaran tara saika fito" "To shikenan nima tafiyar zanyi. Inna saida safe" "Allah ya tashemu lafiya" Fita yayi tare da yima su Inna Abida sallamar sai kallonshi suke yi. A ƙofar gida yaci karo da Azgar hannunshi ya ja suka isa gaban motar Hindu. "Azgar ina Hindu taje nasan dole kun sani"? " Hakane Abba mun sani. Tana Ingila ta samu aikin kwantiragi da Bbc sashen Hausa landan. Shekara biyu zata yi" "Me landan fa kace Hindun, shine ba zata faɗamun ba sai kace zaman kanta take yi. Landan Hindu, landan fa Azgar? shikenan" Sai kuma yayi muƙus dan haƙiƙa yasan abinda ya aikata yana da girman da dole Hindu saita horashi. Amman baya jin zai iya shekara biyu ba tare da yaji ɗuminta ya sakata a idanunshi ya roƙi gafararta ba, shekara biyu ai mutuwa zai. Tabbas ya fahimci in yaci gaba da riƙe igiyoyin auren Asama'u to tabbas Hindu zata iya rabuwa dashi shi kuma akan ya rasa Hindu gara ya rasa duk abinda ya mallaka ya rasa kowa da komai, ko da wasa bazai ba maƙiya daman ganin bayansu ba, yasan da yadda akayi aurensu ya kuma san matsayinshi a gidansu Hindu, da irin ɗauki babu daɗin da akaita faman yi, da tataɓurza, wa ma ya taɓa tunanin za'ayi auren. Ajjiyar zuchiya ya sauke. "Shikenan kaje Azgar, ga wannan ku riƙe a hannunku" Ya miƙa mishi kuɗi masu yawan da ko ƙirgawa baiyi ba. Azgar ya noƙe yace. "Ka barshi Abba. Ammi ta bamu wadatattun kuɗin da zasu ishemu har ta dawo. Sai da safe" A tsaye ya barshi baki a sake, bai bar wajen ba har saida Azgar ya shige shagon kwanan samari na gidan kamar ma kuka yake yi, kuma da ƙyar yake magana, idanunshi sun yi jawur har jijiyoyin saman idanunshi sun kumbura, yanayin da bai taɓa ganin yaron nashi a ciki ba kenan. Da ƴar Mijinyawa ya shiga mota ya ja ya koma gida. Yana shiga Ƙawar Nanno Innatu tana kiran wayarshi sai faɗa take yi wai taji labarin Hindu bata gida shine ya kwashi jiki ya bita abinci ma sai a gidan cin abinci aka siyo. "Kiyi haƙuri Innatu bata nanne tayi tafiya aikine ya taso mata naci gaba babba, kuma da izinina ta tafi kiyi haƙuri." "Shikenan ai sarki mai Hindu dama haka suke da baƙar zuchiya masu sunan ko a tarihi jarumtarsu ba irin ta mata bace. Yarinya ta samu ta sakata ta wala kafin ta dawo. Sannan ko da wasa Asama'u ba zata yi aiki ba sai dai sana'a a gida ita waccan data fifita boko sama da Aure shi yasa ma yaran take ganin biyu sun isheta ai, shekara da shekaru ance ma mahaifar ta tursasa maka kuka juya mu dai a haka ruwayar tazo mana. Shikenan sai taje ta riƙe boko Asama'u zaman aure zata yi duk shekara banƙi in tawo suna ba" Illahirin kunya saita cika mijinyawa. Bai iya cewa komai ba har ta kashe wayarta. "Qasimu ga ɗakunan yara zaku iya kwana a ciki kaina ciwo yake yi zan haɗiyi magani in kwanta" "Ai ba sai mun shiga ko'ina ba nan falon ya ishemu gobe sassafe mu kama hanyar ƙauyanmu kuma. Ai kuwa hakan akayi wanka ya shiga banɗakinshi yana yi babu nutsuwa tattare dashi sam, haka ya fito babu komai a jikinshi sabida yana tunanin babu mai shigo mishi ɗaki yana fitowa yaga Asama'u kwance a tsakiyar gadonshi tayi ruf da ciki da wasu fitinannanun kayan bacci masu nuna sura. Da sauri ya koma baɗakin ya ɗauro tawul a ƙugunshi ya fito. "Me kika zo yi ɗakina gida cike da baƙi, falo cike da maza, wannan wacce iriyar fitsara da rashin ta'ido ce Asama'u wai ubanme yake damunki ne haka?" A yadda yayi maganar babu wasa bare wargi ya ɗaure girar sama data ƙasa tamau, tare da kawar da kanshi daga kallonta. Zama yayi a kujerar