Sashe 54
Tsuron Tsirin Tsandauri Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
kawai zan dinga siye akwai kuɗi a hannuna fatana shine ka kula mun da kanka kuma kar ka wuce sati biyu ka dinga waiwayowa kasan ka sabamun da kwanciya a jikinka kana yi mun hira mai daɗi, ni inta kama duk sati ma ka dawo abunka." "Hmm Tutar so kenan Allah ya hore mun in kula dake yadda ya dace in kaiki birni in sakaki a makaranta ki cika burinki na son zama ƴar jarida, a lokacin ko aiki na fita nayi kuɗin sukutum zan dinga baki wallahi sai yadda kika yi dani. Kai da kaya duk mallakar kuya ne" Dariya muka yi dukkanmu nan muka ci gaba da tattaunawa, kwana biyu da wannan maganar Mijinyawa yabi abokanshi suka wuce Azare ya rage ni kaɗai sai karatun littattafai suka zame mun ababen ɗebe mun kewa, na koyi abubuwa da yawa a karance karancen da nake yi kusan ma littattafan hausa shi ya wayar mun da kaina fiye da tunani kuma nasan bani kaɗai bace. Marubuta madubaine ko kuma walƙiya masu iko da tararrafin hasko rayuwar Al'umma su haska ma duniya su wayar da kan matan da basu da damar da zasu iya fita suyi cuɗanya da mutane su samu wayewar kai. Basu da damar da zasu san abubuwan da dama saita hanyar karance_karancen a karatune marubuciya zata kutsa cikin rayuwar wasu ma'auratan ta haska muku, wata sai taga kamar da'ita akeyi a sannu tana karantawa tana bi har ta samu warwaruwar matsalarta cikin kwanciyar hankali da izinin Allah. Littatafin hausa jami'ace mai zaman kanta wanda yake da shashe_shashe ya rage ga makaranci ya zaɓi shashen da yake so haka ya rage ga marubuci yasan me yake haskama al'umma ya sani shi madubine abun koyi, shi malamine mai gyaran tarbiyya da gyaran gidajen aure, in wannan ɓangaren ya zaɓa. In kuma yabi masu tutuya da adabin bariki, masu haska mana rayuwar mata ƴan maɗigo, da mata karuwai, ba tare da nuna illar hakan ko da a ƙarshen labarin bane, to kunga wannan aikinsu na wargaza tarbiyyar al'ummane da nuna ma yaranmu kai tsaye hanyoyi da dabarun biya ma kai buƙatar sha'awa da Allah ya halicceta a jikin ɗan adam. Wa'iyazullali. Madallah da duk marubutanmu na da dana yanzu, madallah dake Mrs BUKHARI. Bayan tafiyar Mijinyawa da kwana biyu na isa ɓarayin Nanno nayi mata share_share bata ko yaba ba, bama ta nuna tasan nayi wani abun yabawa ba. Ƙorafinta shine ni kullum ɓarayina a kulle sannan in an ganni a tsakar gidan ruwa nazo ɗiba ko kuma na fito a gaisa da safe ne. Audiga nasa na toshe kunnena domin bazan iya wannan zaman ba, sai kuma ta tsiro da cewa mu haɗu ni da uwatale mu dinga hira, nanma na nuna bana so Baraka ce ma dai jininmu ya haɗu da'ita. Ta shigo mun sau biyu bayan tafiyar su Mijinyawa, ni bamma samu damar shiga ba, nafi sha'awar zama ni kaɗai littattafan Hausa su zamemun ƙawaye. Tun ana jibi sati biyu da tafiyar mijinyawa na soma gyaran jikina dilka dama da'ita nazo mai dunƙule dunƙule wanda baya komai ko shekara zai yi ( Dilkar sirrin matan sudan kenan. Mai saka laushi da fito da ainihin kalar mace, mai danƙarar, dauwamar da ƙamshi a fatar mace, musamman ki haɗa da turarenmu na turara jiki wato dukkhan Hajiya tare set ɗin nasu yake. Akwai wannan Dilka a wajena da kin shirya ki yi mun magana ni Mrs BUKHARI ga lambar wayata 081_79523215 saina jiku) Magungunan matana nagartattu, ingantattu na wajen Surayya D (08032773332) dana zo dasu bansha ko ɗaya ba, in banda sanyi fulosha na dama nayi ɗibge ɗibgene sai na shiga tsifar kaina Baraka tace zata rakani gidan wata mai kitso data iya itama ƴar garinmu ce Maiguduri, ta iya kitso cikin kwana ɗaya na tsefe kitsona fes da daddaren na tashi da lalle yayi duhu kalar jinin kare dashi, dake akwai ragowar na biki da bai fita ba, yi ɗaya nayi amman ya kwanta yayi lub. Wajajen ƙarfe goman safiya Baraka ta shigo bayan na fito sai na tafi neman izini wajen Nanno. "Mijinyawane zai dawo aka ce mun tun shekaranjiya kike juyin ɗaki ko yaya, ga kitso kince zaki je? " E haka nake saka rai sati biyu yace mun zaiyi ya dawo" "Sati biyu, ke Baraka sati biyu Qasimu yake yi ne ya dawo daman?" Baraka tace. "A'a wani sa'in wata ɗaya wata biyu ma kafin ya dawo amman bai taɓa dawowa sati biyu ba" Shiru tayi can tace sai mun dawo. Muna tafe muna hirarmu a ƙafa muka je unguwar dake babu nisa kuma inason ganin gari. Gidan kitson munje mun tarar da wata mata anayi mata amman ita baƙuwace ma ta shigo ziyarane shine tazo ayi mata kitso. Bamu daɗe ba aka gama mata ni kuwa sai da akayi awa biyar ana abu ɗaya danma tana da sauri sosai guda ɗari da shittin akayi mun wajajen dab magriba muka isa gida, Nanno tai ta faɗa kishiyoyinta na tayata daga baya kuma suka shiga bata haƙuri. Raina ya matuƙar ɓaci sosai amman haka na bata haƙuri na tafi shashena. Washegari wajajen azahar na gama girkina tsab na zuba kwalliya ko ina tsab ga ƙamshi ta ko ta ina, ina jiran miji shiru_shiru sai dab magriba na jiyo ihun yara suna mishi oyoyo ajjiyar zuchiya nannauya na sauke. Jakar kayanshi aka shigomun dashi, shiru_shiru shine har sai bayan isha ya shigo hannunshi da tsarabar da yayo mun Nanno ta ɗibi nata dana matan gidan. Babu walwala sam a tattare dashi duk da ganina cikin ado da kwalliya ya sanyaya ranshi amman damuwarshi ta kasa ɓuya. Wanka na taimaka mishi yayo na kawo mishi abinci na tusashi gaba inaji kamar yau sallah. "Tutar so kinga yadda kika yi kyau abunki, fatarki sai sheƙi take yi. Kamar kitso kika sake ko?' Kafin ma nayi magana ya zame mun ɗaurin nawa ya shiga shafa kan nawa wanda ya sha kulaccam ta gashi mai bala'in taushin ƙamshi sai da ya lumshe idanunshi. ( maza dai ki zauna Abulle kada ki motsa ki lalo kuɗi kizo in fiddaki kunya da kayan ƙamshi. Su Khadija da Kattime anata abun arziki ke an barki a baya. In kinga dama ga lambata ki kirani in fiddaki 081_ 79523215 mrs BUKHARI GIDAN ƘAMSHI) "Kitso da lalle yayi kyau wanda akayi dominshi ya yaba, gashi ko ya kika motsa ƙamshi kawai ke fitowa a jikinki, mala'ikun Allah ku shaida Allah yai ma Tutar so albarka ni mijinta na ɗaga ƙafata ta shiga aljannah. Nayi kewarki fiye da kewar daddaɗan girkinki harma bansan da wanne zan soma ba" Da ƙyar na lallaɓashi yaci abincin muka wuce ɗaki. Sai da asuba na tattare komai. Yau saina wayi gari garau dani sawai nake jina babu nauyi. Da kaina nayi ma Mijinyawa abun kari duk da uwatale ke da girki ban tsaya jiranta ba, ɗumamen tuwo ta miƙo mun babu ko shayi bare kokko. Muna karyawane mijinyawa yace dani. "Tutar so jiya dana dawo Nanno tayi mun faɗa sosai akan dawowata, ta dinga take tsikara ba tanan take jawowa ba. Sannan ta kafa mun dokar sai dai in dinga yin wata biyu kafin in dawo kamar yadda Qasimu da Abdulƙadiri suke yi. Hankalina ya tashi sosai ko da safennan da zancan naje mata taƙi fur wallahi. Ya zanyi da kewarki da rashinki nisan yayi yawa Tutar so ina buƙatar matata a kusa dani, sannan na miki alƙawari bai kamata in saɓa ba. Bansan mabuƙaci bane ni saida na aureki na ɗanɗani zumarki sati biyunnan ma a daddafe nayi shi ina ga wata biyu daga yin aure ko amarcin bamu more ba." Ajjiyar zuchiya na sauke domin a lokacin kaina ɗaurewa yayi na rasa abinda zance. Kar ka damu zamu tattauna a nutse kaji? Yanzu ka daure ka ture duk wata damuwa babu abinda zai gagara, Allah shi ke da tararrafi akan bayinshi" "Ai bazan iya turewa bane inaso gobe zan kai ma Kawu ziyara in faɗa mishi halin da ake ciki ko akwai taimakon da zai mana shine kaɗai mai tafarrafin faɗama Nanno taji" Amman kai kana ganin yin hakan daidaine kar taga kamar ƙararta aka kai kuma ya zama wani abun daban mijinyawa, naga a wajen Nanno komai na faɗa ne. Ka daure kawai kaje ɗin ayi yadda tace ɗin wata rana sai labari babu abinda yake dammawa face ƙudurar Allah shine mai tasarrafi da buwaya, kuma gagara misali" Da ƙyar na shawo kanshi ya amince ya bar maganar. Badan komai na hanashi kai ƙara ba sabida abu biyu ne bana son su san logona domin dashi za'a iya kaini ƙasa, na biyu bana so hakan ya sake ruru wutar rikicin da kullum ruwa nake yayyafa mata. Bayan dawowarshi da kwana biyu da safe yana mana wanki a banɗaki ni kuma na dasa kujera muna hira shine yake sanar mun ai ba Azaren ma suka je ba cikin garin Bauchi suka shiga anan suke ciraninsu Mijinyawa yace shayi yake siyarwa da ƙwai. "Wani mai shayine zai koma garinsu shine ya siyarmun da komai nashi naci gaba da yin shayin a inda yake yi dake na shiga da canjina a hannuna. Shi kuma Qasimu teburin lemo ne dashi Abdulƙadiri kuma aiki yake yi a tasha sai dai duk wajen kwananmu ɗaya. A tasha muke kwana rumfar wata mai tuwo_tuwo a saman bencinta washegari kuma mu biya nera goma_goma muyi wanka mu kimtsa ko wanne ya fita wajen nema kinji sana'ar da nake yi, kuma da riba babu laifi in faɗa miki kinga in Allah ya dafa sai kiga mun koma Bauchi da zama na saka ki a makaranta kin cika gurinki na son zama ƴar jarida" Shiru nayi ina tallafe da kumatukana dukka biyu. Kumfa ya watso mun nayi firgigit na kalleshi. "Tunanin me kike yi kika barni inata zuba Tutar so? Ni na zaci murna zaki taya ni tunda ba ɗaukar kaya nake yi a ka ba. Ko kina tunanin kamarki ace mijinki shayi yake saidawa ko? " Ko ɗaya bana wani abu daya danganci nadamar kasantuwata iyalinka abadan. Ni dai fatana mijinyawa ka riƙe ni da amana kaga na rabu da ƴam uwana, na rabu da kowa sabida inzo nan in rayu dakai" "Kar ki damu mijinyawanki mai ƙoƙarin yaga ya saka miki da mafiyin alkhairin da kika yi mishi