Sashe 23
Tsuron Tsirin Tsandauri Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
uku cur ƙafafuna basu sake taka turakar Babanku ba na yafeshi gabaki ɗaya ya kaɗa ya raya naƙi fur wallahi, gashi a fuska babu canji, a girmamawa babu canji, a kwalliyata da abincina duk babu canji. Hindu da ƙyar da jiɓin goshi na haƙura muka shirya a hakanma saida ya bani miliyan guda yace in ƙara jari banda alkhairai da yake tayi mun. Kinga a cikin ruwan sanyi na dafashi ba hargowa ba fishi, daga ranar bai sake bari abu makamancin haka ya shiga tsakaninmu ba, fishi wannan baya so inyi gudun kar kwanana ya zagayo in ƙi zuwa turaka. Hindu in kin yadda kina da abinda ke gamsar da ƙishin ruwan Mijinyawa, kuma kin yadda ke macece cikakkiya wacce tasan kanta, in kin yadda kina da kima da daraja, kuma kinsan ƙwallonki tana shiga raga da kyau. To ki koma ɗakin ki kiyi yaƙin gidanki da kanki kamar yadda kika saba al'amuranki ba tare da sanin kowa ba. Na sanku bakwa bin bokaye dan ban ɗauraku a wannan gwadaben ba, nasan bakwa sharri shima. Amman ban yadda kuyi zaman boranci ba. Kin ganni ban taɓa zuwa kai ƙara gida ba, a dangi har misali akeyi dani. Kuma babu abinda ban ƙunsa ba da kike ganina saida na tashi tsaye na dena shakkar kowa na zama mafaɗaciya haiƙan kana na zama mai cikakken Ƴanci. Da ba haka nake ba a lokacin kuna yara baku san komai ba" Innarmu ta dinga wanke mini kaina da dabarbarunsu na manya na dinga tarawa da nawa dana sani da gogewar da nake dashi, tuni naji babu duk wani ƙunci a cikin raina illa iyaka na zafin Mijinyawa da bana jin akwai ranar da zan dena ji. Amman fa inanan kan bakata wallahi bazan zauna ba. Innarmu ta harhaɗomun magungunan gargajiya, itace harda bani kyautar atampa da mayafi duk dan ta sanyaya mun raina. Uwa kenan. Haka ta wuni tana lallaɓani. Allah sarki duk wanda ya rasa kafaɗar uwa dole a koka mishi, in banda uwa wa zaima wannan? Sai da yamma lis na bar gidan, dama bani da asament yau duk da ya kamata in kasance a wajen aiki bazan rasa abinda zanyi ba ko da editin zanyi. A hanya na tsaya na sai banƙararriyar kazar gidan gona, da masa, na biya shago na sai jus na cikin kwali na nufi gida. A tsakar gidan na tadda Mijinyawa a zaune a kujera yayi shiru yana kallon fulawowi yaga na shigo. Fitowa nayi da ledata duk maiƙo na nufoshi da fara'ata. Ranka shi daɗe ango hutawa akeyi ne? " Kallona yayi muka zuba ma junanmu idanu na ɗan lokaci. Shigowar Uwatale ne yasa duk muka juya sabida sunana data ambata. "Ashe kuma Mijinyawa ya kai sadakin Asama'u har an saka rana? Allah mai iko kenan, girman ɗan mutum babu wuya" Wallahi ai inata so ma inna dawo in shiga in faɗa muku to dawowar tawa kenan " Da fara'a a fuskata ta kalleni da kyau taga babu damuwa a tattare dani. Mijinyawa muje daga ciki na kwaso gajiya" Tsohuwar munafukar a wajen muka tafi muka barta sai daga baya ta biyo mu a baya a baya. Sabira ce kaɗai a falon tana zaune tana kallo. "Sabira ku shirya ke da wanki in anyi sallah zamu je cin abinci ko? " Cewar Mijinyawa. "To Abba dama mun riga mun shirya Ammi kawai muke jira ta dawo" Murmushi nayi ma yarinyar nace. Gashi Ammi babu inda zata iya zuwa aikin da suke kaina da yawa kwa tawo mun dashi. Bari in kwatsa ruwa" Na faɗa tare da shigewa ciki. Banɗaki nayi shigewata shi kuma ya zauna a kan gado. Harna fito yana zaune, da ɗan ƙaramin tawul a jikina nayi zamana a gaban madubi na dinga bin fatata da love neture na kamfanin Oriplem wanda nake siya a Hannun Mamanmu Hajara Aliyu da lotion ɗin da oil ɗin harma da sabulun wankansu na ruwa dashi nake amfani fatata kullum cikin sheƙi da laushi. ( ni kaina Mrs Bukhari shi nake shafawa kuma yana gyara fata sosai ga laushi ga sheƙi, ga ƙamshi mai daɗi da riƙe jiki) Yana zaune harna saka kaya riga da wando falazo na saka ƴan kanti na feshe kaina da humrar gashi na saka hula. "Tutar so wannan shirun yana dafani sosai" Juyowa nayi nace. Wanne shiru kenan, naga duk abinda kace saina baka amsa ko? " Sai ya zabura ya iso inda nake a tsaye ya mannani a bango tare da riƙe ƙunƙuruna. "Kiyi haƙuri wallahi nasan abinda akayi miki da zafi sosai. Amman Tutar so umarnin Nanno nabi dole inyi abinda take so in dai inason in rabauta. Ko ɗigon son yarinyar babu a raina, ni bansan ma ya wannan lamarin zai faru ba, bana ji a jikina Aurennan zai yiwu. Ni yarinyar ce ma nake jin kunyarta bansan ta yadda zan iya rayuwar Aure da'ita ba yarinyar da take kallona a matsayin uba" Ammm Mijinyawa naji zafi, zanji zafi duk bashi bane. Aurene dai babu fashi Allah ya sanya alkhairi bana son maganar ma aita nanatawa dan Allah" Ina kaiwa ƙarshe na cire mishi hannayenshi a ƙuguna na koma banɗaki nayi zamana akan sita har saida naji ficewarshi zuwa masallaci kana na fito na tada kabbara nayi sallah na jawo ledar kazata na baje na hau tutturawa ina korawa da jus nice harda saka film a labtop ɗina inayi ina kallo A haka ya shigo cikin shiri ya sameni. "Da gaske ba zaki zo muje ba? " Gaskiya na gaji kuma ina da abun yi" "To mun tafi me za'a tawo miki dashi? " Ni kam Alhamdulillahi nagode Allah ya tsare" Haka yayi ficewarshi. Daga wannan rana na sake canja takuna sosai anata tsogumi a danginsu Mijinyawa, da dangin iyayen ita Asama'unma. Ranar asabar saiga masu fenti sun wuce can cikin gidan ɓarayin dake kulle sun soma fenti haiƙan wuni suka yi suna abu ɗaya. Washegari sai ga mota tazo mijinyawa ya sameni a ɗaki yake sanar dani za'a kwashe komai na falona da cikin ɗakina zuwa gobe kuma za'ayi fenti jibi za'a kawo wasu sababbin kayan. To kawai nace mishi. Aka kwashe komai har maƙota sun shigo tsogumi a tunaninsu ko na tada fitinane aka sakeni shine ake kwashe kaya. Sai da suka shigo su munafukan gidan da duk suka fito tsakar gida shine suke shaida musu gyara za'ayi mun. Ni da yara gidan Yaya Saratu muka wuni sabida fentin da za'ayi. A nanne nake sanar mata abinda ke faruwa daga ni sai ita. Jin Asama'u za'a auromun ta hau zage_zage ni kuwa sai kallonta kawai nake yi. Ita ta kira dukka ƴan uwana take sanar musu halin da ake ciki. Nan fa duk suka ɗauka Yaya Zakiya ma garzayowa tayi tazo ta samemu sukaita zage zagensu ita da Yaya Saratu. "Shi yasa ni tun farko banso aka bata yarinyar ba, yarinya da uwarta a raye ace an wani kyautar da'ita dan kawai ubanta ya mutu. Babu mamaki dama sun daɗe da son haɗa auren fa ƙila ma tun tana tsumma aka bashi ita" Rayya tace. "Nifa in nice wallahi Allah sai dai mu rabu yaje ita ya aureta ko ya haƙura da'ita muci gaba da zama." Yaya Saratu tace. "A.a in tayi haka kuma dama haka danginshi suke son ayi fa. Saida ta gama wahalarshi tukunna zata rabu dashi? Ai a wannan gaɓar in tace sakin take so da yanzu ya tafa mata takaddarta. Gara tabi a hankali ta ƙwaci ƴancinta lokacin da zata ce ya zaɓa yana nan zuwa" Sukaita tattaunawa ni dai ina tsakiyarsu ina jinsu kawai sai wajen magriba na ɗauki yara muka tafi. A mota suka tutsiyeni da tambayar Aure wai Abbansu zaiyi. Na sanar dasu har kwanakin daya rage ranar auren amman ban iya sanar musu wacce za'a aura ba tukunna dai bansan bayanin da zanyi musu su gamsu ba. Munje gida ko ina yasha fenti mai tsada da kyau, har fentina yafi na wancan ɓarayin na Amarya kyau da tsada. A katifu muka kwana washegari litinin sassafe Mijinyawa ya fita. A gurguje na fito nima dan yau ƙauye zan shiga ɗakko rahoto ma, gashi saina je office tukunna. A bakin titi naga mijinyawa na taran abun hawa yana ganina na miƙe abuna wallahi kallo bai isheni ba, motata ce dai ya bar hawa. Dana je office ogana yake sanar dani tafiyata ranar Juma'a wanda yayi daidai da ranar da mijinyawa zai angwance da amaryarshi. Muna zaune ni da Luba nake shaida mata auren da Mijinyawa zaiyi da wacce zai aura ɗin. Luba harda kukanta ni dariya ma ta bani. Haba Luba menene na kuka Aure fa nace miki za'ayi ba wa jo ko ba" "Hindu mazan wannan ƙarnin haka suka lalace wai. Yanzu duk irin wahalar da kika sha da Asama'u itace zata zama kishiyarki daga ƙarshe ki shiga turaka ta shiga itama wannan turakar? Allah ya kiyaye wuce nan nu Hindu, ta shiga turaka dai. Ai ko yanzu bana tarayya dashi balle in sun yi aure. Luba kenan kin mance wace Hindu ne ma. Ai ni da turaka har abada" Murmushin takaici tayi tace. "To aure yana yiwu ne babu tarayya Hindu ballan tana nasan ke mabuƙaciyace sosai? " Luba in kika ji ana ƙi gudu sa gudune baizo ba buƙatuwar abu ta kazan... Kinsan inna juya ma abu baya har abada bana waiwaye Luba. Ai aurenmu ba na zobe bane duk ranar daya gaji zai sakeni. In kuma bai gaji ba saimu dauwama a haka. Ba zan kashe kaina akan ɗa namijin da baisan darajata ba." "To Hindu gida ɗaya zaku zauna? Dariya nayi mata. A. a ba zamu taɓa zama inuwa ɗaya da Asama'u ba Luba har shi mijinyawan ma." "Ƴan hayar gidanki zaki tasa ki koma ciki kenan Hindu? " Ashe kin gane Luba. Ke zan ɗaura akan aikin gyaran gidan sabida ni ranar da za'a ɗaura Auren ranar jirgina zai tashi zuwa landan. Kafin in dawo an gama komai an zuba mun komai sai tarewa a ciki kawai" Shiru tayi tace. "Yanzu da ace nayi dubara irin taki wallahi nima da babu abinda zaisa in tare a gidan Sunusi. Ke Hindu ina kwasar baƙin ciki" Luba ke kika so ki kwashi baƙin ciki. Kinga gidannan dana siya ban siya da tunanin zan zauna a ciki ba, wannan