Sashe 38
Tsuron Tsirin Tsandauri Part 1 Complete Hausa Novel · about 10 min read
TSURON TSIRIN...
TSANDAURI
LITTAFIN BADIAT IBRAHIM MRS BUKHARI GIDAN ƘAMSHI
LAMBA TA GOMA SHA ÆŠAYA
*Bojuwa herbs*
*By*
*Surayya Dee.*
*08032773332.*
*Sanyi flusher!*
*Yana wanko dukkan sanyin mara, mahaifa Har ma da jijiya.*
*Tasirin da karfin maganin sanyinmu ya wuce misali don kuwa duk wacce ta siya sai ta dawo ko ta turo wasu*.
*Alhamdulillahi Allah ne ya yi mana.*
*Tightening set na hade mace ta dawo zamzam tamkar yar budurwa, kuma babu na insert a cikin park din*.
*Tasirin magani idan andafa tamkar yankan wuka ne shiyasa kazar sababi da ciccibin garari na Surayya halin yau suke da kyau da tasirin gaske a jikin mace.*
*Muna da gimbiyar zabuwa da tattabarun alheri.*
*Akwia packages na mussaman ga amare, uwargida, zawarawa da masu jego.*
*Tuntubeta a wannan lambar*
*08032773332*
*Don samun ingantattun kayan gyara da babu algush.*
*Nation wide delivery*.
Sun jima sosai dan sunfi goman dare suna abu É—aya, Baba Sojanmu gaskiya bayayin ta daÉ—i. Nasan sai da safe kuma za'a neme mu koma menene Lokacin zamu ji.
Wajajen goma da arba'in bacci ya soma ɗibata muka jiyo muryar Baba Sojanmu yana ta zage_zage da turanci ranar ba hausa halamun ɓarin rai mai tsanani kenan in muka ji yana zuba turanci.
tom yau dai nasan lallai ranshi ya ɓaci a zafafe ya shigo ɗakinmu Innarmu ta miƙe da sauri
Matsar da'ita gefe yayi yasa hannu ɗaya ya fincikoni a maulidi, sai gani a ƙasa a gabanshi.
Duka ya rufeni dashi yana tattakani da ƙafarshi da dukkan ƙarfinshi yake dukana, ni kuma inata kwarmata ihu. Bel ya zare ya dinga labtamun tako ta ina inata ihun ceton rai dan wallahi dukan sa'a yake yi mun, kuma duk wannan dukan babu ƙidon hawaye a idanuna sai dai idanuna sunyi jawur a halittatane da wuya abu ya sakani kuka zuchiyata bata fiye tsinkewa ba ina da dakiya da jarumta sosai gaskiya.
Cikin ƙanƙanin lokacin aka taru a ɗakinmu Innarmu na zaune a bakin ƙaramin gado ta hau tayi fam, magana wannan bata yi.
"Wai lafiyarka ƙalau kuwa Ganaral ka saki yarinyarnan haka in ba kasheta zaka yi ba, da ƙarfi irinna sojoji zaka daki Hindun"
Cewar Baba Dogara da ya rirriƙe Baba Sojanmu da ƙarfinshi na gidan soja ya fincike da ƙarfi sosai.
"Ai gara in kasheta data kasheni da baƙin ciki kai kaga komai a kan idanunka komai ya faru, yaro bazai kasheni da baƙin ciki ba, sai dai shi ya mutu" Da turanci irin manyannan fa yake magana yaƙi hausa fur.
BuÉ—ar bakin Innah Abida sai cewa tayi.
"Ciki tayo ne hala? "
Wannan kalmar ta girgiza zukatanmu ni da Innarmu amman dake a cikin maÉ—aukakin fishi take bata tanka ba amman martani dole ne kamar cin bashine da ko ka mutu sai an biya maka.
Baba NagoÉ—ine ya balbaleta da faÉ—a duk ya kori matan da suka cika falonmu suna son jin gulmar me ya faru.
Baba Lukumanu ne ya fito da Baba Sojanmu yana ta gwarancensu na sojawa.
Ina durƙushe na kasa ko da tashi ne jikina yayi laushi kuma ya farfashe.
"Tashi Hinduwa koma me kikayi baki cancanci duka haka ba.
Bari ina zuwa"
Fita tayi sai gata da ruwan ɗumi da tawul ta dawo a bakin gadonmu ta zaunar dani ta gasamun jikina a Lokacin zazzaɓine kau a jikin wanda ita kanta saida ta tsorata, a darennan a kaina kusan duk ƴan falonmu suka kwana makarainane suka motsa irin motsawar da basu taɓa yi ba, a da basa magana sai dai su rabkeni in ta shan wahala amman a wannan rana sukaita zage_zage da alwashi iri_iri sukaita bige_bige da fisge_fisge dan da ƙyar aka iya danneni. Shi Baba Sojanmu bai yadda da makarai ba. Ko kuma ince bai yadda makarai na shiga jikin mutane ba, tunda duk musulmi yasan akwai Aljanu tunda sura garesu sukutum a Qur'ani, kuma su suka soma zama a duniya kafin bil'adama.
Baba Lukumanu ne suka rufu a kaina akaita mun adda'a ana tofamun kafin suka lafa na samu bacci bani nasan me nake ciki ba sai bakwai na safe.
Fuskata ta kumbura sosai abun tsoro da Innarmu ta fito dani zanyi alwala sai da hankalin kowa ya tashi harda Baba Sojanmu dan hatta kaina saida ya ƙara girma baka isa kace nice ba. Amman Baba Sojanmu dakewa yayi, ya nuna ko a jikinshi sai turanci yake yi.
Alwalarma yi mun akayi na dawo nayi sallah a zaune.
Jikina babu daÉ—i sam, matan gida sukaita shigowa dubani tare da jajanta abinda ya faru.
Da Innah Abida ta leƙo tana gaisheni da jiki banza muka yi da'ita har ta saki labulen ta koma.
Jamila ce tayo sallama ta leƙo.
"Innarsu Saratu ana nemanki dake da Duwaf a falon Baba NagoÉ—i"
"Jeki gamunan, Hindu zaki iya rarrafawa muje ko inje ni kaÉ—ai? "
Ni ba raguwa bace duk irin ciwon dake jikina da irin yadda makarai suka luguiguitamun gaɓɓai baisa na sare ba nace.
Zan iya Innarmu"
"Rayya kamo ta ku tawo ni bari in yi gaba"
Miƙewa tayi ta fice mu kuma muka fito a hankali sai kallona akeyi a cikin gida kai tur da gidan yawan daya haɗa haula iri da kala. Masu mayar da ƙaramar magana ta zama babba.
A cike falon yake babu ma masaka tsinke dan da ƙyar muka kutsa na rakuɓe a jikin Innarmu.
"To maƙasudin wannan taron akan bikin waɗannan yaranne. A gaskiya mutum takwas daga ciki yarane na sanannun mutane anan cikin garin Kano face Saurayin Jamila daya kasance ɗan Gombe bamu da masaniya akan asalinshi amman yana da mastas ɗinshi ma aiki yake yi anan garin Kano.
Sai kuma shi wanda Hindu ta rakito yace ɗan ƙauyen jama'are ne amman asalin iyayenshi daga Jimeta suke jihar Adamawa. Kuma lemo yake saidawa shine sana'arshi. Matakin karatunshi yayi sakandare ta ƙauye shikenan, dan tambayoyin da Soja yayi musu da turanci. A gaskiya bai amsa ko ɗaya ba, yace baya jin turanci sam"
Nan ɗakin ya hau hayaniya da ƙus_ƙus.
Innarmu tayi mun wani irin mummunan kallon da saida nasha jinin jikina ba shiri na É—an muskuta daga kusa da'ita.
"Sabida haka ita Hindu an soke Aurenta da Gawata zamu haÉ—ata Aure da Qazzafi wanta shi yafi cancanta da'ita. Yarannan sati mai zuwa iyayensu zasu tawo mu gana zamu tsayar da lokaci amman bazai É—auki lokaci ba ku zauna da shirinku kawai. Kuma sun amince ba batun karatu da aiki da Soja ya sharÉ—anta musu. Da sharaÉ—in ko gaba suna son yin mastas ko phd zasu basu dama, duk kuma sun amince kasancewar suma daga gidan boko yawanci suka fito"
"Ina da magana. Ban yadda da wanda Hindu ta kawo a matsayin miji ba hauka tayi ma shi yasa ta kawo mana shi sabida rashin hankali. Amman kuma ban yadda ta auri Qazzafi ba. Babu ta yadda za'ayi a haÉ—a wannan Auren wallahi"
Cewar Innarmu dake yinƙurin tashi.
Baba Sojanmu yace.
"Sabida ke kaÉ—ai kika haifeta ko? "
"Ko bani kaɗai na haifeta ba ina da hakki nima a kanta. Banga abinda zaisa ka shiga lamuran yaran maƙota ka ƙwato musu hakkinsu ba. Sai da yazo kan ɗiyarka kace ba zaka tsaya mata ba.
Ba wanda za'aima Auren dole ehe nasan rait É—ina kuma ina da rait a matsayina na uwa"
Ficewa tayi fuuu ni dai ina zaune tsamo _tsamo dani.
"Ai kaga illar bokon da aketa nuna maka baka ji. In banda Ruwayya cikin matanka wake maka wannan fito na fito ɗin? Babu sabida su ƴan boko daka taɓasu zasu ce sun san ƴancin kansu suna da hakki. Ke kuma Hinduwa kinga abinda kika jawo mana akan wani bagidajen ɗan ƙauye tantagarya."
"Hmmm ai kamar yadda Ruwayya ta nuna ƙin kinina a fili to muma mun fasa auren sai dai a haɗata da wani a gidan ga samarinan iri da kala a cikin gidan kuma ko wanne da iliminshi"
Wani kallo da Baba nagoÉ—i yayi mata ai ba shiri ta kame bakinta.
"Kuje an sallameki"
"A_a Baba kuyi haƙuri ku bani Gawata wallahi shi nake so mutuwa zanyi in ba'a bani shi ba. Qazzafi bana son shi"
Salati falon ya É—auka kawai ni kuwa ko gezau iyakar gaskiyata nake faÉ—a dan yanzune na É—aura É—ambar son Gawata."
Miƙewa Baba Sojanmu yayi aka yi saurin riƙeshi.
A daddafe na shige É—akinmu na kwanta Innarmu bata É—akin sai Yaya Saratu da suka zo babu mamaki sunji labarin abinda ke faruwane.
Luba ce ta shigo a sanyaye bayan sun gaisa da su Yaya sai akai kiransu suje Inji Baba NagoÉ—i. Suna fita Luba tace.
"Kinga abinda nake ta jiye miki ko Duwaf? Dama nasan babu mai ƙaunar Gawata a gidannan inata jan kunnenki ƙin ƙi ji dama taurin kan tsiyane dake. Jiya ihunki har waje duk unguwa ta ɗauka anata surutai iri da kala.
Gawata bai daÉ—e da barin gidanmu ba Hinduwa ya bani takadda yace in baki, yazo tare da abokinshi mai lemo dake sana'arshi a cikin kasuwar Æ´an lemo."
Me yace miki Luba? Kinsan Allah sai dai a kasheni ko in dauwama babu Aure in basu bani Gawata ba."
"Na sanki da taurin kai ai. Takadda ya bani in baki yace mun shi ya koma garinsu baki É—aya"
Ai sai ganina nayi a zaune daɓas.
Takaddar na fiske na buÉ—eta.
"Hindu duk duniya in sun taru ba zasu iya raba wannan ƙaunar ba. Allah shine masanin abinda ke sama, kuma shine masanin abinda ke ƙasa, dana ƙarƙashin ruwa. Shi ya halicci zuchiyar dake gaban ƙirjina Hindu sonki rayuwatane ƴan gidanku suna son kasheni sunce ba zasu bani ke ba Hindu, sunce ilimina bai kai ba, ni baƙauyene, talaka kuma. Hindu ina sonki har abada amman kiyi haƙuri na koma garinmu sabida in nisanta dake in yi jinyar dundumin sonki.
Gawata ne naki mijinki na har abada"
Yawu na haɗiye na duƙunƙune takaddar na kwanta ina nazari.
"Baki ce komai ba Hindu kin kwanta"?
Luba kinga bani da lafiya zan rubuta miki saƙo da kuɗi dan Allah abokinshi ya taimakeni ya san yaya za'ayi saƙon ya isar mishi, inya haura kwana bakwai da kaina zanje garinsu Gawata kuma inna tafi na tafi kenan har abada bazan taɓa dawowa ba."
Baki Luba ta rufe mun.
Motsin shigowar Innarmu ne yasa mukai shiru.
Zama tayi tana fuskantarmu.
"Ke Luba ina Hindu ta haÉ—u da É—an iskan yaron data kawo mana nasan kinsan komai ko ki yi magana ko in haÉ—a dake in dakaku? "
"Mai lemon dake ƙofar makarantarmu ne Innarmu"
"Ke ban gane me kike cewa ba.
Mai lemon zaƙi na ƙofar makarantar da nake koyarwa shine dama duk tsawon wannan lokacin yake zuwa wajen Hindu? Amman Hindu baki da hankali baki san abinda yake yi miki ciwo ba ke yarinyace ƙarama shi yasa. Ina ke ina auren jahili ace mijin da kike son Aure sakandare kawai ya gama a gidannan kuma kike ganin zamu amince? Har abada wallahi babu ke babu shi ki nemi duk wanda kike so banda wannan yaron"
Shigowar su Yaya ne yasa Innarmu tayi shiru sai Yaya tace.
"Akwai abokin mijina daya nuna yana sonta sai nace mishi tana da wanda take so. To ko shi zanyi ma magana ne kawai ya turo tunda dama a shirye yake. Ma'aikacin hukumar fasa ƙwauri ne yana jibiya amman iyayenshi mazauna Kano ne"
Innarmu dajin haka ta yi na'am harma hankalinta naga ya kwanta. Nan suka fita suka barni ni da Luba na yagi takadda na rubuta saƙo na bata ta kaima abokin Gawata. Ai kuwa tana dawowa take sanar dani saƙo ya faɗa inda akeso ya faɗa domin akwai bawan Allahn da gobe sassafe zai tafi Jama'aren kuma basu da nisa tsakaninsu da Gawata.
A wannan ranar haka aka wuni ana abu ɗaya a kaina har rubutu Baba Nagoɗi daya dawo da yamma ya karɓo mun da na sha ne ma na samu salama har nayi wani irin baccin da sai da safe na farka tun shidan Yamma shima fa tashina ma akayi.
Sai suka ga na yi fari na saɓe wannan kuburin sai ya zo da rama sosai idanuna kuma suka jujjuya ya zama kamar mai harari garki wallahi. Makarai sukaita sauya mun halittata kamar almara.