← Book details Tsuron Tsirin Tsandauri Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 32 OF 77

Sashe 32

Tsuron Tsirin Tsandauri Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

Asama'u kuma duk yadda take kallon al'amura da sauƙi sai suka zame mata wani iri. Mijinyawa ya zame mata abun tsoro dan baya ko sakin fuskarshi, kallo wannan bata isheshi ba.
Gashi ta kasa faÉ—ama kowa halin da take ciki.
Ɗakinshi na ɓarayinta yake shiga ya kulle kanshi yayi baccinshi washegari ya fice sai dare yake shigowa gidan.
Asabar su Azgar suka zo suka wuni dashi amman falon Hindu ya buÉ—e musu acan suka wuni ko kallo Asama'u bata ishesu ba, itama nunawa tayi kamar bata sansu ba.
Ranar monday yana fita aiki ta kira mahaifiyarta a waya"
"Asama'u kuna lafiya ina fatan komai na tafiya daidai ko, kuma Hindu bata takura miki ba ko? "
"Mama ai Hindu ta tarwatsamun duk wani shiri da mafarkinmu Mama."
Mama daga cikin wayar tace.
"Asama'u sai kin buɗe idanunki kinyi da gaske, ai dama zama da kishiya zaman yaƙine. Ko ki yaƙeta ko ta yaƙe ki, kina ganin yadda na kafa gwamnatina a gidannan har mota ya siya mini matanshi dana zo na samu ko tayar keke basu da'ita. Babu boka ba malam kirsa da kisisina da maɗe kawai ya ishi maza, wallahi ba sai an bi bokaye za'a mallakeshi ba Kiyi amfani da hikima ki tabbatar kin mallakeshi kamar yadda na ɗauraki akai. Ai anyi mai wuyar tunda har kuka yi Aure"
"To ai Mama yaƙi kusantata sam ɗaki ma yaƙi mu haɗa ita kuma naji ƙishin_ƙishin tayi yaji bata ma gidan shekaranjiya dai yaran sunzo sun wuni wallahi Mama ko kallona basui ba"
"Danƙari ai kuwa bazan yadda ki zama bora ba wallahi. Zanyi duk yadda zanyi sai kin mallaki mijinki.
Gobe zan tawo in sha Allah ki jiraci zuwana. Ki kuma kwantar da hankalinki."
Da haka suka ƙarƙare wayar.
Washegari kuwa da yamma sakaliya Asama'u na riƙe da kaskon turaren wuta tana turara gida sai ga Mamanta ta iso ita da ƴarta da take goyo da kanta tayi tuƙin.
Su Uwatale suna ganin shigarta. Sai ga uwatale harda kularta ta abinci.
"Halima ikon Allah yau kece a gidan namu. Hindu ta raba zumunci amman yanzu yaya ta'iya É—iyarki na aure a gidan? "
"Uwatale kenan baki da dama. Hindu kam sai dai ta ganni ta barni ai tunda É—iya sukutum naba mijinyawa. Yaya gida ya yaran? ".
Uwatale na dariya tace.
"Lafiya lau sai kika ji labarin Hindu dai tayi yaji tabar gidan. Iyayenta kuma madadin su dawo da'ita sunƙi sun riƙeta harda yaran. Dama kinsan ƴan gidansu da nuna gadara, ga shegen son boko gani suke sunfi kowa"
Sun daÉ—e suna tattaunawa har saida akai kiran Magriba kafin uwatale ta koma shashenta.
Halima na sallah a falo mijinyawa ya shigo da sallamarshi harda ledarshi na kayan marmari.
"Sannu da dawowa Sikari, ga Mama tazo ganin waje"
Dai_dai Halima ta sallame sallarta.
"Mijinyawa maraba ka shigo? "
Fuska ya É—an sake yace.
"Halima kece a tafe, ya mai gidan naki? "
"Yana lafiya, nazo ban samu Hindu ba ince dai ba akan Aurennan bane ta tafi ba ko? "
"Ahh ko É—aya ba tafiya wani wajen tayi ba. Aikinta ne ya taso mata, bari in shiga daga ciki"
Ya wuce ciki yana jiyo Halima tana cewa.
"Maza bishi ki haÉ—a mishi ruwan wanka"
Murmushi kawai yayi yana zama a kan gado ta shigo ta wuce ta haÉ—a mishi ruwan wanka.
"Na haÉ—a maka ruwan wanka kaje kayi wankan"
Dariya yayi mata na takaici ya wuce banÉ—akin kamar zai mutu, ita kuma ta fita tana murnar yau har dariya yayi mata, bata san dariyar takaici bace.
A falo ta tarar da Halima tana cin abinci ita da É—iyarta ta goye.
"Kin haÉ—a mishi ruwan wankan? "
"Na haÉ—a mishi yau har dariyarshi na gani mutumin da ya dena mun dariya sam Mama"
Murmushi tayi na samun nasara.
"Akwai wasu surrukan dana kawo miki na magungunan mata ya rage naki kiyi amfani da hila ki karkato hankalinshi kanki.wallahi wallahi in ya kusanceki Hindu saita dawo mishi nama mara maggi da gishiri ba zai sake jin ɗanɗanonta ba, zaki ta baza mulkinki a cikin gidan, zaki cika gidan da yara dam mu mallake kab illahirin dukiyarshi. Magungunan matane wanda nima su na riƙa a matsayin makamina"
Magungunan duk ta miƙa mata tace taje ta adana da safe tayi mata bayanin yadda za'ayi dasu.
Mijinyawa ne ya shigo da sallama ya zauna suka sake gaggaisawa Asama'u ta kawo mishi abinci duk da tasan ba ci yake yi ba a tunaninta ko ganin idon Halima zaisa yaci. Sai yace yaci abinci a wajen aiki kayan marmari daya shigo dashi kawai zata kawo mishi ta É—ebi nasu.
Dama kullum hakan yake dawowa a ƙoshe, da safe kuma baya karyawa yake fita abunshi.
Data kawo mishi kayan marmarin sai yayi musu sallama ya koma ciki.
Halima kuwa kusan raba dare suka yi tana É—aura É—iyarta akan hanyar yadda zata kafa gwamnatinta a gidan ta ture gwamnatin Hindu.
(Akwai fa kallo a cikin wannan turka_turkar ku dai ku gyara zama ina fatan kuna gane inda muka dosa?)
Chapter 32 · 0% Book details