Sashe 51
Tsuron Tsirin Tsandauri Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read
kamar ma yasan da maganar bai ce mun komai ba har muka je muka ci tuwon muka dawo tare da kankanar da na kai aka taɓa hira mukai musu sallama muka dawo. A nanne yake bani haƙuri akan batun cin abinci umarnine na Nanno. Bagarar da zancen nayi kawai na kawo mana soyayyen nama muka ci mun kai kusan sha biyun dare muna hirar biki da abubuwan da suka faru damu. Daren shima mai tsada ya kasance muka wayi gari cikin farin ciki. Haka amarci yaci gaba da tafiya da safe muna zuwa gaida Nanno abincin dare in yau munci a ɓarayin uwatale gobe a ɓarayina za'aci haka dai har kwana bakwai ta cika. Cikin kwanaki bakwai ɗinnan wata sabuwar shaƙuwa da soyayya muka sake ginawa ni da mijinyawa bana so ko da wasa ya fita ya barni in kuwa ya dawo da rana ina manne dashi ko da yaushe bana bari mu zauna ba a manne da junanmu ba. Kuma yana taimaka mun da wanke wanke yau ma wanki yayi mana amman a banɗakinmu na ciki dugun kada a ganshi saida ya shirya ya fita tukunna na shanya kayan a katanga. Saida na gama gyara ɓarayina na yafa mayafina na nufi ɓarayin Nanno acan na tadda Uwatale gaishe da Nanno nayi ta amsa babu yabo babu fallasa tace. "Yau ke zaki yi muku girki ke da uwatale, zaki yi na kwana biyu in kika fita saita karɓa, haka zaku dingayi safe rana dare. Sannan wannan risho naki sai dai ki dinga dafa ruwan zafi amman a itace zaki yi girki kamar yadda kowa yake yi za'a aiko miki da itace da kara, sannan za'a aiko miki kayan miya. Sannan zaku dinga zuba mun abinci da mahaifiyar Uwatale da daddare kaɗai sauran mun yafe" Kunji wani salon takura da neman magana sabida in ba'a sonka dole sai an nemi hanyar da za'a bi a takuraka. To shikenan Nanno babu damuwa ɗazu ma da zai fita nake yi mishi batun itace. Dama rishon na ɗan dafa ruwane kawai. Babu damuwa shikenan wanda kike son a zuba ma abincin?" Na faɗa da murmushi a fuskata sosai. Sai tace. "Mu kenan sai kamar yau da zaki yi girkin farko zaki yi da ko wanne ɓarayi ki basu a kwano amman daga yau shikenan sai in abun ɗaukani kika yi shine zaki basu" Na ɗan zauna kaɗan kana nayi mata sallama na shiga ɓarayina ina huci dan raina ba ƙaramin ɓaci yayi ba. Naman kannan na wanke na jiƙa a ƙaramin bokiti na jawo kujera na zauna a dokin ƙofata ban bari tunani ya dameni ba na zauna ina karanta wani littafin hausa mai suna SABALULA na marubuciya Sa'adatu Saminu kankiya Ina tsaka da karatun aka turo ƙofar tawa ba ko sallama.. Su Yaya jamila ne da su Yaya Zakiya da Autar ɗakinsu. Sannunku da zuwa" "Yauwa dai sannu Amaryar binni" Murmushi kawai nayi na shiga ciki suka biyoni zama suka yi na ɗebo musu ruwa da cincin harda soyayyan nama. Gaisawa muka yi sama sama duk mukai shiru na lokaci mai tsayi sai can Yaya Jamila tace. "To Allah yayi wannan aure dai ya ɗauru sai kiyi ƙoƙarin zama da kowa lafiya ki kuma san a gidan surukai kike, sannan ba zaki ta ƙunshe kanki a ɗaki kina karance karancen litttafan da babu abinda ake koyawa sai bijirema miji ba Ga uwatale can a tsakar gida tana hira amman ke kina nan kina karatu. Kina so ki nuna cewar kinfi kowa tun kafin aje ko'ina kenan? " Bance komai ba harta gama maganganunta suka ce in basu leda zasu juye cincin ɗinsu. Miƙa musu nayi suka juye suka tafi. Na koma nayi zamana naci gaba da karatuna dan ina jin daɗin littattafan Sa'adatu saminu kankia sosai ta iya rubutu na kece raini da feƙe ƙwaƙwalwa. Ba'a jima ba sai ga yaro an turo da kayan miya da itace da kara. Shinkafa da miya naso nayi sai naga a cikin cefanan an haɗo mun harda karkashi sai nace to bari in yi tuwo da daddare. Kunji ƙaddara ta farko ko? A cikin gidan fa kowa girkinta take yi, sai waɗanda suka haɗa miji sune masu tukunya ɗaya. Amman ni sabida a ƙuntatamun an haɗa mun girkina da Uwatale, kuma wai tare ma za'a dinga cin abinci fa. Duk wannan salon takurawane da hanaka sakewa da miji. Ku dai muje zuwa shafi na gaba kuga yadda zanyi wannan tuwon ni Hindu Duwaf sai anjimanku Mrs Bukharihttps://chat.whatsapp.com/JI1IGIBFHYm64hr6IfVfqR