Sashe 10
Tsuron Tsirin Tsandauri Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ga Mijinyawa Babba a zaune shima dai karyawar yake yi. "Abba ga Ammin ta ƙaraso, Ammi tunda Abba ya farka sunanki yake ta ambata" Hmmm wasu maza sun shiga ukunsu da yaudara da munafurci. Ni dan baƙin ciki ma sai nake ji kamar in zazzagama kaina gas ko fetur. Ɗan murmushi nayi na ƙarasa bakin gadon Mijinyawa ya dubeni nima shi nake kallo ina kallon wannan bidiyo na tsaraicin a fuskarshi. Sannu mijinyawa ashe ka farka? Allah yasa kaffarane ya tashi kafaɗunka sannu kaji" "Ameen Tutar so kinga yadda Allah yayi dani ko? Na buɗe idanu ban ganki a gefena ba shine Mijinyawa Babba yake faɗamun ba'a barin mata jinya" Sai tari ya sarƙe shu ba tare da ya samu zarafin ƙarashe abinda yake son faɗi ba. "Sannu mijinyawa ka dena yawaita maganar haka akace. Hindu ƙarasa bashi shayin, mu kuma mu samu muje mu kintsa zan fita kasuwa Azgar yaronnan ko bacci bayayi duk sanda na farka zan ganshi a zaune ya tusa uban yana mai addu'a" Zama nayi a bakin gadon na amshi kofin shayin a hannun Azgar. Kaje kaima Azgar ka shirya ka tafi makaranta ƴar uwarka daga gida zata wuce. In kuma ka sameta a gidan sai ku tafi tare. Amman ga abinci kuci tukunna naga wanda kuke ci na siyarwane" Lafiyayyen abincin dana kawo su ka zuba su ka ci sukai ƙat kana sukai mana sallama. Mijinyawa kuma tsomen biredi da dingayi mishi ina bashi da cokali. Hannuna ya riƙe yana kallona. "Ya'isa Tutar so amaine yake yinƙuromun" Kafin ma ya rufe baki ya soma amai kamar zai amayar da ƴan hanjinshi. Ina tsaye ina mishi sannu, daya gama aman na zuba ruwan zafi a bokitin wanka dasu Azgar suka siyo, na surka da ruwan gora, ɗankwalina na cire dashi na goge mishi aman tas na goge mishi jikinshi da kyau, ina gamawa su Ado na shigowa. Tare dasu na fita na barshi da tambaya na isa inda majinyata suke wanke kayansu da wanke_wanke. A nan na wanke dankwalin nawa da zallan ruwa na wanke bokitin tas, ɗankwalin na shanya a igiya na dawo da bokitin na sake zama a bakin gadon, lokacin ma'aikaciyar jinya tana kanshi tana bashi baki akan ya daure yaci wani abun sabida magani da zaisha. Naga ma har an ɗagoshi bayanshi na jingine a jikin gadon. "Madam ki bashi abinci yaci zuwa anjima zan kawo mishi maganinshi, sannan za'a wanke mishi ciwukan dake jikinshi." To mungode" Iyakar abinda na iya cewa kenan. Abinci na zuba mishi a hankali yake buɗe baki ina bashi, muna cikin haka sai ga su Yaya Jamila da su Inna Duduwa ko yaushe ita Yaya Jamila tazo oho. Zuwansu yasa su Ado su kuma sukai mana sallama kowa ya tafi aikinshi. A cikin jam'u na haɗa dukka na gaishesu Yaya Jamila dai bata amsa ba, dama banyi gaisuwar dan ta amsa ba. Sai cewa tayi. "Hala a garin sunturin kai Zinariya Hindu wajen aikine ka gamu da wannan iftila'in ko? Dan nasan ta cika Zinariya sai anje an dakkota" Kuma wai har dariya take yi tana nufin bada faɗa take maganar ba tsokanace kawai. Ni dai abinci na sake saka mishi abakinshi sai da ya cinye kana yace. "Ko ɗaya ita ranar ma da motarta ta tafi aiki, na fito daga bankinmu ne zanje wani wajen abun ya faru" Da ƙyar yake magana a kuma mugun raunace. Sai kuma tayi dariya tana kallona, murmusawa nayi nima na nuna mata ai banma san nufinta ba. Yaya Saratu ce tayo ma su Inna Mairamu jagora su shida dukka matan yayye da ƙannen Baba Sojanmu kenan, duk gidanmu ɗaya dasu kuma ko wacce tana da kishiya. Sakamakon ba lokacin dubiya bane gaisheshi da jiki kawai suka yi suka ajjiye basket cike da abinci har biyu, ga leda biyu cike da lemo da ayaba. Miƙewa nayi nabi bayansu muka fito, suma su Inna Duduwa suka fito Yaya Jamila ce take wajenshi. Sannunku Inna mairamu nagode sosai jikin da sauƙi ma" Nan suka ɗan jima dai haka suka tafi, ban kai ga komawa ciki ba abokan aikina suma suka zo duba jikin nashi suma da kayansu na arziki harda kuɗi da aka haɗamun masu tsokar gaske, suna bani wannan kuɗin Yaya Jamila ta fito idanunta akan kuɗin ya sauke. "Hindu Mijinyawa na nemanki, ya daga rakiya baki dawo ba kin barshi sai faman nunfarfashi yake yi wannan wanne irin jinya kenan?" Gafa abokan aikina tana gani amman dake bagidajiyace saida ta tsinkani abunka da ƴar ƙauye. Baki ganni da baƙi bane, dubiya suka zo kinga ai bazan barsu a tsaye su kaɗai ba ko?. Kuma yanzu ba lokacin dubiya bane balle ince dasu mu shiga ciki ba? " Na mayar mata ina kallon cikin idanunta dan na tsani a tsinkani. Sai dai babu harigido ko nuna jin zafi sam a cikin muryata da kuma salon isar da saƙon. Tattaki nayi musu na rakasu duk dan in cunkusa musu haushi tunda su dangin miji ba'a iya musu da yawansu. Duk yadda zaka kai ga tautatawa ba lalle su gani ba sam. Aiko ina dawowa na tadda Yaya Jamila tana ta ruwan faɗa da zage_zage shigewata ciki dai nayi kanzil bance ba. A zaman jinyarnan na haɗiɗiyi baƙin cikin dangin Mijinyawa ƙari akan halin da nake ciki fa. Musamman Yaya Jamila da bata ƙaunar ta buɗe idanunta ta ganni tare da ɗan uwanta. Dangina wanda muke uba ɗaya, da yaran yayye da ƙannen Baba Sojanmu duk saida suka zo asibiti kuma duk wacce zata zo saita riƙo abinci ko kayan marmari ta tawo dashi, haka sukai ta nuna fariya da gasar kawo abinci kai harma da gasar kuloli dan kawai ace ai wance tana jin daɗi a gidan Aurenta. Wasu ma hannayen mazajensu suka riƙo suka tawo tare da rigi_rigin arziki. Kada kuce zaman lafiya ko zaman haɗin kai da zumunci fa akeyi ko wacce ta cikinta na cikinta da sannu zaren zai jamu har mu isa wajen. Maƙotanmu maza da mata suma haka sukaita sunturin zuwa. Sabida ina zaune da kowa lafiya, gashi suna mugun mutumtani gaya. A wannan zaman asibitin komai daya danganci kuɗi ni Hindu ake zuwa aima magana, ma'ana ni nake biyan kab kuɗin jinyar Mijinyawa ba tare da saka hannun danginshi ba sam. Su Yaya Jamila su kuma suka samu duniya wuni suke ciye_ciye a asibitinnan duk abinda aka kawo sai sunci, inma ban musu tayi ba sai ya zama rigima yadda kuka san gidan biki. Mijinyawa yana ji da ganin duk abinda yake wakana sai aka barshi da rarrashina da bani baki kamar yadda ya saba tun baya. Ni baisan ma a yanzu nafi ganin farinsu sama dashi ba, baisan dawar garin bane sabida ba ƙaramin dannewa nayi na ɓoye damuwata ba, dama ina da zurfin ciki kuma ni duk bala'i bana nuna na karaya, ba'a sanin logona kuma duk ƙwaƙwudubar mutum. Haka dai tafe_tafe har sati ya zagayo kuma jikin da kyau yana samun sauƙi. Sai Monday na koma bakin aikina na tawo na barshi dashi da danginshi da suke ganin sunfi kowa sonshi. Hankalina a zahiri a kwance babu wata damuwa mai yawa da zaka gane girman abinda ke zuchiyata, sai dai fa ina shiga office Luba tace mun. "Kin rame Hindu Duwaf duk jikin Mijinyawanne, naga idanunki sun farfaɗa." Murmushi nayi wanda ke kawar da tunanin wani abun a kaina. Zirga_zirgan asibiti ma kaɗai ya'isa yasa na rame, gashi warin asibiti yana sani tashin zuciya da ƙyar nake iya cin abinci ke kin sani. Ga miji babu lafiya Luba dole in rame" "Kuma hakane zaman jinya akwai wuya sauƙinta ma bake kike kwana ba. Wani ciwo da Sunusi yayi saida mukai wata huɗu a asibiti cur. Kinga yadda na fita hayyacina, gashi lokacin ba kuɗi bane damu nice nake ɗan aikin ma, wallahi bayan an sallamomu saida nayi jinyar jikina na zurga_zurgar da nayi ta yi ai lokacin ma kin zo gari kin same ni a wannan halin bazan mance ba" Sai muka ɗanyi shiru na fahimci tana cikin damuwa sosai gaskiya kuma ita macece mai son a tattauna, bata iya ɓoye damuwarta ta ko wacce fuska raguwar zuchiya gareta. Amman naga kamar a cikin damuwa kike, dan har a muryarki da kike karanto labarai babu irin wannan karsashin kinsan hakan koma nakasune ga aikinmu. Dole ka burne damuwarki a yayin da kake kan aikin ki musamman ku da ake jin muryoyinku" Sai kawai naga tana sharɓe hawaye wanda yazo mata babu shiri. To nasan bazai wuce Sunusi bane ya guma mata ba. Mata basu da aiki sai kuka akan maza hmm wannan fa ragon salone sosai wallahi mata. Ba Ko yaushe kuka ke zama mafita ba, ba kuma dole sai kinyi kuka kike nuna kin raunata ba, kuma ba dole sai kinyi kuka za'a tausaya miki ba. Amman naji ana cewa mace da rauni aka santa harma ana cewa wai kukan mace na karya alkadarin maza. Amman bana jin alkadarin mazan irin wannan zamanin ake nufi mazajen da da yawa yawansu basu san ma darajar matan ba balle har su tausayama zubar hawayensu ba. Ai da kukan suke cuta mana da wannan kukan suke kaimu ƙasa warwas. "Hindu kinsan ashe Sunusi aure yake nema? " Ni kaina saida na nuna mamaki. Amman wallahi kaɗan daga aikin maza. Ba gara Aure ba da abinda na kama Mijinyawa nayi ba? Na faɗa a zuchiyata a fili kuma nace. Aure Luba shine kike kuka a kanki zata zauna ne, ke da kike aikinki me zai dameki ne? " "Ba auren bane yasa ni kuka ba. Karfa ki mance gidan da muke ginawa tare dani dashi muke ginawa, wannan watan in ya saka kuɗi a ginin, wata na gaba ni zan saka. Muka koma rayuwar turawa hamsin_hamsin (50_50) haka muke rayuwarmu duk dan mu tsira da mutuncin kanmu mu tashi a gidan gandu mu huta da gori da tsangwama. Sai kawai ace yanzu tare da wata ƴar iska zan tare a gidanmu da muka gina? Shin da kaina na gina da yanzu banfi haka ba, da yanzu ban mallaki gidan nawa na kaina ba? Hindu sau nawa Zarah abokiyar aikinmu zata kawo suturu aita ɗauka da takalma ni bana ɗauka sabida adashe _adashe da nake yi sunfi uku, saida muka gama tabka gida ana shirin tarewa zai