← Book details Tsuron Tsirin Tsandauri Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 75 OF 77

Sashe 75

Tsuron Tsirin Tsandauri Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta ɓangaren mijinyawa duniya tayi mishi ɗaurin lemar minti, jinshi yake yi tamkar ɓari ba guda ba. Hindu dai dama ya kwana da sanin wani ɓangarece a rayuwarshi sosai kuma jigo. Sai yake jin rayuwar tashi da wani wawakeken giɓi wanda bazai iya cukowa ba matsawar Hindu bata ɓangarenshi gaskiya. Da zaran yayi tuntuntuni akan abubuwan da suka shiga tsakaninshi da Asama'u illahirin kunyar Allah da nauyin Hindu da taga komai sai ya lulluɓeshi, ji yake yi tamkar ƙasa ta dare ya faɗa ciki. Watan Hindu huɗu da tafiya amman yayi iyakar yinshi dan ganin ya rage tunaninta amman sai abinda ya hauhawa. Gashi ta toshe mai duk wata hanyar jinta ko labarinta. Ta ɓangaren Asama'u ta ɗauka yaƙin shine na samun zuchiyar Mijinyawa shine mafi wahala. Sai ta samu ƙoshi da kuma kwanan yinwa, gata a matsayin matarshi, amman kuma ta rasashi harma take jin ɗan da kace basui auren ba watsewar kawai suka ci gaba dayi. Gashi tayi mugun sabo ta tasirantu da abubuwan da ya shiga tsakaninsu kafin Aure. Amman a yanzu a yanzu gashi ta rasa duk da cewar Nanno tazo tace in ya sake kwana ɓarayin Hindu bata yafe mishi ba, sannan zata ɗaga mishi Nono muddin ya sake raba ɗaki da Asama'u. Da wannan dalilin ya lallaɓa ya baro ɓarayin Hindu duka ya dawo wajen Asama'u wanda a yanzu yake ganin baƙinta. Gashi dai a ɗakin amman doguwar kujerar cikin ɗakin nanne gadonshi. Sannan babu fuskar da Asama'u zata yi yinƙurin yi mishi wani abun, duk da a baya tayi yinƙuri har sau biyu a na biyun dai tayi nasarar cire mishi wandonshi ranar hankalinshi ba ƙaramin tashi yayi ba. Kamata yayi ya mammareta tare da mata gargaɗi mai zafi, sai zazzare mata idanu yake yi. "Waike wacce iriyar rashin kunya da fitsara yake damunki ne? Ni dai nasan Hindu ta baki tartibiyar tarbiyyar da Uwarki ma ba zata iya baki ba, wannan dalilinne yasa tun fil azal bamu bar amanar tarbiyyarki a hannunta ba." Ya gargasa mata maganganu kaifafan gaske. Washegarin da abin ya faru sai ga kiran Halima tana son titsiyeshi dan jin menene yayi zafi da ya zama har da duka, da kuma aibatata a gaban yarinyarta. "Me yayi zafi Mijinyawa da zaka dukan mun ƴa, kuma kana neman sunce mun zane a kasuwa. Shin ku abu baya wuce wa a wajenku ne mijinyawa? " "Baya wuce wa Halima, dalilin da yasa a cikinmu kab abokan marigayi babu wanda yayi yinƙurin aurenki, shi kanshi Abdulƙadirin kara da kiyashi ya ɗauko ɗaukan maras sani. Kuma ai kinsan babban dalilin da yasa muka karɓe Asama'u a hannunki ko? Da ace nasan riƙo Asama'u haka zai zame mun da tun farko gidan raino muka kaita taje ta rayu acan wallahi. Yanzu ke har kina da bakin kirana kina mun titsiye akan ƴar ko Halima? " Rikici ne babba ya ɓalle a tsakanin Mijinyawa da Halima, dama akwai magana a danƙare fa. Bayan sun gama wayar yayi tsaki. "Aikin banza da badan na zubar da girmana ba tayaya Halima zata kirani tana faɗa mun magana. Ita kuma yarinyar dake bata da kunya cema uwarta tayi wando ta cire mun kenan? Dan a maganganun Halima ya nuna tasan musabbabin marin harma shi yasa take tambayar nenene laifi a cikin abinda tayi ko? Hmmm Allah wadaran naka ya lalace, ashe dai da gaske barewa ba zata yi gudu ɗanta yayi rarrafe ba." Haka dai wannan zaman doya da manjan yaci gaba da tafiya. Kamar ko da yaushe da safiyar asabar yana zaune a saman Daining da laptop a gabanshi yana aiki da misalin ƙarfe sha ɗayan safe. Asama'u kuma tana Kitchen tana neman abunda zata ɗaura musu na rana sabida biredi da shayi kawai suka ci da safe. Kwatsam sai ga sallamar su Sabira har da Baba Sojanmu. Da sauri mijinyawa ya miƙe bayan sun shigo, Baba Sojanmu na sake da riga da wando na ƙananun kaya da fosinkaf ta sojoji harda zanzaro da bel ɗinshi irin na sojoji. "Sannu da zuwa Baba Sojanmu kune ashe a gidan, ni naji shigowar mota na zaci ko Mijinyawa Babbane ya fita ashe kune? " Ya ƙarasa yana shirin tsugunnawa Baba sojanmu ya katseshi tare da miƙa mishi hannu su gaisa irin na boko. Ala tilas ya miƙa hannun suka gaisa cikin fara'a, kana suka zazzauna yaranma suka gaisheshi ya amsa da kulawa yana tambayarsu karatu. "Dama cewa suka yi in rage musu hanya ni zan wuce yanzu akwai wani taron ritayat sojoji da zani ne. Inna gama zan biyo in ɗaukesu mu koma tare kamar yadda muka fito." Asama'u ce ta fito a Kitchen. Azgar ya ƙura mata idanu kamar zai halakata dan ƙiyayya Mijinyawa na kallonsu yaga sanda Asama'u ta zuba ma Azgar hararar da yaji kamar ya tashi ya zuba mata mari. "Ina kwana Baba soja, ya su Innarmu? " Muryarshi ya saisaita tare da cewa. "Lafiya lau Asama'u ya gidan ya haƙurin zama?" Ɗan murmushi tayi kanta a ƙasa. "Ta dena karatune ko ko dai ta koma ta ɗaura karatunta? Kasan fa karatu na da mahimmanci kuma Asama'u ai tana da ƙwazo" Kai mijinyawa ya sosa tare da cewa. "Bata koma ba, dake Nanno ce tace a barta a gida kawai ta zauna, ta kula da Aure" "Wat no no akanme yarinya a irin wannan shekarun ace wai ta zauna Aure, au dama aure na hana karatune? Kai ke nan ka auri mace ka jibge a gida sai an kai ruwa rana kafin a koma karatu? Ka mayar da yarinya makaranta. Nanno mai ta sani akan karatu tunda batai ba" Mijinyawa dai kanshi a ƙasa yana tuno artabunshi da Baba Sojanmu akan makarantar Hindu an yi ɗauki babu daɗi gaskiya. Baba soja ya fita Mijinyawa ya bi bayanshi aka bar Asama'u da su Azgar. "Wallahi in sha Allah sai alkadarinki Ya karye Asama'u ashe da Abba kuke wannan wayar da kuke yi kullum a gabana? In kina tunanin kinyi domin ki ƙuntatama Amminmu ne wallahi Allah bazai baki iko ba. Ammi tayi miki nisan da iyakar rayuwarki baki isa kin kamota ba" "A matsayi na duniya ba, bana fata in zama mai cuɗanya a cikin maza. Amman a matsayi a zuchiyar mijinyawa sai dai ta biyo bayana. Abinda muka aikata ai ba haramun bane kuma in kukai mun haka ba kui mun adalci ba, sabida babu wanda yake a haƙƙu ya aureni sama da mijinyawa ai" "Wallahi ƙarya kike. Ammi ta riga ta rufe ƙofar zuchiyar Abbanmu babu wata macen duniya da zata iya buɗe zuchiyarshi. Ai da ganin zaman babu daɗi kuma ba zaki samu nitsuwarshi ba har sai farin cikinshi ta dawo gidan. Bar miƙe ƙafa yarinya Ammi tananan dawowa da zaran ta gama abinda take yi a landan zata dawo ɗakin aurenta, kinyi tsararo ki raba wannan ƙaunar da Allah ne ya ƙulla. Sabida baki da daraja da Mijinyawa kike kiran Abba" Azgar bai saka baki ba, kuma bai hana Sabira amayar da gubar da Asama'u ta shayar dasu ba, sabida ita macece rauni gareta. Amman ya fita jin zafi da ɗacin abinda ya faru, kuma a idanunshi yana tuno wasu kallon_ kallo daya wanzu tsakankanin Asama'u da Abbansu wanda sai da abinda zai faru ya faru ya iya fassara kallon. Ji yake kamar ya shaƙe Asama'u, ba dan biyayyar iyaye ba mai ma zai kawo shi wajen Abban kanshi. Miƙewa Asama'u tayi taja tsaki tare da cewa. "Aikin banza aikin wofi kada ki sake zuwa har ɗakina kice zaki faɗamun magana ina matar ubanki" Ai wannan kalmar ta MATAR UBA ita ta tunzura Sabira, tana miƙewa ta dira a wuyan Asama'u dambe sosai ya kaure a tsakankaninsu. Uwatale ce ta ƙaraso a guje tana shigowa mijinyawa na shigowa. Damben yaƙi rabuwa a tsakaninsu Uwatalate ta kasa rabawa Sabira ta ɗafe Asama'u sosai. "Jeki abinki uwatale ki rabu dasu" Ya faɗa yana kallon yadda Asama'u take naushin bakin Sabira, ita kuma Sabira ta riƙe wuyanta tamau idanunta sun firfito. "A barsu mijinyawa a dai rabasu. Ga babban banza a zaune ya kasa rabasu, sai kallonsu kawai yake yi. Duk ba ƙannenshi bane" Ta nuna Azgar dake kallonsu. "Naga matar Aure ce kinga ai bazan iya taɓata ba shi yasa" Azgar ya kashe bakin Uwatale, mijinyawa kuma yana ta kallon yaron yayi tsam yana nazari. Tim suka ji Sabira ta kayar da Asama'u ta hayeta da sauri Uwatale ta ƙarasa mijinyawa yace. "Uwatale nace ki barsu ki fita dan Allah kar kiga ɓacin raina" Tsawar daya daka ita ta tsayar da damben, uwatale tayi saurin fita Sabira ta jeru da ɗan uwanta daya miƙe tsaye. Asama'u ta miƙe tana kukan makircin ƙafarta ta goce. Hannaye ya goya a baya yana ta kallonsu Sabira ƙirjinta nata hawa da sauka, Asama'u nata kuka fuskarta duk yakushi kaca_kaca. Bai tuno irin wannan zai iya faruwa ba, iyakar son zuchiyoyinsu ya hanga. Baiyi nazari kan mutanen da abun zai taɓa ba, bai tuna zai iya cusa ma yaranshi tsanarshi ba. "Yayi kyau Asama'u kinji yayi kyau. Azgar kuzo mu fita" Ciki ya shige da saurinshi. Azgar ya kamo Sabira suna shirin fita Asama'u tace. "Sabida waɗannan ƴan iskan yaran kake mun faɗa, yarinya ta dakeni kuma kazo kana ce mun yayi kyau... " Tau Azgar ya ɗauketa da mari daidai fitowar Mijinyawa da sauri, sarai yaji abinda ta faɗa abinda ya fito dashi ma kenan. "Ƙara mata a ɗayan kuncin" Mijinyawa ya ba Azgar Umarni. Tau ya kuma ɗauketa da mari a ɗayan kuncin nata. Hannun ƴar uwarshi ya riƙe jikinshi na rawa suka fita. Asama'u ta bi Mijinyawa ciki ta sameshi yana sake riga harya sake wando. Bata iya ce mishi uffan ba, haka zalika shima. Kuka take risga kamar zata mutu. Kin mota ya zara ya fice. Suna tafe da su Azgar a mota ya rasa me zaice dasu har suka ƙarasa kantin da suka saba siyayya suka shiga. Azgar na biye dashi a baya da basket ba ƙaramar siyayya yayi musu ba, ya shiga gari dasu sukaita zagaye, tunani kawai yake tatayi ta yadda zai bama yaranshi haƙuri dan so yake abun yazo ƙarshe a gama. Hotel ya wuce dasu kawai ya kama ɗaki suka shiga. Ciki da falo ya kama musu, yana zaune a kujera su suna zaune a gabanshi a saman kafet. Azgar
Chapter 75 · 0% Book details