← Book details Tsuron Tsirin Tsandauri Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 61 OF 77

Sashe 61

Tsuron Tsirin Tsandauri Part 1 Complete Hausa Novel · about 9 min read

Hindu:.
Ji nayi ruwa ya sauka akan fuskata da sauri na miƙe zaune idanuna naji suna mun wani irin yaji da raɗaɗi kawai.
"Sannu yarinya ya kike jin jikin naki? "
Mai magani ta tambayeni da jajayen idanunta.
Kasa magana nayi, sai tayi dariya ta dubi mijinyawa tace.
"Sun riƙe mata bakin basa so tayi magana dani. Fishi suke yi dan nace su baku iska. Kada ku damu da kun bar wajennan bakinta zai buɗe. Kuma sun haƙura"
Mijinyawa yace.
"Mungode sosai nawa zamu bayar kuÉ—in sadaka to? "
"Ai bama faÉ—a abinda Allah ya tsaga rabonmu ne shi muke samu ka ajjiye kawai ku tafi"
Hannu ya saka a ajjihu ya É—ebo dubu huÉ—u ya ajjiye mata, shi da Innarmu suka kamani muka fito.
"Kai da ita sai ku hau Acaɓa ka riƙeta da kyau"
Cewar Innarmu, ita ta taimaka mun na hau mijinyawa ya hau bayana, ita da Abdul Ƙadiri kowa ya hau nashi muka tawo.
Wani sanyi ne yaketa ratsani jikina har kakkarwa yake yi. Ƙam mijinyawa ya riƙeni yanata mun karatu a kunnena can sai na sauke ajjiyar zuchiya na dena jin wannan sanyin.
"Sannu Tutar so Allah ya inganta lafiya"
Ameen'
Kawai nace dashi nayi shiru ina sauraren zuchiyata.
Sai bayan la'asar muka shiga gida, fuskata tun a hanya naji ta sawai ta saɓe ban gasgata hakan ba saida na fito wanka na tsaya a bakin mudubi sai na ga na rame sosai fuskata kamar ta ƴar mage.
Magriba na dosowa Innarmu da kanta ta bunke ɗakina da hayaƙi ta zagaya lungu da saƙo.
Muna yin isha tasa nayi wankan magani Alhamdullillahi yau kam nayi bacci harda makara nayi saida Innarmu ta tasheni kana nayi sallah muka gaggaisa.
"To mu kam anjima kaÉ—an zamu É—auki haramar komawa inda muka fi wayau.
Kada kiyi wasa da magungunanki Hindu ki dinga yin hayaƙin kuma ki dinga yin wankan kinji ko Allah zai baki lafiya. Kuma kar ki saka damuwa a ranki dan kawai kinyi wata takwas baki samu rabo ba, baki ma ƙarasa takwas ba wata bakwai ne kamar da kwana goma sha uku, kowa da lokacinshi masu goranta miki in sunyi zuchiya su baki mana tunda a gidansu ana bada ɗan mutum kyauta. Ki maida hankali akan abinda ke gabanki. Yaya batun komawarki karatu da mijinki yayi alƙawari? Ai yanzune ya dace ya sakaki ki kammala digiri ɗinki kafin ku soma tara yara ko, ko kuwa ya janye alƙawarinnen sai musan me zamu ce da Baba sojanku dan wallahi akan karatunki kinsan Aurennan zai mutu ko?
Bazai yiwu ba wallahi Allah kinji na rantse miki. Sai dai muji da ɗaya kasancewarki a ƙauye amman dole kiyi ilimi ba zaki haɗa biyu ba ga ƙauyanci ga jahilci ba. Ni naji daɗi ma da baki yi ciki da wuri ba. Nifa bana jin akwai ranar da zan so Aurennan naki. Ga Saratu harta samu aiki ta soma ɗaukar albashinta mai tsoka. Ku bani amsar abinda zanje ince ma Baba Sojanku saƙon daya bani in kawo shine yaushe za'a soma karatunne."
Mijinyawane ya shigo da sallamarshi yazo duba Innah a kuma gaisa ya tarar tana maganar karatu. Bayan sun gaisa tace.
"Gara daka shigo dama inason ganinka akan maganganu da yawan gaske.
Na farko yana da kyau danginka su sani cewar Hindu ba juya bace tunda ba dole bane saita haihu a cikin shekara guda da aure ba, ni sanda akaimun aure saida na shekara uku kafin Allah ya bani rabo. Ikon Allah ban taɓa ji daidai da rana ɗaya an kirani da juya ba, sai Hindu wata takwas kawai, anan garin bata da gatan kowa sai kai yana da kyau ka tsaya mata ka tsawatar ma danginta su guji kiranta juya a gabanka.
Kaji abinda mai magani tace, suma makaran kaji abinda yake kawosu, domin samun nutsuwarku da lafiyarta sai ka gargaÉ—esu.
Sannan batu na biyu menene dalilin da yasa abincin cikinku ku biyu ba zaka dinga siyo ma Hindu kalanzir tana aiki a risho ba saita kunna itace abincinku kuku biyu? "
A hankali mijinyawa yace.
"Kiyi haƙura Innah in sha Allah zamu tattauna da masu ruwa da tsaki a gidan babu mai sake kiranta da wannan sunan.
Dangane da batun aikin girki a murhu umarnin mahaifiyata ne muka bi tace bata yadda ita Hindu ta dinga aiki da risho ita kaÉ—ai a gidan ba, sai dai tayi a murhu kamar kowa shine kawai dalilin."
"To batun komawarta karatu daka ɗauki alƙawarin zata ci gaba da karatunta in ka aureta fa, shi wannan mahaifiyar taka zata amince dashi kuwa, kasan fa akan karatunnan wallahi sai dai aurennan ya mutu, zamu iya yadda da komai amman banda zama babu ilimi kuma ba ilimin da mace zata yishi ace ta zauna ƴaƴanta ne kaɗai zasu amfana ba, a'a ilimin da zata fita ta bayar dashi al'umma su ƙaru da'ita tayi aiki kamar ni, kamar ƴan uwanta. Kasan yana cikin sharaɗin aurenku ai. Kai Magawata yaushe zata koma bakin karatunta? "
"Ban manta da alƙawarin ba. In sha Allah zata koma makaranta nayi wannan alƙawarin bazan saɓaba. Ina jiran sana'ar da nake yi ta tsaya da ƙafafunta ne tukunna, sannan ita kanta ta samu lafiya"
"To zuwa yaushe kenan dan in sanar ma mahaifinta ko ba gaskiya ba? Dan ina ganin yanzune ya dace a ɗebe mata kewar raɗaɗin zaman ƙauyennan da karatun ko? Kuma kaga ai gara ta soma tun kafin ta shiga laulayi ko, in kuɗinne babu sai na tallafa maka na ɗauki nauyin karatun mu dai fatanmu shine a samu ilimin yara su dogara da kawunansu."
Shiru yayi har a fuskarshi ya nuna rashin jin daÉ—inshi, nima naji wani irin kunya gaskiya.
"Kiyi haƙuri zata yi karatu in lokaci yayi kuma in sha Allah ni zan ɗauki nauyin karatunta harta kammala, kuma zata yi aiki kamar yadda kuka buƙata in sha Allah nima zanyi alfahari da hakan"
Innarmu tace.
"Amman... "
Yaya Saratu ce ta katseta ta hanyar cewa.
"A bashi lokaci kamar yadda yace tunda yace zai ɗauki nauyin karatun kamar yadda dama haka sharaɗin yake. Kuma ya nuna baya buƙatar tallafinki akan karatun ai shikenan Innarmu"
Ajjiyar zuchiya ta ja tare da saukewa tace.
"Shikenan mun baka lokaci lokacin shi zai mana alƙalanci. Amman yana da kyau ko koyarwa a firamare ka nema mata ga makarantun gwamnati nan a garin naku da zaman banzan da take yi, ko nawa ne albashin a ƙalla zata samu, sannan ko babu komai fitar zata rage mata damuwar cikin gidan, ko babu albashi gara ta dinga yi, a ƙalla karatun ba zai bar kanta ba"
"To shikenan zan nema mata wannan baida matsala, akwai wanda na sani in sha Allah zan mishi magana zai sama mata gurbin koyarwar"
"To madallah mu zamu wuce akwai biki nan da wata biyu da sati biyu na yayunta maza munaso ka barta tazo, sannan akwai bikin ɗiyar ƙanwata a Maiduguri shima zamu je tare da'ita in an gama bikin gida da sati guda, muna saka idanun ganin ka barta tazo"
Kai ya sosa yace.
"In sha Allah zata zo Allah ya nuna mana lokacin rai da lafiya mungode sosai Innarmu da wannan ziyarar"
Tare dashi muka ɗunguma muka raka su Innarmu har gaban motar Akarami da yaƙi shigowa sai yaro ya aiko wai su fito su tafi.
Ɓarayin Nanno muka leƙa suka yi sallama babu yabo babu fallasa.
Saida motarsu ta ɓace ma ganinmu kafin ya rakoni muka shigo gidan a tsakar gida muka zauna na kawo mishi kayan karyawa, kana na jibge mishi tsarabar da suka kawo komai da komai harda kuɗin ɓatarwa da Baba Sojanmu ya aiko mun dasu, na miƙa mishi ƙyallen ankon gidanmu duka dai.
Yana cin doya yana korawa da shayi yace.
"Gaskiya sun yo tsaraba da yawa, wannan doyar da suka kawo akwai gari gata da haske, mungode sosai ga wake ma mun samu"
Ina dariya nace.
"Kuma kaga kayan abincinmu shinkafa kaÉ—ai ta rage itama bata fi kwana biyar ba. Bari in samo ledoji in zuzzubama matan gida tasu tsarabar. "
Hannuna ya riƙe yace.
"Baki karyaba kizo muci Tutar so, naga jikinki da sauƙi sosai"
Sai naji ƙaunarshi ta sake yin lub a ruhina nayi murmushi nace.
Naci tare da su Yaya Saratu wannan ai du naka ne kaci ina zuwa"
Ciki na shiga na ɗebo ledoji na zuzzuba waken diyar na samu wuƙa na yanka na sakama kowa
Su Nanno ma na cire musu nasu, na cire ma Baraka nata dan tayi hidima dasu Innah sosai da kaina na mimmiƙama kowa na Baraka na ba yara suka miƙa mata. Da kwana ukun wake, doya huɗu muka tsira. Turaren wuta dama ban samma kowa ba adana abuna nayi a durowar turarukana.
Saida na kammala na zauna kusa da mijinyawa muna fuskantar juna nace.
Kayi haƙuri da duk maganganun Innarmu nima ba sui mun daɗi ba balle kai"
"Ko kusa, ai kamar yadda Nanno take yaɓo mana ni dake mu shanye, itama Innarmu dole mu shanye nata, in kikai la'akari dukkansu da hujjojinsu salone nasu na nuna soyayyarsu garemu. In sha Allah zaki zama abinda kike son zama da gumin halak ɗina zan biya miki karatu.
Kuma zan nema miki gurbin koyarwa a makaranta kamar yadda Innarmu ta buƙata gobe_gobennan kuwa zan shiga in samu hedimasta muyi magana da takaddunki ma zan tafi in sha Allah zaki samu koyarwan in dai hakan zai baki farin ciki.
Masu miki wannan gorin kar ma ki sake kulawa ke ba juya bace zaki haihu har ma sai kince da kanki kin gaji. Kuma in so samu ne yara nawa zaki haifo mun ne?"
Ina dariya nace.
Bakwai ma ai sun isa ko?"
Shima dariyar yayi mun yace.
"Baki da burin tarawa ma sai nuna damuwar kawai dai".
Mun jima muna hirarmu cikin farin ciki da annashuwa. Daga bisani yace yana son zai yi ƙaikula, ya shige daga ciki ya kwanta ni kuma na shiga aikace_aikacen gida inayi ina girkina na rana faten wake da doya nayi mana munci shinkafa munci dama har mun gaji.
Washegari kuwa da yamma Mijnyawa yaxo mun da albishir na samu gurbin koyarwa a makarantar yara ta firamare jama'are sentaral makarantar firamare da sakandare ta gwamnati duk wata ina da albashin nera dubu huÉ—u ta wancan lokacin.
Nayi murna sosai nayi farin ciki, duk da an sha daga da Nanno amman daga ƙarke ta amince dan nayi rantsuwa da Rabbil ka'aba akan dole in koyar tunda har naci sa'a suka ɗaukeni, akan wanne dalilin za'a hananu.
An sha artabu dani sosai, banyi da wasa ba sam, nasan muddin nayi sake kuma na amince na zauna. To wallahi batun karatuna ma babu ina ji ina gani zata zaune mun.
Kunji yadda al'amura suke ta cukumurÉ—ewa ko? Ku dai ku ci gaba da biyo Duwaf É—inku.
Mrs BukhariTSURON TSIRIN...
TSANDAURI...
Chapter 61 · 0% Book details