Sashe 60
Tsuron Tsirin Tsandauri Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read
Mijinyawa:.
"Ku shigo da'ita ai dole su zubar da'ita wannan fadar bata wasa bace. Ku matso da'ita kusa dani"
Cewar mai magani tana yi tana murmushi ga haƙoran makka a bakinta kusan shida, ga zobuna da awarwaro marasa iyaka, sarƙoƙi a wuyanta babu dama ne, ita kanta tayi zubin aljanu kuma da kun haɗa idanu gabanka zai tsinke ya faɗi.
Tattago Hindu suka yi zuwa gabanta ta shiga yarfa mata ruwan magani nan take Hindu ta soma kakari tana sambatun cewar ko kashesu za'ayi ba zasu fita a jikinta ba, kuma in ba'a dena mata gorin haihuwa ba ba zasu dena zuwa ba. Su asalinsu makaraine na gadon gadon gidansu Innah suna tare da kaf zuriyarsu ko ita Innah suna tare da'ita su ba masu cutarwa bane ayi sulhu dasu kawai in kuma anason zaman lafiya kada a sake kiran goÉ—iyarsu da juya" Da wata iriyar murya mai sauti biyu suke magana da kuma wani irin amo mai tsoratarwa.
"Au juya suke kiranta wata bakwai da ɗan wani ɗoriya kacal da aure dan bata samu ciki ba? Allah mai iko, ƙauye kenan"
Cewar Innah kenan tana girgiza kanta.
Mai maganin tace.
"Amman ai kuna cutar da'ita dayawa me yasa kuke son kashe mata Aurenta ku barta hakanan ta huta tunda ku mallakin zuriyar gyatumartane mana kuyi alƙawarin barinta ta huta ko in haɗaku da babbanku"
Makaran suka ce su babu inda zasu matsa suna tare da Hindu kullum kuma basu ga wanda zai iya matsar dasu ba"
"Ashe ba sonta kuke yi ba kenan kunce ku ba masu cutarwa bane amman kun hanata ita da mijinta samun farin cikin dare, sannan ziyarar da kuke zuwa mata cikin dare zai iya hanata samun rabon da akeyi mata gorin akai ai. Ku matsa ku bata waje kuyi haƙuri na roƙeku ku barsu su mori gajiyar aurensu"
Da haka dai ta shawo kansu suka ce zasu dena bigeta in aka dena mata gori amman duk sanda akace mata juya tabbas zasu zo kusa su kuma. Kuma sun kusa soma juyar da bakin duk wanda ya sake cewa da Hindu juya"
Hayaƙi ta zuba a cikin kaskon dake gabanta ɗakin ya turniƙe da hayaƙi mai tuƙuƙi mai maganin tace da Innah.
"Kiyi haƙuri na kanki ba zasu motsa ba, naki dattijaine basa tashi miki tunda kika tsallake abubuwa da yawa ba zasu tashi miki a yanzu da girma ya hauki ba. Amman sabida ke suke bibiyar yaranki dukkansu suna tafe da abinsu ita nata ne suke da tsauri shiyasa suke tashi mata. Su kuma kalar tasu nuna ƙaunar kenan. A zuriyarku akwai masu hawa makarai kamar inda ita wannan take yi?
"Eh akwai hatta gyatumarmu itama tayi ciwon makarai sosai. Akwai ƙanwarmu da suka hanata zaman auren saida tayi aure shida ana bakwanne ta dace da magani, mai maganin ma dai ta aura dashi suka ci gaba da rayuwa, amman bata taɓa samun haihuwa ba, ko ɓatan wata gaskiya bata taɓa yi ba Sai ɗaiɗaiku a cikin yaran ƴan uwa."
"Gadon gidankune ta ɓangaren mahaifiyarku, sai dai ba masu cutarwa bane kuma musulmaine ba kafirai ba, ta dage da magani sannan a guji ce mata juya sabida dugun abinda kaje kazo ita ba juya bace tana da ƙwanta na haihuwa, kuma zata haihu lokacine bai yi ba.
Kai kuma ga wannan hayaƙin duk magriba da zaran almuru yayi a turare ɗakinta dashi, sannan wannan ruwan maganin a dunga sirka mata ta dunga wanka dashi a bawo, kada ta goge jikinta in tayi wankan ta barshi ya bushe a jikinta, zasu barta ta huta. Sai a kiyaye a dena aibantata ana kiranta da suna juya kasan makarai suna da naci da rashin yafiya, kuma sukan taya wanda suke karewa faɗa kota wanne siga, amman ba masu cutarwa bane, kada ace za'a rabata dasu bisa dole zasu iya cutar da'ita da duk makusancinta a wannan gaɓar. Sannan in aka kaisu bango zasu soma hana duk wanda zai kira musu goɗiya da juya sukuni, kaji da kunnnenka me suka ce zasu soma yi ai? "
Hayaƙi da na wankan ta miƙa mishi ta ɗebi ruwa a tafin hannunta ta yayyafama Hindu"