← Book details Tsuron Tsirin Tsandauri Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 57 OF 77

Sashe 57

Tsuron Tsirin Tsandauri Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da sauri na miƙe ina ambaton Allah. Ji nake yi kaina kamar ana mun yawo dashi a sararin samaniya, ga wani kururuwa da nake ji a kaina. Shiru nayi idanuna a runtse inaji yadda Nanno take fama da mijinyawa, sai bambami take yi. "Kiyi haƙuri Nanno bai kamata in fita in bar Hindu a wannan halin ba amanarta a hannuna take, ki yi haƙuri dan girman Allah na roƙeki. Dan Allah kiyi haƙuri zanje in dubo Yaya jamila a darennan amman inason sanin halin da Hindu take ciki, kinga bamu samu zama da'ita ba" Sai ganina nayi a cikin ɗakin cikin dakiya da nuna rashin kulawa da abinda ya faru nace. Babu abinda ya sameni kaje ka dubo ƴar uwarka baka da kamarsu a rayuwarka, ni zaka iya rabuwa dani, ita kuma har abada taka ce" Zama nayi a kan gado, na jawo tiran abincin gabana, jikina tamkar zai tsattsage jini ya fatso ya fito, sabida ciwo. Nanno ta tusashi gaba suka fita, da murmushin baƙin ciki da takaici na bisu kawai. Ni Nanno mamaki take bani, bama ita kaɗai ba harda ire_iren surukai irin Nanno. Da ƙannen miji, da yayun miji masu ƙara tura rigima, su kuma so suke a so su, a ƙaunace su a nasu dangin mijin fa. Amman kai in ɗan uwansu zai nuna darajarka, sai dai in asiri kayi mishi kawai hakan zai iya faruwa. Son kai irinna mata abun azimun. Ashe bayan samun damar rayuwa da zaɓinka akwai ƙalubale masu yawa zagaye da Auren? Ni da nayi tunanin duk damuwar duniya ta gushe mun matsawar na samu mijinyawa a matsayin abokin rayuwa, ashe tsugunne bata ƙare ba. Yanzune zan soma ganin rayuwa. Wata shida kaɗai an soma gorinta mun haihuwa. Murmushi na kuma yi kalmar juya na yi mun yawo a jinina yana tuƙamun a ƙirjina. Shayin na soma sha dan yinwa kamar zata halakani jikina babu kuzari sam. Taliyar kaɗan naci naje Kitchen na rufe na ɓalli ƙwayar bature guda biyu na watsa. Saida nayi sallar isha na shafa humra na saka kayan bacci na kwanta. Ban wani jima da kwanciya ba mijinyawa ya shigo babu daɗi sam a fuskarshi idanunshi sun kaɗa sun zama jawur ƙirjinshi sai hawa da sauka yake yi. Hayowa gadon yayi ya jawoni nayi lamo a ƙirjinshi sai lumshe idanuna nake yi. Shi kuma ƙirjinshi nata dokawa. Mun jima a haka sai shafar bayana yake yi yana sake shigar dani jikinshi kamar irin za'a ɓanɓareninan haka yakeyi. A hankali cikin wata murya mai zurfi da kauri ta cikar mazantaka yace dani. "Zan iya fito na fito da duk wanda ya nuna miki ƙiyayya ko ya nuna baya ra'ayinki. Bazan zuba ma Yaya Jamila idanu tana aibanta mun ke ba tana kuma sake zuga Nanno a kanki ba. Wallahi Tutar so Nanno kaɗai zan iya ɗaga ma ƙafa a kanki, banda ita bazan iya ɗaga ma kowa ƙafa ba." Kaina na ɗago na dubeshi ƙur sai can nayi murmushi kaɗan nace. Yaya akayi kuma, ta sake tayar maka da zancanne ko ko dai ita ta tayar da zancan da kaje dubo ta? Kada ma ka ɗaga hankalinka in dai Yaya Jamila ce ta daɗe tana faɗamun maganganu na wannan karonne suka dakeni irin dukan da abadan bazan warke ba matsawar zan buɗe idanuna in ganta. Babban abinda yafi komai zama zunubi a wajena shine a tsinkani a cikin mutane, ballentana ita tasakani a halin da bansan ya kaina yake ba, na bayyana tsaraicina, ko ban bayyana ba duk ban sani ba, ga gidan dam da taron mata" Ajjiyar zuchiya na ja na sauke. "Kiyi haƙuri ina tare dake kuma zan tsaya miki sai iyakar inda ƙarfina ya ƙare. Mu zuba dani dasu Yaya Jamilan tunda haka ta zaɓa. Mijinta dake shanyayyene shima har yana cemun ya kamata in ɗauki mataki a kanki in da makarai da iskanci ya zaki shaƙe yar miji kiji fa. Itama Yaya Shafa sai sake zuga Nanno take yi dake duk bakinsu ɗaya Yaya Salihun mijin ita Yaya Shafan shima mun haɗu masallaci yake cewa tun wuri in ɗauki mataki a kanki in ba haka ba watarana Nanno zaki shaƙe kiji mun wannan magana fa sai yayata magana akeyi. Ita kam Yaya jamila bamu rabu da arziki ba nasan gobe sassafe zaki ganta ta tawo gida tazo haɗin faɗa. Duk da wuyan nata ya aune. Naje na samu mijinta ma yana shafa mata man Ayu kinsan yana maganin kumburi" Shiru nayi sai can nace. Wata shida da aure baiyi wuri ace har an soma kirana da juya ba, kenan in ni juyar ce danginka ba zasu iya karɓata ba kenan mijinyawa? Nifa a duk halin dana tsinci kaina ina godiya kana ina son kaina a hakan. Duk rintsin da zan shiga ni Hindu inason kaina, kuma ina godiya ga Allah, rashin haihuwa ai ba gazawa bace shirin Allah ne." "A duk yadda kike inma mai haihuwa inma mara haihuwa ni dake har abada, muna tare babu gudu babu ja da baya. A duk tsawon zamani zanyi alfahari dake ƴar matata. Wallahi ko ki haihu ko ki kasance juya Hindu ni Mijunyawa ina tare dake abadan" Da dadaɗan kalaman yabon halayena da zatina ya mantar dani damuwa, amman sunan juya yaƙi ya kwanta mun sai ma maimaita kanshi da yake yi. Washegari kamar yadda aka saba ina idar da sallah na koma na kwanta jikina sai ciwo yake yi. Cikin bacci nake jiyo tashin murya a falo babu shiri na duro a gado na leƙo. Yaya jamila ce a zaune akan kujera ta tusa Mijinyawa a gaba tana mai sababin faɗa ga Mijinyawa Babba daga bakin ƙofa shi da gambo suna bata haƙuri. Wuyanta ya aune gaya Mijinyawa kuwa yana zaune a ƙasa ko ɗagowa bayayi. "Ya dace kenan ita fa sanda na leƙa tana gado tana bacci, shi kuma yanata faman yi mata soye_soyen doya sabida rashin kunya da rashin mutumci. Ɗan uwanka haka kaga yana yi ma matarshi ita da take da ciki ma, me zai aikeshi shiga madafi sai dai in ciwo yayi tsanani a nemo ƙannenta su zo su zauna da'ita ai" Mijinyawa Babba yace. "Yaya Jamila a dai taru ayi haƙuri kai kuma kada ka sake gaskiya. Ai gara ma ka shiga cikin gida ka nemo mata abinci. Ga uwatale canma tana suyar ƙosai har daku nace mata tayi. Me zai kai ka madafi in ba neman sababi ba, dole sai ka kiyaye, madafi ai sai mata. Gaskiya banda ciwon da zai sa in shiga in ma mace girki a madafi ba. Yaya Jamila ke kuma kiyi haƙuri hakanan muje Nanno tana nemanmu har da kai da Hindu tace duk muje, Yaya Zakiya da Yaya Adamu, da Yaya Salihu ma duk suna ciki da iyalansu." Miƙewa Yaya Jamila tayi ta fice, idanu na zuba ma mijinyawa muka sakarma juna murmushi kawai. "Taso muje kinji inzo in ƙarashe miki girkinki. Kinji ƙauyanci wai mijinyawa Babba ina shi ina shiga Kitchen ko? Ƙauyancine yake ɗawainiya dashi. A littattafan Hausa dana kakkaranta maza na yin fiye da hakan" Ni dai babu ruwana kar kasa Nanno ta leƙo ta ganka" Jawoni yayi ya matse gam a ƙirjinshi muka sauke ajjiyar zuchiya yai ƙasa da muryarshi raɗa_ raɗa yace. "Kada ki damu da kowa da komai. Duk abinda za'a tattauna kar ki bari yayi miki tasiri ni ɗinne dai mijinki mai riƙe da igiyoyin Aurenki uku wanda akaima ƙullin da babu kuncewa ko a Aljanna kece shugabar matana nacan" Idanu na ɗago nace. Anan duniya ma nice shugaban matanka? " Hancina ya lakace dan bai isa ya gane da wacce siga nayi mishi tambayar ba, fuskata ba zata iya fassara mishi manufataba. "A nan duniya ke kaɗai kike mulkin birnin zuchiyata yanzu dai ba wannan ba muje mu dawo in baki labari mai daɗi" Tare muka fito muna murmushi madadin aganmu cikin damuwa sai ga akasin hakan. Wannan abu na dafa dangin Mijinyawa sosai haka sanda nake gida wannan halin nawa na shanye damuwa inyi murmushi a madadin ɗaure rai yana damu ƴan uwana wanda muke ƴan uba da waɗanda muke ƴaƴan wa da ƙani kuwa, kirana suke munafuka miskila wacce ba'a iya gane me tafi so ko menene bata so. Da sallamata raɗau na shiga ɗakin ina biye da mijinyawa. Waje muka samu a ƙasa muka gurfana kamar yadda sauran suka yi. Nanno kaɗai na gaisar daban amman sauran duk kuɗin goro nayi musu. Sun amsa basu amsa ba, banyi da nufin dole sai sun amsa ba. Taro aka haɗa mana. "Abinda yasa na taraku anan akan maganar wannan makirar yarinyar da take yinƙurin farraƙa zumuncin ɗakinnan tasa kishiyoyi da yaransu sai zunɗena suke yi. Gari ya ɗauka anata yamaɗiɗin matar mijinyawa ta shaƙe wannan yarinyar da ƙyar aka ƙwaceta. Yau kuma gashi an ganshi yana girki a madafi. Kuma naji a majiya mai ƙarfi har wanke_wanke da wanki du yana mata, ya wanke mata tsakar gida ta maisheshi lusari dai". Sai kawai ta fashe da kuka ƙaƙas fa wallahi abun dariya, abun baƙin ciki. Iko sai mai yi mana iska harda ruwa kuma a lokaci guda, menene abun kuka a wannan lamarin in ba dai so ake a nuna mun iyakata ba. Matan suka shiga bata haƙuri ni da Mijinyawa babu wanda ya tanka sai ido kawai illahirin mamaki. "Ki yi haƙuri Nanno tunda muka je kai lefe muka ga irin tarbar da uwar Hindu tayi mana nasan akwai matsala, kawune yayi ruwa yayi tsaki shiyasa bamu da yadda muka iya. Amman fa dan shanyewa wallahi ta gama shanye mijinyawa dama Kanuri haka suke jan mazajensu a ƙasa, an tabbatar mana uwarta ma sai abinda tace ma tsoho" "Bana son sake ganinka a Kitchen ko yima wannan juyar hidima. Wanka gashi matarshi a cikin laulayi take amman ita take yin komai na gidanta, amman dake ita ƴar gwal ce shafaffa da mai sabida tayi makarai na ƙarya shine ta shinfiɗe kake mata girki, ga rashin mutunci da kaje har gida kaima yarka duk akan wannan abar ko? Kai wannan yaron ku shaida wallahi akan Hindu zan iya sallama Mijinyawa domin yadda yake nuna fifiko akan matarshi abun yayi yawa. Nan ko tsaraba ya kawo na karɓa na raba sai ya nuna rashin jin daɗinshi da hakan yafi so ita a bata ta raba, duk
Chapter 57 · 0% Book details