Sashe 33
Tsuron Tsirin Tsandauri Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
LANDAN:.
Mun sauka a Landan cikin aminci da kwanciyar hankali.
Mota aka turo ta É—aukemu zuwa masaukin da Bbc ta tanadar domin ma'aikatanta
Gaskiya Bbc É—ayace tamkar da dubu kuma gagara gasar masu gasa.
Gidane mai kyau da tsari ko wanne ciki da falo ne, akwai kaya da duk wani abun buƙata na rayuwa a ɗakin dangin su gado, kujera, kayan kallo, kayan Kitchen da dai abubuwan amfani yau da kullum.
ÆŠakina yana jere dana Shamsiyya.
Ki nasa na buɗe na shiga ajjiyar zuchiya na sauke mai nauyi, na nemi waje na zauna akan tiri sita dake falon ina daɗa ƙarema tsarin wajen kallo, tsarine irinna turawan asali, babu tarkace da yawan kaya a ɗakin amman dake sun iya tsara waje wajen yayi kyau da sha'awa Sosai hakan zai baka dama ka samu lafiyayyen bacci ta yadda zaka gudanar da aikin ka yadda ya dace.
Miƙewa nayi naja akwatunana zuwa ciki, kai tsaye na wuce banɗaki nayi wankana na fito.
Saida na rama sallolin da ake bina kana na samu nutsuwa da zarafin shirya kayana a sib dake mun ci abinci a Airport bana jin yinwa, kuma ina da dambun nama da cincin dana tawo dasu.
Washegari da safe bayan nayi wanka na fito zuwa É—akin Shamsiyya akan ya zamu yi muyo cefanen kayan abinci tun wuri kafin monday mu koma bakin aikinmu.
A kan titin layin da muke akwai kantuna na saida kayan abinci wata balarabiyace ta nuna mana, itama ma'aikaciyar Bbc ce fannin larabci.
Ita tai mana jagora muka yo cefanen duk abinda muke buƙata kowacce ta jibge a ɗakinta.
Da daddare shinkafa da miyar kifi naci, na É—anyi miyoyi kamar kala uku na adana a firji sabida rage aiki.
Ranar monday muka É—unguma Bbc domin soma aiki.
Gaskiya ma'aikantansu suna da kirki da haba_haba da baƙi sosai haka sukaita janmu suna zagayawa damu suna nunnana mana waje.
Rigiji gabji ashe Bbc girma gareta hawa_hawa ko wanne hawa da ma'aikatansu.
Bbc Hausa
Bbc shashen turanci
Bbc shashen faransanci
Bbc shashen larabci
Gasunan da yawa kuma ko wanne fanni hawansu daban kuma akwai soyayya da halaƙa a tsakankanin ma'aikatan sabida al'umlace ƙasa_ƙasa yare daban_daban haka ma addinai daban_daban amman aiki kuma ya haɗeku ya dunƙuleku a waje guda kun zama ƴan uwan juna a ƙasar da baku da kowa sai kawunanku.
Madallah da shugaban shashen Hauwa shugaba mai mutunci da karamci da sanin ya kamata.
Gaskiya ita kanta Bbc wata jami'a ce ta É—aukar ilimi na musamman bazan rufeku ba.
Aikina dasu na kwana ɗaya rak ya haskamun abubuwa da yawan gaske. Babban abinda yafi komai burgeni dasu yadda tuƙuru suke son ci gaban aikin jarida, da ci gaban ma'aikatan gidajen tv da rediyo wannan dalilin yasa suke karɓo ma'aikata daga gidajen rediyo daban_daban mutum yazo yayi aiki dasu ya sake gogewa akan aikinshi ya sake samun horo na musamman.
Kai madallah madallah da Bbc da ma'aikatanta baki É—ayansu.
Lokacin tashi nayi muka wuce gida, mu bamu soma aikin ba tukunna dai, ana dai kan nunnuna mana yadda al'amuran suke ne tukunna.
Abinci na É—umama na zauna a lokacin na sake kunna wayata na kira wayar Innarmu ta manhajar whatApp a bidiyo ma na kirata nako taki sa'a tana É—akin Baba Sojanmu itace da kwana suna tare.
Mun gaisa dasu cike da farin ciki inata basu labarin yadda ma'aikatan Bbc suke da karamci, da irin yadda suke murna in suka ga sabon ma'aikaci daga Najeriya.
Bayan mun gama wayar dasu nan na kira Azgar da Sabira mun jima sosai dasu a waya muna gaisawa. Muna gamawa na kira Ƴan uwana mata.
"Ai munyi fushi sai jin tafiya kawai muka yi Hinduwa babu ko sallama? "
Yaya Saratu ba haka bane a dai yi haƙuri yanzu ba gashi na kirawo ba"
"Yanzu Hinduwa kin barma Asama'u Mijinyawa kenan gashi kin tafi tafiya mai tsawo wanda in da rabo kafin ma ki dawo ta haihu?"
Murmushi nayi mata tare da cewa.
Aikinane a gabana Yaya Saratu. Ko da inanan Mijinyawa ai mijintane itama, babu abunda zan tare mishi tunda a tsakaninmu dole yayi mana adalci. Bari in nuna miki É—akin da nake"
Na bagarar da hirar ta hanyar haska mata wajen zamana tana ta santi da taya ni murna. Da haka muka ƙarƙare wayar tamu dasu na ajjiye wayar tare da ajjiyar zuchiya. Take kuma Yaya Saratu ta hautsinamun lissafina a ranar kwanan baƙin ciki da tunane_ tunane kala_kala nayi.
Haka rayuwar Landan taci gaba da tafiya cikin jin daÉ—i da kwanciyar hankali sai ranar lahadi na samu damar zuwa gidan Abokin Baba Sojanmu. Su sukaima É—an tasi kwatance ya kaimu ni da Shamsiyya.
Gidansu mai kyau da tsari sosai gidane na ƙasa ga matarshi mace mai kirki da sanin ya kamata sunyi mana tarbar arziki, har Baba Soja ya kira a waya ya sanar dashi zuwanmu.
"Zata samu gurbin karatun mastas ɗinta Soja in P. H. D ma take so data gama mastas ɗin ta jona ai sai tayi babu laifi. Amman in sha Allah zata samu shiga na fahimci tana da hazaƙa da son karatun babu laifi, zanyi iyakar yina Soja Hindu ai tamu ce na tuno lokacin da aka haifeta mu kuma muna filin kwantar da tarzoma"
Dariya suka yi Baba Soja yaita mishi godiya. Bamu muka bar gidan ba sai dare su suka kaimu har gida suka ga waje har É—akina suka shiga na kawo musu dambun nama da abun sha.
Rayuwa taci gaba da garawa duk ranar Lahadi ina kiran ƴan uwana muna gaisawa harma da wasu daga cikin ƴan gidanmu. Rayuwar a Landan taci gaba da garawa, ta ɓangaren aiki kuma ilimin da muke kwasa ba na wasa bane gaskiya, kaina ya sake buɗewa sosai akan aikina.
Allah cikin ikonshi da Amincewarshi ni da Shamsiyya muka samu gurbin karatun mastas É—inmu a jami'ar Landan a lokacin Shamsiyya mijinta yazo suna zaune tare sabida yawanci ma'aikatan suna zamane tare da iyalansu, ko kuma iyalan su su kawo musu ziyara.
Nakan tuno Mijinyawa da Asama'u kaÉ—an bamai yawa ba sabida na riga na shafesu a babin rayuwata ni ba mace bace mai É—aura damuwa araina ta hanani cikar gurina ba, kuma inna wuce da sanin abu na wuce da saninshi har gaba da abada.
Sai dai fa a ranar da Shamsiyya mijinta ya iso mu muka je filin jirgi muka tawo dashi tun a mota naga irin soyayyar da suke gudanarwa sai jingina nayi da kujerar motar na lumshe idanuna inajin sabon ciwon da Mijinyawa ya jima zuchiyata da irin butulcin da yayi mun, da irin yadda suka yaudareni dashi da Asama'u.
A haka har muka dawo gida na shige ɗakina na zauna shiru ƙwaƙwalwata ta shiga aikin tariyomun rayuwarta ta baya da farkon haɗuwata da Mijinyawa da yadda har muka ƙulla halaƙar soyayya.