← Book details Tsuron Tsirin Tsandauri Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 39 OF 77

Sashe 39

Tsuron Tsirin Tsandauri Part 1 Complete Hausa Novel · about 9 min read

JAMA'ARE:.

Da yamma sakaliya Nanno na gaban murhu ita ke da tuwon dare ranar kishiyoyinta duk ko wacce tana ƙofar ɗakinta suna aikace_aikacen dake gabansu dai. Kwatsam sai ga Gawata da buhun kayanshi.
"Ahh Gawata ikon Allah ai kuwa Nawata yau ɗinnan ya koma ɓoto yazo kusan satinshi biyu kai kuma sai gaka yau"
Cewar Inna kenan kishiyar Nanno."
Tsugunnawa yayi har ƙasa cike da ladabin mutan ƙauye ya gaishe da iyayen nashi. Nanno tace.
"Shiga daga ciki bari a kawo maka fura yannzu akwai wacce Bala ya rage"
Miƙewa yayi yana sosa kai ya shiga ciki.
Gadone guda biyu a ɗakin lamba wan da kuma bono ya sha shinfiɗar zanin gado mai ɗawisu, ga kwaba bango guda shaƙe da jeren samiru da tasoshi an lulluɓe bangon ɗakin da kwatin ga kwatin bot zagaye da ɗakin jere da takalman masu ɗakin.
Ƙasa leda ce shinfiɗe sai alkuki da aci balbal a kai.
Jingina yayi da jikin bangon ɗakin yana jin babu kuzari da ɗanɗano sam a bakinshi. Ko wanne hali Hindunshi zata shiga in wasiƙarshi ta isan mata oho. Yasan yana ma Hindu so mai girma, amman da kanshi yasan yadda take son shi yafi yadda yake sonta.
Amman yana ganin sai dai suyi rayuwarsu a matsayin gwagware babu Aure domin babu rabuwa a tsakaninsu. Basu soma dan su bari ba, tunda iyayenta sunfi fifita iliimin boko fiye dana addini yasan ba zasu iya bashi Auren Hindu ba. Dama Qasimu ya faÉ—a mishi gaskiya Dundumin so ne kawai ya makantar dashi.
Nanno ce ta shigo da kwanon sha ta ajjiye a gaban Gawata.
"Mijinyawa lafiya kuwa na ganka babu kuzari sam a jikinka, ko wani abun ya faru a binni ne? "
"Babu komai Nanno gajiyace sai rashin jin daÉ—in ganawar da bamu yi da Nawata ba naji haushi sosai."
Kwanon shan ya buÉ—e ya saka ludayin duma ya soma shan furar. Duk son shi da fura É—aci yau take yi mai.
"Mijinyawa faɗamun gaskiya ko dai saɓani kuka samu da yarinyar da kake nema ne?
Kaga dama jiranka nake yi ka zo muyi magana.
Nawata sun daidaita da Uwatale muna shirin saka rana tunda Allah bai yi dakai za'ayi ba, amman dole tare za'a haÉ—aku a Aurarku zaifi ga waje nan sai ku yanka ku soma ginawa tun wuri."
ÆŠagowa yayi ya dubi Nanno yace.
"To matsala aka É—an samu daga gidan nasu. Amman in sha Allahu zamu shawo kan matsalar Nanno. Ni zanje masallaci daga nan zan wuce wajen Qasimu ya kaini gidan Yaya Jamila mu gaisa tunda ita a kusa take.
Su Shafa kuma gobe na zazzaga. Banga Auta ba tunda dai na shigo gidan?
"Autar Nanno. Tana can gidan Yayar taku dake ta haihu jiya tana taimaka mata da riƙon shi Habu ɗin tunda shekararshi ɗaya ne kawai"
Kai ya jinjina kawai ya fita.
A masallaci ya haɗu da abokan nashi bayan an isar da sallah suka dawo ƙasan bishiyar dirimi suka baje.
"Gawata na Hindu bada kanka a sare kaje gida kace ya faÉ—i. Ya Hindun take to? "
"Jazuli baka da dama. Hindu tana ƙasan zuchiyata a kwance lub"
Dariya suka kwashe dashi Ashiru yace.
"Baka da dama Baban soyayya ina mamakin a inda ka iya soyayya"
"Ahh ka mance dai. Shi da yake karanta littafan yaƙi harma dana soyayyan.
Su wannan littafin me yake da suna? Soyayya tafi kuÉ—i na Hadi Abdullahi Alkanci
Su kulɓa na ɓarna na Umaru ɗanjuma katsina
Su kwabon masoyi
Su in da so da ƙauna na Ado Ahmad gidan dabino
Duk fa ya karanta jiya nima na soma karanta wani littafi mai suna.
Matar mutum kabarinshi na Bashari Faruku Roukbah
Wasan kwaikwayone na Nura da jummai gaskiya jarumin yayi ƙoƙari gaya"
Murmushi Gawata yayi yace.
"Ashe zan sha karatu mutumina ba da ina baka shawar ka jaraba karatun ba kaƙi. Nima zaka bani matar mutum kabarin nashi in karanta, na tawo da sababbi sai in baka ka karanta ɗaya"
Sun daÉ—e suna hira har dai suka yi isha Qasimu ya ja Gawata can gidansu anan suka ci dambu suna kan cin dambunne Qasimu ya lura duk son Gawata da dambu baya wani ci, ya fahimci tun a wajen hirarsu hankalinshi baya jikinshi.
"Gawata kun samu saɓanine da Hindu ko? Naga hankalinka baya jikinka sam ina lure dakai sosai.
Meke faruwa? "
"To Qasimu hadda ma rashin farin jinina ni tunda a dangi duk wanda aka taya ma baya so yace zan auri ƴarshi ko ɗiyarta. Yanzu Nawata suka ba Uwatale shi sun amince zasu bashi, amman ni da akaso a tambayamun ita a shekarun baya ƙiri da muzu Goggo ta kakkauce zancan bata bari ma Uwatalen taji ba. Baƙin jininane ya bini har birni iyayen Hindu sun rabamu a yadda suka ci mutumcina ko sama da ƙasa zata haɗe nasan ba zasu yadda su bani ita ba. Kaji yadda mahaifinta yake turanci kuwa? Yaƙi hausa fur wallahi ga kayan sojoji ya saka.
Labarin komai ya zaiyana mishi.
"Lallai kuwa Gawata kana cikin damuwa. Amman in da rabon aure a tsakaninku wallahi saika Aureta nake faɗa maka. Ina mamakin abinda yasa ƴan binni basu ɗaukemu a bakin komai ba suke kallonmu a matsayin wulaƙantattu."
Sun daÉ—e suna rabe É—ayan biyu ko gidan Yaya jamilan ma basu je ba sun barma gobe.
Har gida Qasimu ya biyo Gawata dan yau kam anan zai kwana har zuwa lokacin da Gawata zai tattare inashi inashi ya koma. Tare suka shiga É—akin Nanno da sallama.
"Qasimu kaida mutuminne? Gandan_ gandan daku ba aure kun saka fita Binni a gaba. Wallahi kuma kanku faÉ—a fa. Ku zauna kuci tuwo"
Zama suka yi suna dai bin Nanno da dariya kawai.
Tuwonma Gawata ya dai ɗan taɓa dan kada Nanno tayi faɗa.
Nan ya janyo buhunshi ya ciro tsaraba kashi_kashi harda ta maƙota haka suke yi. Shima in zai tafi mai biyar mai goma duk sai an harhaɗa mishi, to shima fa dole yayo tsaraba wani abun sai ƙauye, amman ko babu komai hakan na ƙara danƙon zumunci da soyayya a tsakankanin maƙota gaya.
Saida ta bari sun kammala cin abincin tas kana tace.
"Matsalar me kuka samu da kai da yarinyar da kake nema É—in Mijinyawa? "
"Daga ɓangaren iyayenta ne su ɗan boko suke son su bata ni kuma gashi banyi boko ba"
"Baka yi boko ba kuma. Duk bokon da kuka shafe shakara sama da goma daga firamare har ta gaba da'ita. Kana gani in banda ku É—in waye yayi boko a cikin gidannan ga Æ´an uwanku nan na ragowar É—akin babu wanda yayi karatun. To akwai bokon data wuce wannan ne, ga Qur'ani izifi sittin a kanka, me suke so, ko dai kora da hali suke yi maka ne? "
Qasimu yace.
"Akwai karatuka masu yawa a gaba waɗanda muka yi sune dai tsanin hawa na gaba, amman karatu an dai yi yaƙi da jahilci. Irin karatun su Dauda shine karatu"
"Dauda ɗan wajen Tine da yake shigowa ƙauyannan da mota wanda akace yana aiki a binni?"
Gawata yace.
"Yauwa Nanno irinshi suke so Nanno, to shine aketa turka_ turka gashi tare akeso a aurar dasu su kusan goma a rana É—aya. Yanzu dai halin da ake ciki sunce ba zasu bani ba gaskiya a haka muka rabu dasu"
Ya ɓoye ci mishi mutuncin da suka yi sabida gudun abinda kaje kazo.
Sama da ƙasa Nanno ta rasa abinda zata faɗi ita a tunaninta matsalar daga Gawata ne tunda a cikin dangi da abokan arziki da dangin abokan zamanta babu inda bata tallata Gawata ba ko za'a dace amman duk wacce akaima maganar sai ta ƙi ko iyayensu su ƙi. Amman Nawata yayi budurwa rasuwa tayi, ta biyun da yayi kuma cikin shege tayi daga ƙarshe zaman garin ya gagareta ita da iyayenta suka bar garin.
To a baya har Uwatale Nanno tasu ta haɗa da Gawata amman mahaifiyar ta nuna taƙi, amman da tace a ba Nawata da gudu ta amince ba kwana_kwana. Duk da shi Nawata yana da kuɗinshi inda yake aiki yana samu sosai saɓanin Gawata da lallaɓawa kawai dai akeyi dan kada a zauna.
"Hmmm Allah ya rufa asiri. In suka dage sai ka haƙura ka nemi wata. Bana ga laifinsu ba su da ɗiyarsu ga mutumin binni da raina na ƙauye, ni kuma nace in kuka yi aure ko a ina aka Auro yarinya to a nan ƙauyen da gidan zaku zauna bana son zaman bariki irin na Dauda kawai a je a shanye maka ɗa sai yadda danginta sukai da shi."
Su Gawata dai sukai shiru babu ta cewa.
Maƙotane sukaita aiko da kwanukan abinda na baƙo kusan kwano goma aka kawo. Gawata dai lallaɓawa yayi suka fito zuwa ɗakinsu shi da Qasimu. Matan gidan da yaran kab suna tsakar gida manyan sun ware kansu yaran ma. Gaggaisawa aka kuma yi anata zolayar Qasimu yau yaga aboki.
Ko da suka shiga É—akin mai katifar yayi da tabarma karauni Gawata bashi da sukuni. Duk yadda Qasimu yaso ya ribaceshi ya mance damuwar tunanin Hindu wallahi ya kasa cin nasara.
Kafin kuwa Safiya ya wayi gari da zazzabi da ciwon kai mai tsananin gaske.
Daddaurewa yake yi baya son Nanno tasan halin da yake ciki.
Shi yasa ma sha biyun rana a gidan Yaya Jamila tayi musu, da sukai azahar suka wuce gidan Yaya Zakiya itama sai zuwa la'asar suka baro gidanta suka nufo gida.
Suna tafe a hanya shiru_shiru Qasimu yace.
"Baka karɓi littafin matar mutum kabarinshi da kace zaka karanta ba. Bari in ɗakko maka tunda mun iso ƙofar gidan jirani kawai"
A jikin bishiyar ƙofar gidansu Qasimu ya tsaya yana ƙarema unguwar kallo.
Tunano yadda Hindu ta tsara musu yadda zasu gudanar da soyayyarsu da yadda zasu reni yaransu yayi. Murmushi kawai yayi daya tuno irin yadda Hindu take matuƙar sonshi kuma yake burgeta.
Fitowar Qasimu ce ta dawo dashi daga tunanin daya lula littafin ya karɓa suka wuce majalisarsu ta matasa aka shiga musu, Gawata dai ya kalli wannan ya kalli wancan ya rasa tacewa.
Acaɓa ne ya ajjiye Zakari a daidai majalisar da buhun kayanshi.
"Yauwa Gawata wallahi dama dalilin saukata anan kenan sabida kai zo mana"
Da sauri Gawata ya ƙarasa wajen Zakari dashi da Qasimu. Hannu yasa a ajjihu ya zaro takadda a ambalob mai ruwan ƙasa ya danƙa mishi.
"Musa mai yalo shine ya bani taladdarnan kuma ya roƙeni ta iso hannunka daga isowata to gashi na damƙa maka ita. Saƙone ƙawar Hindu Luba ta kawo tace a baka"
Zakari na faɗin haka ya saɓa bakkonshi a kafaɗa ya ƙarasa majalisar matasan aka gaggaisa ya gangara unguwarsu.
Sai da akayi sallar magriba Gawata ya maƙale a gefe ya buɗe takaddar ga abinda ta ƙunsa.
_ka sani zuchiyata in ta buga kaine sanadiyya. Gawata a duk sanda wasiƙata ta iso gareka ka tabbatar washegari ka kamo hanyar Kano kazo na ganka mu tattauna, in ba haka ba da kwatance zan biyoka mijina.
Wallahi babu mai rabamu sai mun yi Aure da izinin Allah.
In kazo, kazo gidansu Luba zata zo da dabara ta kirani.
Ko kuma in zauna in jiraka a gidansu Luban.
Gawata ina jiranka dan Allah kada ka gujeni a lokacin da nafi buƙatarka yanzu haka bani da lafiya a kwance nake ciwon sonka ya kwantar dani.
Matarka Hindu_
Ai da ganin saƙonnan Gawata hankalinshi ya tashi washegari sassafe yaima kowa sallama Qasimu ya rakashi har tasha saida motarsu ta tashi ya juyo.
Sabida lalacewar mota a hanya basu suka shiga Kano ba sai taran dare ga alƙawarin shi da Hindu ko kusa baya son saɓawa. Bashi ya iso ƙofar gidan ba sai wajajen tara da rabi, matasa suna zazzaune a waje ana shan iska.
Da ƙyar ma ya samu ya aika yaro gidansu Luba yace ana nemanta.
Chapter 39 · 0% Book details