← Book details Tsuron Tsirin Tsandauri Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 42 OF 77

Sashe 42

Tsuron Tsirin Tsandauri Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

ne bayan siyar da lemon da kake yi. Sannan kayi karatun addinine? " "A'a bani da wata sana'ar bayan wannan in sha Allah zan riƙeta da kyau iyakar ƙarfina kuma, amman ina da gonar gado wacce take haɗaka da abokin tagwaitakana, mu kan noma dawa. Batun karatu kuma na yi saukar Qu'ani mai girma, na yi haddar hadisai daidai gwargwado in sha Allah" "To amman a rana kamar cinikin nawa kake yi, ribar nawa kake samu da har kake tunanin iya riƙe mace kamar Hindu, kasan dai matsayinku ba ɗaya bane ko? " "Zan riƙeta in sha Allah ba zatai kuka da riƙon ba in sha Allah. Duk da na kasance ba mai ƙarfi ba" Baba Nagoɗi yace. "To Ganaral kaji iyakar magana sai abinda zai biyo baya na ƙarshe kuma in ka gama naka" Baba Soja ya muskuto yana dubanmu cike da ɓacin rai da baƙin ciki fal zuchiyarshi yace. "Yaro inna baka Hindu babu saki, babu yaji, babu ƙorafin da zaka kawo mun gidana, ko ta kawomun gidana, sannan dolenka ka mayar da'ita makatantar jami'a ka biya mata ta gama ta samu aikin yi tayi, kamar yadda akeyi a cikin gidannan, ni nake biya ma ko wacce ƴa kuɗin makaranta ki da tana gaban mijinta. Amman ita wannan kai zaka biya mata. Ko da wasa kada in ga ƙafarku da sunan matsalace ta kawo ku, zuwanma na lafiya bana so a cika zuwa mun gida ana ci mun abinci. Sannan zaka biya nera dubu ɗari sadakin Hindu, kayi mata kayan akwati kamar yadda za'aima sauran ƴan uwanta. Mun baka nan da kwana uku a kawo wannan sadaki cikin gidannan. Wannan shine sharaɗina akan ka da kanta kun amince." Shiru nayi ina tunanin ta yadda Gawata zai samo dubu ɗari a cikin kwana uku da akwati daidai dana ƴan birni, wannan korace kawai da hali sabida ansan bazai iyaba inya saɓa kwanakin sai su samu hujjar cewa basu suka hanashi auren ba gazawarshi ce. A lokacin sadaki baya wuce dubu goma, su Yaya Saratu ma da sukai tsada dubu ashirin ce da biyar masu daraja irinna shekarun baya. "Na amince Baba Allah ya nuna mana. Sannan in sha Allah zamu zauna lafiya albarkarku kawai muke bara a sanya mana. Sannan ku yafe mana ɓata muku da muka yi" Ya faɗa a sanyaye muryarshi har rawa take yi sabida kaɗuwa Baba Nagoɗi ya ɗaura da cewa. "Sati biyu ne yayi ragowa ayi bikin, muddin aka wuce kwana uku babu sadaki da kayan lefen baki ɗaya to Aure zai sauka a kanka zata auri Qazzafi tashi mun sallameka. Ke Hindu ki bishi kuje ku tsara yadda komai zai kasance" "Ina ai zai yi cike_ciken takadda" Cewar Baba Sojanmu. Baba Nagoɗi yace. "Haba janaral sai kace wani wanda aka ɗauka aiki. Wai kai me yasa komai sai kace sai an yi rubutune" "Manzon Allah SAW ma yace duk abinda zamu yi musamman abinda ya shafi yarjejeniya muyi rubutu. Babu damuwa zan rubuta" Cewar Gawata kenan. Baba Sojanmu ya ƙura mishi idanu tare da yin shiru, shi kam kanshi na ƙasa. "Ma firen saka sunanka anan, nan kuma ka saka hannu. Ka nutsu ka karanta takaddar" Da sauri ya karɓa, rubutun turancine nasan ba duka zai gane ba, haka dai ya saka hannu da sunanshi, Baba Sojanmu ya riƙe takadda ɗaya shima Gawata aka bashi ɗaya ya riƙe a hannunshi. Godiya yai ta yi musu. A hankali ya miƙe ya fito tsakar gida, nima na biyo bayanshi, Innarmu ce ta leƙo tace. "Hinduwa kuje daga falo can ku yi abinda zaku yi jikin ki ba daɗi bane dashi ga rana" To Innarmu" Gaba nayi Gawata ya biyoni mukaita ratse gidanmu ana ta leƙenmu ana al'ajabin abinda na gani na liƙema Gawata ɗan ƙauye futuk. Tabbas baƙauye ne amman babu duhun ƙauyanci tattare dashi kasancewar yayi karatun arabi da bokon matayassara. A ƙasan kafet muka zauna muna fuskantar juna cike da murmushi zukatanmu fes da farin ciki. "Kinga kudurar Allah ko Tutar so? Tunda abinnan ya faru na hana idanuna bacci ina roƙon Allah yasa ki zama mallakina duk da isata bata kai ta mallakeki ba, kwanana uku a kulle a sell, shima adda'a kawai nake yi ina kai kukana wajen rabbil izzati. In sha Allah zan zame miki huɗu a ɗaya zan zame miki madadin uwa, zan zame miki madadin uba, zan zame miki madadin miji, zan zame miki mijin nuna ma sa'a namijin duniya Hindu. Ubangiji Allah ya bani ikon tsallake jarabawar da aka ɗauramun. Gobe sassafe zan wuce jama'are inaga sai ranar ɗaurin Aure in munzo an ɗaura Aure kafinnan muga juna kuma. Hindu gashi babu kuɗi a hannuna da zan baki na hidimomin biki amman waɗanda zasu kawo sadaki da kayan Aure zan basu saƙon kuɗi su baki kiyi duk abinda ya dace" Ina murmushi nace dashi. Allahu shi kaɗai muke ma bauta Gawata, shi ya ƙaddara gareka nazo mata ko munyi daidai da juna ko bamu yi ba. Damuwata a ina zaka samu waɗannan kuɗaɗen a cikin kwana uku shine fargabata. Sannan batun wajen zama fa" "Tutar so baki da damuwa ko kaɗan hankalinki ya kwanta zaki ga ikon Allah in sha Allah. Wani hanzari ba gudu ba shine a Jama'are zamu zauna sabida Nanno taƙi yadda mu zauna a binni da matanmu zaki yi haƙuri da wannan bansan ko zaki iya rayuwa dani a ƙauye ba. Sannan na kasa sanarwa a gabansu Baba Sojanmu wallahi bazan ɓoye miki ba a lokacin da nake falon in da za'a tsaga jikina ba za'a tadda jini ba." Ashe tsugunne bata ƙare ba kenan jama'are, ni Hindu na shiga uku duk yadda akaso ɗaga mana ƙafa abun zai yiwu kuwa? A zahiri nace. Baka da matsala dani duk inda zaka ajjiyeni zan zauna da sharaɗin ba ajjiyeni zaka yi ka dawo birni ba, kuma zaka tsaya mun duk runtsi? " "Wannan ratayayyen hakkin soyayyane a wuyana ina da wuyan ɗauka. Na kuma sake yadda da wannan ƙauna zan nuna miki soyayya zan riritaki, zan tarairayeki har sai kin manta kowa da komai" Mun jima muna hirarmu daga bisani yayi mun sallama ya tafi, ni kuma na koma cikin ɗakinmu.
Chapter 42 · 0% Book details