← Book details Tsuron Tsirin Tsandauri Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 45 OF 77

Sashe 45

Tsuron Tsirin Tsandauri Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tun safe aka soma shigowa da lefe cikin gidan daga masu akwati biyar shine dama saitin sai masu huɗu babu masu ƙasa da hakan. Duka dai sonsanet ne kaloline suke bambamta da kuma irin kayan da aka danƙara a ciki. Cikin gidan namu duk Inda ka wulga ƙamshin kaji da toye_toyen kayan fulawa kawai akeyi. Banda lungunmu da yake tsit kamar ba kayan lefena za'a kawo yau ba abun mamaki da ɗaurewar kai. Shinkafa da miya da naman kasuwa Innarmu tasa su Yaya Saratu suka girka, sai zoɓo da akayi shikenan iyakar abinda tasa akayi, tana zaune tana waye _waye da kafinta. Saɓanin sauran lungunan da aketa soya kaji da abubuwan arziki. Nasan duk dan a tozartani ne yasa akayi hakan ko, ni kuma a lokacin ban damu da komai ba ni dai cikar burina shine kawai Gawata ya zama mijina daga haka bana neman komai, kuma ina ganin samunshi tamkar duniyata ne. Luba tana gefena muna aikin ƙus_ƙus. Sai kiran Innarmu akeyi tazo an kawo akwatin ƴan matan gidan barin da akayi la'asar yamma sakaliya, abubuwan arziki ba kama hannun yaro gaskiya. Sai daf da magriba muka jiyo shigowar dangin Gawata mata da kayan Akwatinsu Inna Abida ta basu izinin zama a falo. Mazan kuma suna falon Baba Nagoɗi. "Saratu kuje ku same su ganinan zuwa dallah" Cewar Innarmu da ranta ya sake ɓaci ita so tayi Gawata ya gaza da kanshi ya janye sai hakan bata faru ba, dama ni nasan shirin Baba Sojanmu kenan shi yasa aka gabza mishi kuɗin sadaki. Haka dai aka amshi akwatunan aka gabatar musu da abinci babu yabo babu fallasa ni da Luba muna ɗaki muna jiyo maganganun matan gida a falon amman bama iya jin me suke cewa. Sai da sukai sallar magriba da isha kana sukai musu sallama suka tafi akan sai ranar ɗaurin Aure in sun biyo ƴan ɗaurin Aure domin tafiya da Amarya, Allah ya taimakeni basu fasa ƙwan a Jama'are zan tare ba. Suma su Innarmu babu wanda yace dasu ina zan zauna. Innarmu ce ta shigo ta nemi waje ta zauna tare da yin tagumi tayi shiru. Yaya Saratu ce ta shiga shigo da akwatin tana masifa. "Wannan kwashen kayan abun kunya sune suke tunanin zamu ɗauki tukuici mu basu, har wata mai bakin surutu tana cewa ba'a basu tukuici ba yaba kyauta tukuici. Wa yace mata an yaba oho. In banda ƙaddara ina Hindu ina waɗannan ƴan ƙauyen. Ga kayan naki nan Hindu babu atampa ɗaya mai mutumci a ciki. Nayi shirune a falo sabida su Innah Abida amman kin faɗo kunya kuma kin gama bamu kin kai kanki ƙasa darajarki ƙasa warwas tayi." Innarmu tace" "Da nasan irin tsinkanin da za'ayi kenan da lefennan ba'a buɗe ba har saida suka tafi da mun watsa abubuwan arziki a ciki. Shikenan gida kuma ya ɗauka kenan har cikin unguwa cece kuce bazai taɓa ƙarewa ba sai dai ya lafa." Ambulan Yaya Zubaina ta jefo mun kan cinya tace. "Gashi nan shi shagon yace a baki. Ace kaya babu guda ɗaya da aka ɗinka a haka suka kawo mu suke so mu ɗinka miki kenan? " Innarmu tace. "Ai gara dai da basi ɗinka ba Zubaina, ma zabtare rabi a kai kasuwa a tsinto mata manya ko koddibuwa babu bare kuma super daga mai kaza sai mai tabarma sai soso shikenan fa. Allah dai ya kyauta. Saratu a ciccire kawai ki jefa a durowar can, akwai manyan atampopi a saman sib ki ƙirga ki zuba mata, sai a haɗa mata da ƴan masu dama_daman a cikin nasu, sabida dai ta saka su gani kar ya zame mata wata jarfar, dan naga danginshi basu da dama ne" Ni dai ban samu zarafin cewa uffan ba wasiƙar Gawata ma sai da dare ya raba na buɗe harda kuɗi dubu ashirin a ciki na kayan fitar biki. Washegari kuwa na haɗa da kuɗaɗena da nake ɓoyewa suka cika dubu talatin na damƙama Innarmu baki a taɓe tace. "Zan haɗa in siyo miki duk abinda ya dace yau ki samu ki kai ɗinki Amman da biye ta halinki za'ayi wallahi babu abinda za'ayi miki. To ina da mutane na kunya dole zan fita kunyarsu ga ƴan sa'ido da suka sakama auren ido suma, ga ƴan uwana da dangi duka dai" Haka akaita shirin biki ana saura kwana huɗu ɗaurin Aure gidanmu ya cika dam da ƴan uwa na nesa anata hidimar yin cincin da su nakiya na amare da shirye_shirye. Na dawo daga karɓo ɗinkuna kenan Innah Yahanasu take tambayata ai ya kamata in ma Gawata magana asan a wacce unguwar ya kama haya sabida batun jere ko? Yace sai ranar ɗaurin Aure in suka zo za'ayi komai amman bansan inda ya kama ba" Na faɗa gabana na faɗuwa burina a ɗaura aurenne koma menene ya biyo baya zai zama mai sauƙi jin a jama'are zan zauna zai iya sawa a ɗaura aurennan da wanin Gawata amman ba shi ba. Ana gobe sakun lalle akaita zuwa jeren Amare ko wacce anyi mata kaya na kece raini amman inaji su Yaya Saratu suna faɗin kayana yafi na ko wacce Amarya kyau da yawa. Da daddare aka soma mun kitso bamu muka gama ba sai asuba kwana akayi cur wallahi ana yi mun kitso irin namu na Kanuri. Bayan mun yi sallah kuma sai muka soma lalle ai kuwa ana gama yi mun makarai suka bigeni a kwance na wuni ga hidimar biki anata yi ni bansan inda kaina yake ba wai sunzo taya ni murna sai guɗa suke yi. Da daddare aka saka amare a lalle ni kuwa sai su Innah Abida ne suka saka ni a nawa lallen Sabida a gaskiya dangin Gawata basu zo ba sabida nisa, kuma basu da wanda zasu wakilta. "Yarinya sai kace bazawara ace ba sakun lalle wannan wanne irin Aure ne? " Inji Inna Abida Innarmu dake ɗauke da cikin maganganu da yawa na Innah Abida tace. "Aurene kamar ko wanne Aure ai sakun lalle al'adace ba addini ba bare ya zama wani abun dan Hinduwa bata sameshi ba. Abida duk yadda kike ji game da Aurennan dake da duk munafukan da kuke ta gutsiri tsoma sai aurennan ya zame muku tsuron tsirin tsandauri wanda baku da yadda kuka iya dashi sai Allah. Aikin banza da wofi ke Hindu tashi mu tafi Allah ya sanya alkhairi a cikin wannan Auren in sha Allah maƙiya kunya zasu ji kawai mu dai da amincewarmu akayi wannan Aure" Ni dai ina cikin mayafi Luba ta taimaka mun na miƙe muka shiga ciki. Washegari ranar Juma'a kenan aka tashi da tuwon ɗaurin Aure wanda akayi na dukka gidan, sai abincin da kake so kuma sai kayi da jama'arka anyi shinkafa da miya, anyi alala da kunun gyaɗa amman dai dangin Gawata masu zuwa ɗaukar Amarya tuwon aka ajjiye musu. Kayan akwatina kuma Innarmu kusan komai ta canja a zannuwan ragowar turamen masu haske ta bar mun su, ta yi mun kayan fitar biki kala takwas tayi mun. Ƙarfe biyu da rabi aka ɗaura Aure a ƙofar gidanmu. Ƴan uwan Gawata kusan mota gudane suka kutso kai suka shigo, ga ciki ga goyo duk a caɓe dai ga rana ƙata. Haka akai musu jagora zuwa ciki ni kuma ina gidansu Luba da ƙawayena biyu na unguwa dan ƙawayenmu na makaranta gargaɗin Luba nayi da kada a faɗa musu ni ban son fitina. Ina saye da lace fari mai adon zare ruwan zuma. Na sanya takalmi da mayafi da gyale ruwan zuma wanda a cikin akwatina yake shine babban seti a cikinsu, ɗan kunne da sarƙata itama ta cikin akwatine na sanyane sabida dangin Gawata su san na girmamasu sun kawo kuma na saka dan har cikin raina banji daɗin yadda aka sake mun turamen zannuwana dan kawai a nuna musu gazawarsu ba, ina da yaƙinin shi kanshi Gawata bazaiji daɗin hakan ba, ta yiwu ya haddace abinsu kuma yana so ya ga na ɗinka na saka. Ina fesa turare Luba ta shigo tana guɗa ta faɗo a guje. "Alƙawari ya cika Hinduwa ta zama matar Gawata ga kayanki nan a mota an zo dasu ƙofar gida ana zuba kayan Kitchen ke kinga kayanki kujerunki manya manya masu ɗan karen kyau wallahi, gaskiya an gwangwajeki gaskiya Hindu wai kinga kaya kuwa. Talatu kuzo dan Allah ku taya ni mu kwashe kayan Kitchen ɗin Amarya mu fita dashi maza" Ana cikin fitar da kayan ina zaune zazzaɓi na ɗebeni ina jin mutanen nawa a kusa dani sosai. Innah Abida da Innah Yahanasu suka shigo suka fito dani tare da innarsu Luba, ƙofar gidan danƙam ga motocin ɗaukata a jejjere bus _bus ne dukka gajiyayyu wahalallu. A haka muka ratse mutane muka shige ciki kaina a ƙasa sai hayaniyar biki akeyi mutanena suna sake matsowa kusa_ kusa. Muna shiga ɗakinmu saka ƙafar da zanyi naji Innarmu na rantsuwar sai dai a sakeni ba zani ƙauye ba. Ihu na daka na faɗi tim a ƙasa ina burburwa, mutanena suka tashi a gidan biki, da ƙyar akaita basu haƙuri suka tafi ni dai na dawo hayyacina dai_dai sanda Baba Sojanmu ya leƙo yana cewa. "Ku fito da'ita ko a sumen ne a wuce da'ita ko ina zai kaita ai mijinta ne kuma shi yace ya riga ya sanar mata acan zata zauna dan haka ku fito da'ita Hinduwa Allah ya bada zaman lafiya ya kaɗe fitina a tsakaninku ya baki wuyan ɗaukar matsalolin da duk suka taso miki. Ruwayya kema ki saka mata albarka fishi ya ƙare Aure ya riga da ya ɗauru" Ajjiyar zuchiya Innarmu ta sauke kana tace. "Allah ya basu zaman lafiya da zuriya ɗaiyiba Yahanasu kamata kuje" Nan fa dangin Innanmu suka miƙe tsaye suna wallahi bazai yiwu akai ni ƙauye a kashe mun rayuwata ba. Hannuna Baba Sojanmu ya damƙa, ba shiri na miƙe tsaye. Yana faɗa dasu Innah Yahanasu. "Wallahi sai ta je. Idan a bangon duniya zasu zauna menene naku? Yarinya dai ta san da maganar kuma ta amince ai shikenan." Baba Nagoɗi ne ya leƙo da sallama. "Ku fito mana a kama hanya waje ba kusa ba. Jama'are da fa nisa. Wai nace a ina Jama'are take ne ma janaral? " " Jihar Bauchi ne Nagoɗi. Muje zan kaita mota matan su biyo bayana." Baba sojanmu ya
Chapter 45 · 0% Book details