← Book details Tsuron Tsirin Tsandauri Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 67 OF 77

Sashe 67

Tsuron Tsirin Tsandauri Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Labari na bashi akan abinda ya faru. Jikinshi har rawa yake yi naji ya fita fuu ina kiranshi amman ina baiko ji ba. Sai jiyoshi nayi a tsakar gida yana faɗa akan bazai lamunci taka mishi mata da akeyi ba ya gaji ya kuma isa. Da sauri na fito gidan harya ɗinke da jama'ar gidan ƙarason nayi nace. Babu komai kayi haƙuri wata rana zai zama labari" "Labari in kika haihu ba, baki da aiki sai zaunar da miji kina kwatanta kishi yadda zai ƙyamaci danginshi, so kike a zuba miki idanu ki illata musu yara sabida baki san zafinsu ba ko?" Cewar Yaya Jamila tana yi tana bubbuga cinyoyinta da tafukan hannayenta du biyun. "Ke Yaya jamila nace ya isheki ya isheki, haka wanne irin jahilci ke sa kuke mana gorin haihuwane. Shin kuna ganin ku Allah ya fi sonku ne daya baku haihuwar? Wallahi ba haka bane sau nawa muke haifar yara su zame mana masifa ko silar zubar hawayenmu. Hindu dai matatace, zamana take yi, na rantse bazan lamunci cin fuska da cin mutuncinta ba akan abinda bata da ikon bama kanta. Shin in matsalar rashin haihuwar daga nine fa, me yasa ba'a ma maza gorin haihuwa dole sai mata, shin mata na iya ma kansu ciki ne koko yaya? " Murmushi nayi kawai, nace. A tunanin ƙauyawan gidadawan danginka ni zan ba kaina haihuwa ai. Ke kuma Jamila kul ki shiga taitayinki ki kuka da kanki, wallahi zan miki abinda zaki jima kina kwance kina jinyar da babu wanda zai iya baki magani." Na juya na shige ɓarayina. Na bunka hayaƙina na shafe jikina da maganina dan naji halamun mutanen a kusa kusa ni kuma yau nake son amayar ma da mijinyawa buƙatata ko Allah zaisa na dace ya amince mun duk da ni akan karan kankin kaina nasan zaiyi wuya satar ɗan mace mai ido ɗaya. Ashe wannan rikici bana ƙare bane dan saida takai mijinyawa Yaya Jamila ta mareshi ya rama, ya bata lafiyayyun mari biyu. To kunsan a ƙauye babban wa namiji, ko babbar Yaya mace, jinsu suke yi tamkar su suka tsugunna suka haifi ƙannensu, fawar da suke da'ita yawa gareta shi yasa ake samun matsaltsalu dasu, saɓama umarninsu ma tamkar zunubi ne. Dambe ne ya kaure a tsakankanin Mijinyawa da gambonsu ina zaune naji hayaniya gida ya cika fam amman na kasa fita in tashi ma na kasa ni bansan a wanne halin nake ba har sai washegari shima da rana. Anyi ɗauki babu daɗi sosai saida na dawo hayyacina mijinyawa yake labarta mun abinda yake faruwa kuma Nanno ta umarceshi da ya ƙara Aure sannan wa'adin data ɗaukarmun yana cika muddin ban samu ciki ba zata sa ya sakeni in tafi dan yanzu haka ta bashi umarnin ya turani gida bata son ganina har sai sanda ta neme ni, tayi kuka harda tumami akan dole sai na tafi gida bata ƙaunar ganina, nazo ni zan tarwatsa mata gida" Amman kasan a kan sharaɗin da iyayena suka gindaya maka babu batun saki, bare yaji ko, kuma a gabanka suka ce muddin hakan ta faru to dole sai dai in nemi inda zani ko? To bari kaji in faɗa maka ka sake ni kawai, nagaji da waɗannan iskancin da ake yi mun a cikin gidannan Mijinyawa ta faru ta ƙare kaje kayi aurenka" Na yi maganar ina ƙanƙance idanu na ɓacin rai. Kuma ɗaurawa nayi da cewa. Nifa mijinyawa wannan jafa'in yafa isheni ka sakeni kawai kaje ka auri wacce zaku haihu kuyi rayuwarku nima inje in auri miji daidai ni na koma makaranta na cika gurina dana iyayena. Dan wallahi in dai kai nake Aure na tsallake kowa na zaɓeka to fa daga ranar da ka yadda zaka ƙara Aure, daga ranar ka rasani har gaba da abada." Zafi kan zafi na haɗa ma Mijinyawa duk inda ya buga babu daɗi dan nima na kafe akan mu rabu na gaji bazan je gida ba sai da takaddata na kuma kafe akan matsayata yasan bana juyuwa ba'a canja mun ra'ayina. Wannan shine karon farko dana taɓa botsare mishi na fitittike na tashi hankalinshi, na saka shi a uku. Saida aka kwana bakwai cur ana abu ɗaya, Nanno na cewa ya sallameni in tafi, ni kuma ina cewa a bani takaddata, har umarni ta bashi sau uku akan ya bani takaddata in tafi tunda shima ba ganin mutumcinshi nake yi ba. Ni kuwa ko gezau na ƙeƙashe ƙasa nace. Daga ranar daya tafa mun takaddata, daga ranar Nanno kin bar ganina har gaba da abada. Sai yaje ya auri mata ɗari ma in ana Aura" Inayi ina zazzare idanu. Duk da a tsorace take saida ta nuna kanta da ɗan yatsa tace. "Ni kike faɗama wannan maganar? " E" Itace kalmar dana faɗa ba ko ɗar. "Hindu kiyi shiru" Ai saina miƙe da a zaune nake fa, na cire zanina ya faɗi daga ni sai gwari na tsuma nace. Bazan yi shirun ba, nace bazan yi shirun ba Magawata" Sun ɗauka makaraine, sum_sum_sum Nanno ta fita, ni kuma ras nake turace kawai ta kaini bango. Matsowa yayi kusa dani ya riƙe mun hannu, na saka dukka hannayena biyu na tureshi da dukkan ƙarfina ya faɗi yib a kan kujera. "Subhanallahi" Ya miƙe da sauri, na kuma tureshi ya koma, na tsaya a kanshi ina huci tamkar kumurci. Karatun Qur'ani kawai yake ta rerawa yana tofeni da yawu. Wallahi ranar yaga abu sosai. Sai da Kawu yazo yaima tubkar hanci akayi sulhu tsakanin Yaya Jamila da mijinyawa ya bata haƙuri itama ta bashi, ya kuma tursasa Nanno akan ta janye batun in tafi gida babu ruwanta. Ina zaune a kan tabarma ina tuno gida da ƴan uwana da yadda rayuwarsu take ta ci gaba suke ta samun ɗaukaka, ga yaransu a gefensu. Ni inna tuno nawa rayuwar Auren da soyayyar miji kaɗai na tsira, soyayya bana jin zata iya riƙeni a yanayin da idanuna suka gama rufewa ɗa ko ƴa kawai nake da buƙata na gaji da gori har kunyar haɗuwa da dangina nake yi ko wani sha'ani ya kaini gida, dan kafatanin ƴan gidanmu babu wanda baimun gorin haihuwa ba. Damma a tsaye nake, duk wanda yai mun gori na dena ƙyalewa saina faɗama mutuwa, tunda kai cuta ka faɗamun wallahi. Gwauron numfashi na ja tare da amsa sallamar mijinyawa wanda shigowarshi kenan fishi muke da juna magana wannan bama yi face gaisuwa yau kwana bakwai Kenan kuma wannan shine karo na farko a rayuwarmu da muka yi faɗan da muka kasa shirya kanmu kafin gari ya waye. Duk da mijinyawa ya buƙaci haka nina matsa lamba badan bana gasuwa da hakan ba sai dan dauriya da jumurin ɓoye damuwa dana fishi. Wallahi a cikin kwana bakwai saida yayi ramar da duk wanda ya ganshi yasan ya rame. Miƙewa nayi zan tafi bayan na ce dashi. Ga abincinka nan sai da safe" Na juya zan shiga ya riƙo hannuna ba shiri na lumshe idanuna ina ma mijinyawa wani irin so marar abun misali, ina tsananin kishinshi fiye da tunanin mai karatu, batun matar da aka bashi yafi komai yi mun ciwo sosai kuma bana ji a jikina da zuchiyata zan iya raba mijinyawa da wata macen na gwammaci ya rabu dani matsawar bazai iya rayuwa dani ni kaɗai ba, inanan daram akan matsayata. Balle wannan auren da akeso a yishi a matsayin hujjar na kasa haihuwa shine akaso a auro mishi wata macen a bashi ita dan tazo ta sama mishi yara ni in zauna a matsayin me to? Duk wuya da bijirewar da nayi sai in tashi a tutar babu a gidan mijinyawan dana ɗaukeshi na shure ɗan uwana Qazzafi. Wanda a yanzu ya sake samun matsayi, ya sai mota mai kyau ya samu sukuni da nutsuwa sosai, ga matarshi da yaranshi biyu dukka maza, kuma har gobe sona na yawo a jikinshi. "Tutar so kwana bakwai cur kina azabtar dani, tako ta ina babu daɗi shin ba zaki ma mijinyawanki mai yawan ƙaunarki afuwa ba. Tutar so shin ta ina nake da lefin da harna cancanci kiyi watsin ruwan tsarki dani? shin bakya ganin ƙoƙarina da jajircewata akan lamarin aurenmu? Fishi da gaba dani shine sakamakon da zan samu a wajenki kenan? " Sai yayi shiru ni kuma ban juyo ba ina dai ta nazarin maganganunshi. Tabbas baida wani laifi tunda ba ƙashin kanshi bane yace zaiyi aure sabida bana haihuwa ba. Amman indai mace aka kawo mishi a matsayin mata watan watarana dole sai yayi ruf da ciki a kanta babu mamaki ma a ranar da aka kawota. Shikenan in suka zama ɗaya ta haifa mishi yara to mecece makomata, matsayina kuma na menene a gidan? " A hankali nace. Idan matar da za'a Aura ma ta shigo cikin gidan ta sama muku abinda na kasa sama muku kai da danginka, to ni menene makomata ko amfanin zamana da kai. Ƴar reno zan zame ma matarka, ko ƴar aikinta zan zamane, ko kuma a matsayin me zan zauna? Mijinyawa bazan rufe maka ba daga ranar da aka ɗaura aurenka da wata mace bisa dalilin danginka na ganin gazawata tabbas kafin Nanno tasa ka sakeni a wulaƙantani ni da kaina zan nemi sakin kuma dole ka sakeni wallahil azeem ko da a gaban kuliyane. Hannuna na fisge na shiga ciki na kwanta a gadon rigingine inata lissafin dokin rano. A haka ya shigo ya hauro gadon shima ya kwanta rigingine yace. "Banyi tunanin akwai ranar da zata zo ke da kanki ki dinga furta mana kalmar rabuwa ba. Tutar so kamar kina mance da yadda akayi aurenmu da alƙawarin dana ɗaukarma iyayenki. Babu abinda na mance Tutar so, sannan bazan bari wani nawa ya wulaƙantaki ba, na fahimci bakya ganin duk ƙoƙarin da nake yi. Hindu irin son da nake miki ruwa da iska basu isa sun rabamu ba, ko su Nanno sai dai suyi haƙuri kin zame musu tsuron tsirin tsandauri babu yadda za'ayi dake. Bazan taɓa auren Kandala da suke son in aura tazo ta haihu mun ba. Ba ita kaɗai ba, babu wata mace a duniya da zata haɗa miji dake, mijinyawa naki ne, wannan shine kaɗai sakamakon wannan sadaukarwa taki gareni, matan duniya a matsayin maza jinsina nake kallonsu, kece kaɗai mace tilo a idanuna, zuchiyata, gidana,
Chapter 67 · 0% Book details