← Book details Tsuron Tsirin Tsandauri Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 77

Sashe 14

Tsuron Tsirin Tsandauri Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Gidane gidan Gandu mai matuƙar girma da yawan taron yara. Gidan rikici da munafurci, gidan rarrabewar kai da son ganin kaine a sama. Gidan da kusan ƴan wannan ɗakin na son ganin beken ƴan wannan ɗakin. Kai gidan yawa gidan masifa, gidan yawa gidan munafurci da girmama ƙaramar magana izuwa babban al'amari kuma mara gogewa duk tsawon zamani. Wannan dalilin yasa ko wanne ɗaki suna tattalin maganar da zata fita, abun arziki kaɗai ake shela na tsiya kuwa sai dai ya fito da ƙarfin gaske. Baba Nagoɗi shine babban wansu Baba Sojanmu, amman asalin sunan Nagoɗi sunan mahaifinsu Baba Sojanmu ne, bayan ya haifi yaronshi na fari sai ya saka mishi sunanshi suna ya bishi Nagoɗi. Shine ya soma fitowa cirani zuwa Kano asalin mahaifarsu kwantagorane dake jihar Naija su ƴan asalin canne. Lungun Baba Nagoɗi shine a farkon gidanmu. Yana da mata huɗu da yara ashirin da shidda. Sana'arshi itace saida kayan kwalliyar dawakai, da alkyabba, da takalma, da mafici da duk abinda ya danganci kwalliyar dawakai da sarakuna. Shaguna biyu gareshi a jere da juna shi yana cikin ɗaya yaranshi maza na cikin ɗaya waɗanda basa aikin kaki, ko aikin gwamnati kenan. Sai Lungun Baba Kumainu dake da matan aure uku yara goma sha shidda. Sana'arshi itace saida su kibiya da manda, da mangul a nan kasuwar kurmi shima. Sai Lungun Baba Sogiji mai mata uku shima da yara ashirin cib. Shi kuma shagon niƙan garine dashi a cikin kasuwar Ƴan lemo nan Na'ibawa. Sai lungun Baba Sojanmu. Shi kuma ritayat sojane har ya kai genaral kafin yayi ritaya. Yana da mata uku da yara talatin maza huɗu daga ɗakinmu duk sojojine su. Sai lungun Baba Alƙali Shi kuma macen Aurenshi ɗaya ce tilo da yaranshi shida kasancewar ɗan bokone sosai alƙaline a kotu. Shi da Baba Sojanmu ne kaɗai sukai karatun boko kuma suka ɗauki boko da mahimmanci musamman dai Baba Sojanmu da bashi da aiki sai son yaga ana ƙaro ilimi. Baba Alƙali yana da zurfin ilimi sosai. Sai lungun Baba Dogara. Lungun masifa da bala'i kenan shi dai matanshi huɗu amman ko yanzu yaga wata zai dawo ya saki wata ya kawo wata. Yaranshi shima zasu yi talatin harda waɗanda iyayensu basa gidan. Yana siyar da kayan marmari Anan ƴan lemo dangin su kankana, mangoro da dai sauransu. Kunji yadda tsarin gidanmu yake. Ko wanne lungu abincinsu sukeyi ba wai ƙatuwar tukunya ake ɗaurawa guda ɗaya ba. Gidanmu yana da girma sosai ga filin tsakar gida fetal. Da Inna Meramu na soma cin karo tana zaune a ƙofar babban falon da shi ya haɗe kan ɗakunan iyalan gidanta tunda duk lungunan irin gini ɗayane sak. Wanki take yi, Inna Baballiya Kishiyarta kuma tana daga cikin madafi. "A_a Duwaf kin dawo daga Abujanne. Akace mana kinje wani taro da Bbc ta gayyaceki, ince Bbc zaki koma da aikine?" Cewar Inna Mairamu, ai kuwa Inna Baballiya na jin haka tace. "Ai ina Bbc ta manyan kaice fa Yaya Mairamu ai sai dai taje taron kawai. Duwaf ya jikin mijin naki?" Murmushin mamaki nayi tare da cewa. Jikinshi da sauƙi ina wuninku? " Nan aka gaggaisa ragowar abokan zaman nasu ma saida na bisu har ɗaki na gaishesu. Duk lungun daka shiga sai kabisu ɗaya bayan ɗaya ka gaishesu da waɗanda suke yinka da waɗanda bama yin naka suke ba basu ƙi su ganka a ƙasa ba. Ga shegen kallon ƙasan zani, da takalmin daka sako, da mayafinka. Allah cikin ikonshi ni da yarana dai kullum cikin sutura muke dan bana wasa da siya mana sutura sabida gidanmu ana yawan yin sha'ani ni kuma akan in fita kunyar ƴan gidanmu na gwammaci inci bashi kuɗi ya hau kaina a ganni dai fes. Ƴan ɗakinmu gaskiya ko wacce a cikin rufin asirinta take tunda gaskiya muna karatu sosai ko wacce tana da aikinta harma da kasuwanci. wata iriyar rayuwar gasa da son kowa ya nuna shi shine haka muke yi daga kan iyayen namu mata, har zuwa kanmu. Muma a hakan muka tsinci iyayenmu akai su kuma iyaye madubaine ga ƴaƴansu. Wata rayuwar ƙaddara ke zaɓama tasowa kake yi ka ganka ciki. Sai wanda Allah yaso shine sai ya kasance shi na dabanne. Yaran lungun Baba Dogarane kaɗai basu yi karatu mai yawa ba iyakarsu Sakandare kawai sai Kakale data ƙuƙuta a gidan mijinta tayi NCE shine ma ta samu aikin koyarwa a wata firamare ta cikin unguwar da take aure. Baya ga ƴan lungunsu gaskiya kowa yayi karatu daga masu digiri sai masu mastas a maza kuwa harda masu PHD amman babu a mata sai ni da nake tunanin in sha Allah da ikon da Allah yaima Annabinmu Arrasul sallalahu alaihi wasallam saina yi PHD bazan sake zaman bautama miji da son ganin na burgeshi ba. A waɗannan lungunan akwai soja wasu ba ɗaya ba, ba biyu ba. Saida na gama zagayena na dawo Lungunmu. Da ɗakin Inna Abida na soma itace a farko. Babban falone sosai mai ɗauke da ɗakuna falle_ falle guda biyar. Kowacce ta ɗauki ɗaya Baba Sojanmu ma ya ɗauki ɗaya ɗayan daya rage kuma ake ajjiye shirgi da kayan abinci dai haka. Falon kujerace doguwa guda ɗaya sai kafet malale a falon, sai tv da wata kwaba mai cike da littatafanmu da jaridun Baba Sojanmu. Da sallama na ɗaga labulen ɗakin Inna Abida da Iyami muka haɗa idanu tana tsakiyar gado tana ba jaririyarta nono, Inna Abida kuma tana zaune tana ƙulla sikari abinda take saidawa kenan. "Duwaf kin dawo daga taron Bbc ɗinne? " Nadawo Inna Abida, na sameku lafiya? " "Ah lafiya lau ya Mijinyawa da jikin? " Jikinshi da sauƙi Iyami wankan gida tazo yine? " "E wallahi Duwaf wanka nazo yi nima inji abinda ake ji" Murmushi nayi nace. To in banda abinki ai wankan gida yanzu ƙauyancine yaushe zaka baro ɗakinka ka dawo gidanku kusan wata biyu" Na ƙarashe ina taɓe bakina. Inna Abida tana dariya tace. "Ato faɗa mata dai. Gata ga gidan taci uwar da akeci faɗan Baba Sojanku ma ya isheta" Da haka na leƙa ɗakin Inna Turai muka gaisa kafin na shiga ɗakinmu. Kasancewar ɗakunan suna da girma yawanci duk sun rarraba da kwali, wasu da gini kamar na ɗakinmu an cirema Innarmu falo ƙarami kujera doguwace kaɗai a falon sai kayan kallo, uwarɗakin kuma da girma. Tana zaune tana shan shayi ga turaren wuta a gabanta a kasko yana tashi, ƙafarnan sai sheƙin mai take yi ga lallenta shar. Yaya Saratu da Yaya Zubaida suna kan gado sunyi ɗaiɗaya da atampopi da lesuka sunata surutai. "Hindu kina tafe ashe har kun dawo daga Abujan? " Zama nayi a gaban innarmu nace. Innarmu kinsan me Inna Baballiya take cewa a gabana kuwa? " Nan na labarta musu abinda tace. Yaya Saratu tace. "Gidannan ba zasu taɓa dena hassada da baƙin hali ba. Kuma in da rai da rabo sai kiga kin zama ɗaya daga cikin ma'aikatan Bbc ɗin badai aikin da kike yi suma suke yi ba? Kinsan ai mijin Kandenta ma'aikacin Bbc ne shi yasa take ganin Bbc tafi ƙarfinki. Hindu kin haɗu dasu Badariyya tijjani ƙalarawi kuwa? Baiwar Allahnnan tana burgeni gaya wankanta yana fita" Ai kuwa mun haɗu har ma da hotuna da bidiyos gajeru da muka yi." Wayar na miƙa musu ni kuma na shiga shan shayi muna hira da Innarmu. "Batun mastas ɗinki kiyi ƙoƙari shekara mai zuwa ku soma ke da ƴar uwarki Baba Sojanku ya matsa jiya inaji yana ma ƴar uwarki tsiya akan karatun itama to ita tace mijinta yaƙi yadda amman yace zaije ya sameshi su tattauna dole ya barta ta ƙara karatu tunda ya iya barinta tana aiki me yasa ba zai barta tayi karatu ba" Gaskiya kam zan jona in sha Allah ni so nake ma inna soma inyi har Phd kawai in wuce wajen Innarmu nasan Baba Sojanmu zaiyi murna sosai. Nan mukaita tattaunawa daga baya su Fhatsima suka shigo. Ba ni na bar gidan ba sai bayan isha tunda munyi waya da Azgar yace an sallami Mijinyawa suna gida hakanne ma yasa na miƙe ƙafata a cikin ƴan uwana naita hira ina jin sauƙin abinda ke cin ƙasan zuchiyata. Da muka tashi gidan muka nufa kai tsaye. Ai kuwa falona a cike da su Yaya Jamila dake yana da ɗan mabuɗi a wajenshi, hamshaƙin yana kwance a kan goduwar kujera muka shigo. Da ƙyar suka amsa sallamata harda Uwatale yau itace a zaune a falona anata hira hiye, sabida sunga bananan. Fuskata kadaran kadahan na nemi waje na zauna. Ina wuninku" Na faɗa babu yabo babu fallasa. "Kin dawo Tutar so? Ai ni da naga tara saura banyi ma tunanin kun dawo ba, na kikkira wayarki baki ɗaga ba." Wayar tana cikin jaka banma gani ba. Mun dawo tun yamma yara naje ɗakkowa acan gida, kuma motatama tana gidan" Buɗar bakin Yaya Jamila sai cewa tayi. "Sabida son yara shine har sai kinje kin ɗakkosu ma su ba zasu tawo da kansu ba? Batun mota kuma ai ta fita daga sahun taki dole ki bama mai mota motarshi tunda dai yanzu bashi da mota tashin tayi rugu _rugu sai dai a yayyankata." Miƙewa nayi saɓe da jakata nace. Son yara ai Yaya Jamila ban kaiku ba" Ina dariya na mayar mata da martani" "Muna son yaran zamu bar Mijinyawa da matar da ita ba juya ba ita ba mai haihuwar ba, wannan tsirarin yaran har yarane gasu Uwatale da akayi bikinku tare sabida jarumtarta har gwarne ta dinga yi" Wato wannan kalmar ta dokeni sosai amman bance mata komai ba taci bashi dan wallahi saina mayar mata da martani. Ɗakina na shige na watsa ruwa na sallaci isha na saka kayan bacci nayi kwanciyata ina jiyo muryoyinsu ko tare dashi zasu kwana ohon musu dan bai dameni ba sam. Sai can wajajen sha ɗayan dare naji fitarsu shiru mijinyawa zai leƙone naji shiru har sha biyu. Miƙewa nayi na leƙa ta gefen ƙofata da ban rufeta kirib ba. Na hangoshi yana ta danna wayarshi yana murmushi. Nima murmushin nayi kawai na saki labulen nayi kwanciyata ƙirjina na soya mun Duniya in akace akwai ranar da mijinyawa zai iya rikiɗewa ya koma haka wallahi bazan amince ba. Irin son da nake yi mishi fa bana wasa bane da kanshi yasan son da
Chapter 14 · 0% Book details