← Book details Tsuron Tsirin Tsandauri Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 71 OF 77

Sashe 71

Tsuron Tsirin Tsandauri Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hmmmm rubutu nayi mai jan hankali dangane da halin maza da irin son kan da maza da yawa suke dashi, bance duka ba kafin a caccakeni. Sai na bi tsokacin da rubuta takaddar da wata baiwar Allah da mijinta yai mata zalunci, daga ƙarshe yai mata sakin wulaƙanci, da dai sauran labarai akan rayuwarsu marar daɗi har idanun yaronta ɗaya ta rasa ta dalilin uban ɗan da kanshi. Tayi ƙorafi ance to ai Ubangiji ne. Kuma yaron yazo tare uwarne a yayin da uban yake mata dukan galila. Na ɗaura a shafina na Facebook na tura a zaurukan whatApp ɗina da nake dashi guda uku. Har zan ajjiye wayar tawa in gabatar da sallar isha sai naga shigowar saƙo da buƙuwar lamba naga kuma an kirani da Hindu Nagoɗi, a tunanina ƙawatace ta makaranta wannan yaja ra'ayina na buɗe saƙon. Hotuna uku na gani ɗaya Asama'u ce a jikin mijin yawa yana rungume da'ita tsam idanunshi cike da buƙatuwa sun lumshe sun fito da wani mai_mai Asama'unce da kanta ta ɗauki hoton. Hoto na biyu na ranar ɗaurin Aure ne da gani. mijinyawa na ƙurama idanuna banga annuri da zaƙwaɗi tattare dashi ba sam. Amman yayi kyau fatarshi lub ga wannan tozali dake sake gayanta gayenshi ya fito ras idanunshi, amman na banza a wajena, tur da Mijinyawa. Ta ɓangaren Asama'u kuwa tamkar wacce akaima bishara da gidan Aljannah. A kanta na zurfafa kallona tamkar ƴar sandar dake son gano gaskiya ta idanun mai laifi. Na fassara dalilan annurin fuskarta fin kashi talati. Murmushi nayi tare da cije gefen leɓena na ƙasa ɓangaren hannun hagu. Hoto na uku kuma Asama'u ce a kan cinyar mijinyawa a ofishinshi har hotonmu dake kan gaban teburinshi ina hangowa, da atampar da Innarmu tayi musu anko da Sabira a jikinta, kanta na kan wannan ƙirjin dashi yafi komai ruɗata shima dashi yake taƙama in dai a gabanane, a da can da duniyarmu take kwance nake nufi. Tuno sanda aka miƙomun Asama'u nayi, na sanya hannu na karɓeta na rungume, yarinyar tayi lub a kan ƙirjina, irin lub ɗin da tayi a ƙirjin mijinyawa a jikin hotonnan. Sai rubutu a ƙasan hoton _Hindu Nagoɗi_ _Yaya akaji da zafin rasa miji, yaya akaji da zafin yadda Asama'u ta ƙwace mijinyawa a wajenki. Nan _nan kusa zaki ji kyakkyawan labarin haihuwar Asama'u_ _Kinga yaranki guda biyu kacal da kike tunanin su kaɗe zasu mamaye gadon dukiyar mijinyawa sai ki sauya lissafi wannan karon anci Kanuri da yaƙi._ Shikenan iyakar abinda aka rubuta. Ko dana duba sama dan ganin hoto sai naga kamar an kulleni bulokin. Dannan lambar nayi ya kaini wajen suna Alhamdulillahi aka rubuta a wajen sunan. Lambar nake ta kallo kamar a jiki zan samu bayani. Luba na kwafe lambar na turama da ɗan taƙaitaccen rubutu. Ki bincika mun waye mai lambarnan Luba. Turomun hotunan mijinyawa da Asama'u akayi kana aka kulleni" Shikenan abinda nace na ajjiye wayar nayi sallah isha na zauna da Qur'ani shiru a cinyata ina rabe ɗayan biyu, zuchiyata tafi tunanin Uwatale ce. To ni menene nawa, itama menene nata Uwatalen? Mijinyawa dai in yaso ya mayar da Asama'u cikinshi ya adanata ƙarshen zama tashi kenan. Kai amman ba Uwatale bace bata san wannan lamarin ba, kuma ba sani zata yi ba. Babu mamaki Asama'unnce tana ganin karanta ya kai tseko, tasan sirrina, ta kwanta da mijinyawa gani take yi tamkar ƙarshena kenan. Murmushi nayi zuchiyata cike da mamaki da raɗaɗin zafi. Wani turiri da wasu munanan hasashen da banso zuchiyata ta hasasomun ba na shiga yi. Murmushi na kuma yi har ina rufe bakina da hannuna. Mijinyawa kenan an dai faɗi babu nauyi gaskiya, an kuma ci baya wallahi. Wani irin ciwo dake cikin ƙirji ke tuƙamun a cikin zuchiyata yana murɗamun notukan kaina, inaji suna kuncewa man kaina na tsiyaya. Sai ajjiyar zuchiya nake saukewa kawai, tare da ambaton Allah a fili. Tunda muka rabu da Mijinyawa rabuwar da suka tafi ɗaurin aure ban sake kallon hotonshi ba sai yau. Na gaban tangaran ɗin wayata dana gaban laptop ɗina tuni na daɗe da cirewa na maye gurbin da hotunan kyawawan nagartattun ƴaƴana, ababen alfahirina, nutsuwata, farin cikin ruhina. Hasken fuskokinsu da adadin yawan ƙaunarsu ne ya dishashen hotunan Asama'u da Mijinyawa a idanuna tuni na danne maiƙon tunanin su da tunano nishaɗinmu da yarana. Ajjiyar zuchiya na sauke na tashi naje na dafa taliyar yara da kifin gwangwami da kuma waken gwangwami, sai baƙin shayin Ahmad mai ƙamshin girfa. Kiran Azgar ne ya shigo ta manhajar WhatApp ɗina. Ai ni na mance shaf yace mun gobe akwai yarinyar da zata zo ta sameni a makaranta zamu gaisa da'ita. Nasan shi da nacin zance tunatar dani yake son yayi. Ɗazu aikine yasha kaina yasa ban yi mishi tambayoyiba akan ita yarinyar. Azgar bana hana ka kiran dare ba shine ka kirani ko. Nasan akan yarinyar da kace zamu haɗu a makaranta ta gaisheni ne, kai da kake da nacin zance ko? " Ɗan murmushin samartaka yayi mun yace. "Ummi har da shi ɗin. Amman rubutun da kika yi a Facebook ne naga anata muhawara akai anata zaginki, shine duk zuchiyata ta tsinke. Ammi mutane basa ganewa, kuma suna da saurin zagi. Abokinane ma yace in duba yaga anata muhawara, kuma anata yaɗa rubutun zuwa groups daban_ daban na mata" Ƴar guntuwar dariya nayi mishi kana nace mishi. Kada ka damu da duk abinda mutane zasu ce a kanka, muddin kana son kaci gaba a rayuwa, kasan domin Allah kake yi, Iyakar wannan yaɗawar kaɗai ya isa ɗaga darajata dana sunana Azgar. Matakin duk nasara, ƙalubale da cin karo da abubbuwa marasa daɗine. Kasan adadin bulogas da suka dena yaɗa abubuwan alkhairi sabida wannan gutsiri tsomar kuwa? Ni bana duba abinda zasu ce kaima kama dena damuwa nasha faɗa maka, ni bani da matsala da hakan. Sai maganar yarinyar menene alaƙarku, sannan wanene tsanin haɗuwar taku? " Ajjiyar zuchiya ya sauke jikinshi duk yayi sanyi saida na ƙarfafashi. Azgar yana jin zafi gaya in yaga ana zagin rubutuna sosai. Su masu zagin, basa duba wanda suke zagin cewar suna da haular da suke son su, kuma basason abinda zai taɓaka. Sun san ni uwace tunda har yarana sun sani da damansu, amman basa duba darajar ƴaƴana su ɗaga mun ƙafa dole sai sun yi zagi, banda masu cewa suna sona. "Ni bazan sake bibiyar shafin naki ba zuchiyata zata iya bugawa watarana Ammi" Allah yasa hakan shine mafi alkhairi. Amman nasihata shine kai namijine ka zama mai juriya da wuyan ɗauke dukkan matsala, ka fiye sanyi da tsoro Azgar ba'a son namiji haka. Da wannan dalilin yasa dole ma in ma Akarami magana da ka gama jami'a a sakaka a aikin soja. Nafi sha'awar namiji jarumi mai zuchiyar dake da jumurin ɗaukar ko wanne yamutsu. Faɗa mun ita yarinyar fa?" "Ammi dama a Facebook muka haɗu da'ita zai kai wata shida haka. Ni na roƙi lambarta ta bani muna gaisawa sama_sama. Shine take faɗamun ai tana Landan tana karatun digiri a jami'arku. To shine nima na faɗa mata mahaifiyata tana mastas tare da jami'ar, kina aiki a Bbc Landan, to itace ta buƙaci tana son ta ganki ku gaisa tunda ni sai dai a hoto ta sanni na santa" Idanuna na lumshe kawai tare da girgiza kai Azgar kenan. Toh shikenan zamu haɗu da'ita ta sameni a ɗakin karatu nasan inta ganni zata ganeni shikenan ko?" "Tana da hotonki ma har da na Abba, da Sabira" Toh shikenan sai goben ka kula dai banda yawan magana da mata, sannan banda maganar da bata dace da addini da tarbiyya ba. Ka riƙe girmanka da mutuncin iyayenka, ka kula da kanka ka kula da ƴar uwarka har zuwa sanda Allah zai dawo dani" "Ammi" Kada kace komai ka adana wannan tambayar har sai na dawo najeriya kamar yaune shekara ai kamar kwanane" Nasan tambayar ɗaya ce inna dawo gidan Abbansu zan koma, shine tambayar da suke matsa mun da'ita shi da Ƴar uwarshi. Ni kuma bana son raba musu hankalinsu. Duk da na fahimci kamar basason in koma gidan Abbansu. Amman dole zuchiyarsu zata yi ƙunci ko babu komai uba ubane, kana akwai shaƙuwa mai yawan gaske a tsakankanin mijinyawa da yaranshi sosai, har nakan rasa gane cikin mu biyu dawa suka fi shaƙuwane su suka barma kansu sani kawai, amman shi Mijinyawa yace Azgar yafi sona sama dashi. Karatu nayi sosai dan bana wasa da dukkan abinda na sanya a gabana. Washegari bayan mun fito daga lekca muna zaune a ɗakin karatu muna hutawa dan yau wuni cur zamu yi a makaranta. Bamu da wajen zuwa ni da Shamsiyya sai nan wajen kasancewar itama mayyar son karatuce gata guruwace sosai kamata. Mun sake haɗuwa da wasu ƴan najeriya mata biyu Nabila da Nafisa. Amman mazauna landanne a yanzu aiki ya kawo mazajensu shine sukai amfani da damarsu wajen ƙara karatu sai dai su digiri suke gwagwarmayar kammalawa, amman a shekaru zamu yi sa'anni da juna. Son karatunsu ya jone mu waje ɗaya duk da a wata ƙasar in ka haɗu da ƴan ƙasarku ko masu jin yarenka sai kaji kamar ka suma dan daɗi. Sau uku muna ziyartarsu su kam sun ziyarcemu yafi a ƙirga muna mutumci sosai harda mazajen nasu, sabida kusan su suke yawan mayar damu gida duk ranakun da muke shigowa makarantar. Dankali da ƙwan da Nafisa ta kawo mana muke ci muna labarin wani littafin turanci da yadda jarumar take jan zarenta a wajen mijinta. Muka ji sallama da wata matashiyar sassauƙar murya a bayanmu. Nina soma waigowa kasancewar nasan zanyi baƙuwa. Tana saye da abaya irin ta zamani ta yane kanta da mayafin abayar a mutumce dai sosai. Kece baƙuwar Azgar ko? " Sai tayi murmushi kawai tare da ɗan risinawa ta gaishemu da girmamawa. "Nafisa dama kinsan Hindu Nagoɗi ne? " Cewar Nafisa ƙawarmu. Kin santa ne, kaddai itace Nafisan da kike kira da takwararki _takwararki tsarar zamanki sit meit?" Nafisa tayi dariya tace. "Itace fa gata da ƙoƙari gaskiya tana taimaka mun sosai akan karatu." Kai na kaɗa nace. Duk guruntakarkinnan Nafi..?" Muka ɗanyi dariyar mu ta wayayyun mata ƴan boko. Hannun Nafisa na jawo ta zauna kusa dani daf har muna jin ƙamshin junanmu. Azgar yaronane ya haɗani da Nafi, shi ya turota ma.
Chapter 71 · 0% Book details