← Book details Tsuron Tsirin Tsandauri Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 77

Sashe 18

Tsuron Tsirin Tsandauri Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Nayi bincike sosai a cikin wayar ko zanga tana mu'amala da wani, irin mu'amalar da take yi da Mijinyawa. Amman bangani ba, sai dai saurayi ɗaya da suke ɗan soyayyarsu soyayya mai tsabta babu kalaman batsa sam a hirarrakin nasu. mayar mata da wayarta nayi jikin caji har lokacin suna ɓarayin uwatale, Mijinyawa babu mamaki yana masallaci dan anata kiraye_kirayen sallah a lokacin. Sallah nayi na haye gado na kwanta kamar gawa, kaina fa ku gane a kulle yake har zuwa lokacin ina canki cankar matakin da zan ɗauka akansu ne mai mugun zafin da sai nadama gami da dakace ma basu san junansu ba. Sannan bani da garaje nafi son bin komai daki_daki domun bana son kalmar faɗuwa, sai dai nasara. Yawan garaje nasa yawan faɗuwa. Bin komai a kan tsari tare da ba ƙwaƙwalwa da zuchiya damar gudanar da tunani mai kyau yana sawa a fidda sakamako duka ɗauka. Dukkan abinda zanyi tunanina bai gushe ba, ina jin kunyar yaranmu suji irin wannan ɗumasariyar da ubansu ya aikata, kuma ace musu da Asama'un da suka ɗauketa tamkar jininsu babu bambanci tako ta ina. Ana idar da sallah yara suka dawo sukaita murɗa ƙofata a rufe ina daga kwance na tambayi waye. Munafukar itace tace. "Mune Ammi? " Lafiya" Na tambaya dan ita da sake shigowa ɗakina har abada wallahi. "Dama zamu gaisheki ne" Ji nayi kamar in lailayo ashariya in narka musu dukkansu ma. Kuje a kwance nake bazan taso ba bana son hayaniya" Ya suka ƙare oho sai na jiyo muryar mijinyawa a dokin ƙofa yana kiran sunana. Da ƙyar na tashi cikin jarumta na buɗe mishi ƙofar ya shigo. Saida ya zauna yace. "Naga sai rufe ƙofar kike yi yarannan zasu kawo mana abincinmu ko kinci naki ne? Miƙewa nayi tare da cewa. Banci ba, bari in karɓo da kaina yaran sun kai minzilin da in kana ɗaki tare dani bai kamata su riƙa shigowa ba" Har nakai dokin ƙofa yace dani. "Waɗannan kuci_kucin cakuri cicin yaran? " Kusan a hasale na juyo nace Su fa" Nayi ficewata da ƙarfina a jikina. Tiran abincin na gani a hannun Asama'u tana rawar kan kawowa cak nasa hannu na zare na juya Azgar na saman Daining shi da Sabira suna cin abinci suna hira kallonsu banyi ba dan ji nake kamar in cinnama gidan wuta duk mu ƙone baki ɗaya. Sai dai kash bazan yi hakan ba sam. Shiru na shiga ko sallama na kasa yi na dire abincin a kan gado. In zuba maka ne? " Ƙur ya bini da idanunshi jikinshi duk a mace. Hannayena ya kamo nayi sauri na fisge tsoro ya kuma shigarshi da irin ƙarfin da yaga na saka yayi tunanin bani kaɗai bace. A ɗabi'ar ɗan Adam yana samun ƙarfi in yana cikin matsanancin ɓacin rai musamman ma in shine da gaskiya. Murya ba ƙarfi yace. "Tutar so wani abun ko dai ya faru ne a lokacin ina kwance a asibiti? Me ka gani? Na tambaya da murya sassauƙa harda murmushi. " Naga tunda kika dawo kika canja ba kamar yadda na sanki ba a satikan baya ba. Nasan baki fiye jituwa dasu Yaya Jamila ba nasan kuma dole ko a lafazi zata cutar mun dake. Amman kiyi haƙuri in akan nama da kifi da suka ɓarnatar miki ne nasa an kawo kifi da nama bayan tafiyarki. In akwai matsala ki faɗamun dan Allah sabida in samu nutsuwa" Murmushin baƙin ciki da takaici nayi, har Allah ya'isa saida na jawo a zuchiyata. Babu fa komai gajiyar tafiya cakuɗe da gajiyar asibiti ne kawai, sai ciwon kai da nake cikinshi dai" "Na fahimci kamar mutanenki ne suke son su sake dawowa kinsan basu fiye alƙawari ba. Amman babu komai zan koma wajen malam da kaina gobe zan rarrafa inje in karɓo miki rubutu' Allah ya nuna mana goben." Abincin na zuba mishi, na haɗa shayi da biredi nasha da naji ban ƙoshi ba na saka Azgar ya dafo mun Indommi naci na ƙoshi abuna, to kashe kaina zanyi in ƙi cin abinci sabida Mijinyawa gona_gonan mazinaci, mayaudari, mai budurwar zuchiya, wanda bai gode Allah bisa ni'imar da Allah yayi mishi ya tsaya a iyakar halalinshi ni ba. Ya ɓige da aikin ashsha da yarinya ƴar cikinshi, kuma yake kwashe mun albarka a gabanta, ya bata ƙofa itama ta zauna a tabarmar rashin darajar daya shinfiɗa mata a kaina. Washegari kuwa ina dawowa daga aiki naga rubutu da hayaƙi da saƙe_saƙi ya karɓomun. Haka lamura suka ci gaba da tafiya wasa_wasa dai har Mijinyawa ya koma bakin aikinshi, ni kuma ina dako, da sanya idanuna a duk motsinsu na cikin gida fa amman. Ni ke saukeshi a wajen aiki in wuce wajen nawa aikin nima. Ya nemi hakkin auratayya na nuna mishi bana jin daɗin jikina sai ya ƙyaleni tunda yaje wajen malam ya haɗo mishi magangunan makarai ya kawo mun, saina fake da wannan naita guje mishi. Shi da Asama'u suka ci gaba da iskancinsu ina sane da duk motsinsu ina kallonsu sosai. Kwatsam rannan na dawo aiki na tarar Nanno tazo tana ɓarayin Uwatale dama nan take sauka in dai tazo. Ina ajjiye jakata na nufi ɓarayin na Uwatale matan su Ado duk suna ciki. Ina shiga Nanno ta rage fara'arta ɗan yaƙe dana saba yi mata albarkacin ɗanta da jikokinta bata samu ba ina gaisheta na miƙe sai cewa tayi. "Dawo zauna" Na dawo na zauna sai tace. "Mijinyawa ya faɗa miki Asama'u zata koma hannuna?" Sai naji mamaki amman sai nace. A.a bai faɗa mini ba babu mamaki ya mance" "To gobe zamu wuce ni da ita riƙonta zai dawo hannuna da makarantarta da komai" To Ubangiji Allah yasa hakan shine mafi alkhairi" "To ameen shikenan jeki" Miƙewa nayi na fice. Karo muka ci da Mijinyawa da mijinyawa Babba suna shigowa zasu je wajen Nanno. Gaisawa muka yi na shige ko duban mijinyawa banyi ba. A falo na zauna cikin su Azgar da Sabira, Asama'u kuma tana ciki. Ina asama'u take?" "Tana ɗaki tana haɗa kaya Ammi wai gobe zasu tafi jama'are da Nanno" E hakane gobe zasu tafi" Azgar yace. "Bamu ji daɗi ba wallahi to Ammi acan zata ci gaba da karatun nata? Ni dai da Nanno ta bari inta gama karatun ta koma, jama'are ƙauyene sosai Ammi dan Allah kisa baki komawar tata tamkar kashe mata rayuwa za'ayi, mun saba sosai babu wanda yake tunanin Asama'u ba ƴarki bace me yasa za'a ɗauke miki ita? " Sabira ta amshe. "Dan Allah Ammi" Murmushi nayi musu nayi farin cikin tafiyarta, amman akwai abinda nake son sani meye dalilin tafiyar tata, tuba Mijinyawa yayi yake son nisantarta ko kuma, wani shirin ake ƙullawa, ko kuma menene?" Sai kawai ma na share nace da yarana. Kuyi haƙuri Nanno ba yadda zata yi ba tunda ta riga tace to dole ayi mata biyayya" Shiru suka yi, ina zaune harta fito idanunta yayi luɓu_ luɓu tazo ta zube a gabana sai kuka. Yaran duk hankalinsu ya tashi. Ƙur ni kuma nayi ina kallonta ina tausayin halin data jefa rayuwarta a ciki, wannan kukan dai na rabuwa da Mijinyawane. Ina son Asama'u sosai kuma tausayintane yasa nake sonta, na bata pawa sosai a gidana ƙila hakanne yasa ta samu waje, ni Allah shine shaidata dominshi nayi kuma Amana aka bani na saka hannu na karɓa. Ana cikin haka sai gashi ya shigo da sallamarshi ya nemi waje ya zauna. "Ita kuma wannan kukan rabuwarne aka soma? Kiyi haƙuri ai zaki dinga zuwa mana hutu kinji ko, nima kuma zan dinga zuwa wajenki, sannan duk abinda kike so ki bugo waya ki faɗama Amminki zata sanar mini, ko ki faɗama mutuminku Azgar." Asama'u kiyi shiru. Ki kuma riƙe mutuncinki ki tsayu akan tarbiyyar da Abbanku ya baku dama wanda nima na baku, ke macece dole watarana dama za'a rabu, da kin gama jami'a aurenki zaki yi. To sai kiyi haƙuri ki rungumi sauyin da kika samu" Ina gama magana na ƙule ciki na barsu sai rarrashinta suke yi yadda kuka san wacce jaki ya kada. Sai da akayi isha muna zaune muna cin abinci Mijinyawa ya kirani a tsanake na dubeshi ba tare dana amsa mishi ba. "Nifa na kasa gane kanki sam Tutar so nafa san halinki ki fito ki faɗamun kawai abinda nayi miki da kika ƙaurace ma turakata da abubbuwa da yawa da kika yi watsi dasu a cikin gidannan rayuwar gidan ta soma rashin daɗi, na damu da yawa duk sanda na tambayeki sai kice babu komai, amman kuma akwai wani abun da kike ɓoyewa Tutar so nayi miki sanin da babu mahalukin da yayi miki irinshi ki faɗamun menene matsalar na roƙeki da girman Allah" Mijinyawa kenan, in da akwai zan faɗa maka ai. Kuma kasan ba haka nake fishi ba tunda babu abinda bana yi maka face kwanciyar aure da muka dena shima kuma lalurace ni kaɗai nasan abinda ke damuna fa" "Aa ba mu'amalar aure kaɗai aka dena ba harda hira, da cefane da kike yi, a da in abu ya ƙare bakya tambayata sai dai ki siya har sai nayo wani cefanen in sabon wata ya shiga, wani sa'in ni dake gogoriyo muke yi wajen cefanen gidannan. Sannan da ko da al'ada kike yi kinsan hanyoyin gamsar dani tunda ke kinsan halittata. Ga motarki kina mun rowarta harma na yi zuchiya na dena cewa ki bani ko a jikinki, na fa soma gajiya kina neman ki sukurkutamun tunanina, wannan abun ya soma taɓa aikina Tutar so, in akwai abinda nayi miki ki sanar dani in baki haƙuri mu dawo da farin cikin gidanmu. Gidan yaushe rahama da haske zai sauka sarauniyar gidan tana nuna halin ko in kula" Ummmm babu komai maganar cefane da kake yi ai ratayayyen hakkinka ne ni taimakawa nake yi, a yanzu bani da halin taimakawanne sannan batun hira da kake yi me ka taɓa cewa ban tanka maka ba" A daren ranar faɗa muka yi ƙaƙas, shi ala tilas yayi fishi dani, ina ɗaga mishi hankali da sabon salon ko in kula da nake nunawa gabaki ɗaya na canja. Kuma ina fara'a muna hira, kwanciyar aure da wasa da dariya na dena kamar yadda ada muke yi, sai ya dakeni, in dakeshi wallahi ko mu kama kokawar soyayya a ɗaki haka
Chapter 18 · 0% Book details