Sashe 11
Tsuron Tsirin Tsandauri Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
zo mun da batun aure, ko kuma ince danginshi zasu dinga yar mun da magana a tsakar gida" Haƙiƙa Sunusi yayi mata zalunci mai girman gaske. Mace ta gama bautama miji amman inya tashi ɗiban albarka a kanta yake nuna ƙarewa. Ni ɗin meye banayi a gidana, meye banyi ma Mijinyawa ba, wacce iriyar sadaukarwace banyi mishi bane a rayuwarmu da zai sakamun da raba tsaraicinshi harda mugayen maganganu masu ciwo a kaina. Ajjiyar zuchiya na sauke kana nayi murmushi nace. A bakin facaloli kika ji labarin kenan bai faɗa miki komai ba ke? " "To na isane ya faɗamun Hindu? A bakin fanfo naji suna faɗan irin lefen da yayi ma matar, da ƙyar na kawo kaina wajen aiki. Hindu jiya_jiya na biya kuɗin makarantar yaranmu uku dubu ɗari da hamsin fa hmmm" Wasu sababbin hawaye suka sake zubo mata. Shiru muka yi kowanne cikinmu na ƙunshe da baƙin ciki da takaicin ɗa namiji ɗa namijinma wanda ka sadaukar da komanka domin shi yayi rayuwa mai kyau. Girgiza kai nayi nace. In nice ke idanu zan ɗauka in zuba ma Sunusi kana duk wani tallafi in janyeshi sai wanda nasan zai iya cutar mun da yara, domin bazan ɗaura yarana a kan dogon laifin mahaifinsu in wofantar da lamarinsu ba, sabida akaina ma akwai hakkinsu. Kinga idanu? Basa ci basa sha amman mashine. Saifa kin dena wannan banzan kukan ke da kanki zaki samama kanki ƴanci wallahi bani zanje in miki faɗa a gidanki kamar yadda na saba tare miki faɗa a makaranta ba. Aure kuma yaje yayi kowa da halinta zata zauna in kika janye tallafi ita kanta amarya saita ɗanɗano kuɗarta kisa farin cikin ki dana yaranki saman nashi, ki ba banza ajiyarshi. Kada ki sake kuka har facaloli su gane rauninki kada kiba maƙiya ƙofar da zasu ga wallenki. Ke da kanki zaki yi yaƙi ki kwaci kanki Luba. Kina aikin ki daidai gwargwado kina samun albashinki kada ki bari ciwo ya kamaki kima ɗiyayonki asarar lafiyarki wannan shine. Ki ɗauki ido ki zuba zaki ga ƙwal uwar dakane." "Nifa da cewa nayi zanje in faɗama uwarshi abinda ake ciki" Baki na buɗe nace. Laa ashe baki san bayan ɗanta zata bi ba? Wallahi da kinje saita faɗa miki cutar da sai tayi ajalinki ko tai miki sanadin ciwo. Dashi da dangin nashi watsasu a kwandon shara. Nifa in kamun saina yi maka ko da daga baya zamu sasanta sai dai mu tashi da ɗaya da ɗaya (1_1) Matar Aure ba fa baiwa bace Aure bafa Bauta bane sunnahce ta ma'aiki Arrasul S.A.W, inda zasu yi koyi da shugaban soyayya na duk duniya Arrasul s.a.w da duniya ta zauna lafiya." Na daɗe ina tausar zuchiyarta duk da nima tawa zuchiyar cikin miki take ɗanye. Lokacin barina aiki nayi na ɗauki haramar fita. Ogane ya kirani na shiga ofishinshi na sameshi. "Hindu sannu da ƙoƙari fa a gaskiya muna jin daɗin aiki dake kina da jajircewa da gogewar aiki sosai. Kuma ina bibiyar aikin ki musamman a shafinki na Facebook duk da naji yawancin kwament ɗin maza zagine da albatawa tunda a tunaninsu yaƙi kike yi dasu. " Dariya kawai nayi bance komai ba. "Amm akwai semina da za'a gabatar a Abuja Bbc ce ta haɗa seminar, ke da Ibrahim ne zaku wakilcemu ko kuma ke kaɗai ma to sai ki zauna da shirinki in sha Allah." Wani daɗine ya lulluɓeni sosai har fara'ar gaske ta wanzu a fuskata. Nagode sosai oga Ubangiji Allah ya nuna mana babu matsala a shirye nake lokacin kawai zamu jira" Da haka nayi mishi sallama na nufi asibiti. Harna isa ina cike da fara'a da jin daɗi inason halartar irin tarukan ƙarama juna sani sosai sabida yana sake wanke mun kaina tas.kuma inason in ganni ina cuɗanya a cikin manyan mata. Musamman Bbc ai burin duk wata ma'aikaciyar rediyo baya wuce son tayi aiki da Bbc ko DW waɗannan manyan gidajen rediyo suna da girman daraja, ni dai burina in kasance ma'aikaciyar Bbc sashen hausa, ban cire raina ba har yanxu in da rai to da rabo. Kamar kullum Yaya jamila ana zaune anata ciye_ciye. Kullum daga gidanmu ana kawo abinci rana dare, abincin safe kawai nake yi musu in kawo musu kafin in wuce wajen aiki. Mijinyawa yana zaune suna hira da abokinshi Nura na shigo. "Madam kin taso kenan yanzu muke maganarki yana yabawa da ƙoƙarinki sosai." Murmushi nayi tare da cewa. To in banyi mishi ba wazai yi mishi Nura, ai mijinyawa yafi haka a wajena guda ne shi har da rabin mutum. Ranka shi daɗe ya jikin naka, duk da naga jiki da kyau ciwon nata kamewa" Idanu ya lumshe tare da mun murmushin da ada in yamun sai inga kamar nafi uban kowa dace a duniya. A yanzu in yayi mun sai inga kamar ma kuka yake yi tsabar baƙin cikinshi. "Da sauƙi sai cinyarne ya rage kawai har yanzu bana iya takawa, kuma likita yace saina taka sun tabbatar babu wata matsala kafin ya sallamemu, gashi duk na gaji da zaman asibitin. Wayar tawa kin tawo mun da'ita kuwa?" Na tawo da'ita da safe ma mancewa nayi ne shi yasa" Jakata na zuge na bashi wayarshi ya kunna. Sallama Nura yayi mana ya tafi. Yaya Jamila tana ganin fitar Nura ta shigo ta zauna ta shiga janshi da hira. Sabida ita bata so yayi hira ne dani, shi kuma idonshi akan wayarshi har murmushi naga yanayi idanuna ƙur a kanshi ita kuma Yaya Jamila sai zuba take yi, jifa_ jifa yake amsata, yama mance da wata banza a zaune a gabanshi, ni kuma inata nazartarshi. Take na sake shaƙa sai ɗan girgiza ƙafa kawai nake yi amman fa a fuska ba'a gane asalin halin da nake ciki. Zuwa kamar bayan la'asar ina yin sallah nace. Zan wuce ni Allah ya ƙara sauƙi sai kuma gobe" Idanshi na kan waya ya ɗago yace. "To shikenan Tutar so nagode da ɗawainiya ki gaishe da yaran" Sallama nayi ma Yaya Jamila na fita. Ina tuƙi ina mamakin Mijunyawa sai dai inyi murmushi kawai abun ma ya dena bani mamaki. Gaga_gaga har tafiyarmu zuwa semina ta matso gobe ne tafiyar, nazo asibiti bayan na taso aiki sai lokacin a gaban Yaya Jamila da bata iya bamu waje ba nace. Gobe zani Abuja akwai semina da zan halarta wanda Bbc ta haɗa, kuma an zaɓeni a matsayin wacce zata wakilci gidan rediyonmu. To gobe da sassafe zamu kama hanya" "Ba shakka, sabida rashin imani mijinki na kwance baida lafiya amman aikin ki ne a gabanki har tafiya ma zaki yi. Kinfi sha'awar ki dinga ganin kanki a cikin maza kuna cuɗanya" Mijinyawa Babba ne yace. "Yaya jamila Hindu tana ƙoƙari duk ɗawainiyar asibitinnan ita ke yi da ajjihunta. Kuma aikinta yana da mahimmanci, Mijinyawa ƙarami jiki da sauƙi ƙafarma ɗazu ya takata." Harararshi tayi, ni dai abinda mijinyawa zaice nake jira. "Babu damuwa Yaya Jamila taje na yarje mata" "Kai dai shanyayyene. Ya zaka bar mace ta dinga takaka yadda taso, kana kwance a gadon asibiti tana zuwa aiki bai isheta ba har sai ta tafi semina ke Hindu zuwa Seminar to dole ne. Wai me yasa ƴan boko basu fiye girmama aure bane su, ko dan kinga an barki a gidan ke kaɗai shi yasa kike yadda kike so ko?" Allah ya huci zuchiyarki Yaya jamila. Ni kam saida safenku." Na miƙe nayi juyawata ina jinjina lamarin ƙiyayyar wannan mata a gareni, ko uwa na kashe mata sai haka. Ina zuwa gida na zube a falo Sabira ce kaɗai a gidan tana zaune tana karatunta. "Ammi yau kin dawo da wuri ya jikin Abba? " Jiki da sauƙi. E nadawo sabida gobe zanje Abuja sassafe, ku kuma zaku je gidan Baba Sojanmu ku zauna kwana biyu kacal zanyi." Shigowar su Azgar yayi daidai da shigowar kiran Baba Sojanmu cikin wayata. "Hinduwa Duwaf nima in ɗana to yaya jikin shi mijnyawan yana dai samun sauƙi ko? " Da sauƙi sosai yauma ya taka ƙafar tashi. Ni gobe ma zanje Semina ne Abuja Na Bbc hausa" "To allah ya taimaka haka nake so ku zama jajirtattu kuma ku riƙe aikinku kada ku zamema mazajenku da yaranku nauyi. Kunga mahaifiyarku dai malamar boko ce har matakin princifal ga kasuwanci da take yi, kafin ta tambayeni kuɗi sau ɗaya tayi da kanta sau goma. Kuma kunga bambancinta da ragowar abokan zamanta. Ya maganar mastas ɗinki ai ya kamata kiyi Hinduwa ko? Kada kisa ƙyuya ke ba yaran goye ba. Saratu da goyon ɗiyarta ta soma mastar ba gashi ta gama ba, ki dai yi tunani mijinki dai ba hanaki zaiyi ba" To shikenan Baba Sojanmu in sha Allah shekara mai zuwa dani za'a soma nima abun yana raina kuma inaso shi dai Mijinyawa bashi da matsala da hakan. Baba sojanmu gobe su Azgar zasu tawo gida saina dawo sa dawo" "To ai babu komai su zo irinsu sunfi ashirin a gidan ai. Allah ya kaimu goben Allah ya tsare miki hanya, amman ki dawo da tunaninki lallai kan mastas ɗinki Hinduwa" Na amsa mishi da amin tare da yi mishi godiya. "Ammi kin dawo, naji kina zaki yi tafiya? " E Azgar tafiyace ta taso mun daga ofishinmu kuma ni aka zaɓa amman kwana biyu zanyi in dawo. Zaku je can ku zauna Na'ibawa bazan barku a gida ɗakina a buɗe ba Yaya jamila nanan" Asama'u tace. "Ko yau Ammi saida tai ta zagin Azgar wallahi kuma bai mata komai ba" Hmm to dama me zaiyi mata shi da uwashi, kuyi ta haƙuri watarana ma ba zasu ganku ba. Kuma kuci gaba da basu girmansu sabida duk tsiya sune bangonku. Bari in shiga ciki in watsa ruwa in fito in mana girki yau taliyar hausa nake son ci ta manja mai kifi" Nan na tafi na barsu sunata cece kucensu nayo wanka na zauna a gaban mudubi ina shafe jikina da kulaccham. Saina tsinci kaina da miƙewa tsaye tare da cire tawul ɗin jikina na ƙurama zatina idanu ina so inga inda nake da wata tawayar da har Mijinyawa zai kirani da tsohuwa, karuwarshi kuma tace dani bagidajiya, banyi tunanin akwai abinda budurwa zata nuna mun ba daya wuce sabon budurci ba. Ƙoƙarin gyaran jikina da nake yi ba duk kai ba a