← Book details Tsuron Tsirin Tsandauri Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 68 OF 77

Sashe 68

Tsuron Tsirin Tsandauri Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

rayuwata. Yaranki nake so, in kuma Allah ya ƙaddara ba zamu ga ƙwanmu ba shikenan ba dole bane haihuwa ba, auren kanshi ba dole matsawar mutum yasan zai iya riƙe kanshi wallahi Hindu ina girmamaki ina girmama lamarinki. Tunda mukai aure komai nawa ya ƙare sau uku kina bani jari yana lalacewa har gobe a ƙarƙashin inuwarki nake. Ni har kunya nake ji irin yadda dangina suka ɗaukeki, da irin nuna gazawata ta kasa riƙeki in kula da komanki, kin tattarw komai na ɗauke dukkan ɗawainiyar gidanmu. Hindu in na samu kuɗi zaki ji daɗi sosai gabaki ɗaya kuɗin zan dinga jibge miki kiyi yadda kike so da shi ni kaina sai dai in karɓi na kashewa a wajenki" Mirginowa nayi na rufe bakinshi da nawa tuni yai ma laɓɓana riƙon alawar yara. A wannan daren mun wankema junanmu duk wani tsatsa da dattin dake zukatanmu. Take naji dukkan wuya da tsangwama ina tare da mijinyawa babu gudu babu ja da baya. Abinda na ƙunshe a raina kuma na ɗan ƙara lokaci kafin in fitar mishi dashi zan sake gayama Allah tukunna, dan lamarin da girma yake ni kaina ina jinjina lamarin. Washegari sassafe na gama komai har girkin rana na gama mana kasancewar ranar monday ne. Muna gama karyawa muka fito tare zuwa gaishe da Nanno. Muka shiga taga muna fara'a muna cikin godiyar Allah. Yana daga cikin abinda ke damun dangin Mijinyawa su kullum burinsu su ganni a ƙasa, ni kuma duk girman abinda ya tunkaroni sai in nuna musu ko oho na gwammaci in kwana a cikin tunani. "Kaje zance wajen Kandala kuwa? Kasan fa wata huɗu kaɗai kuke dashi da zaran watannin sun cika to babu makawa za'ayi auren ita kuma zaku rabu baku dai mance ba ko? " Bamu manta ba Nanno muna nan muna lissafawa duk abinda Allah yayi mai kyau ne rayuwa shirin Allah ne" Na ƙarashe ina murmushi tamkar wacce akaima bushara da gidan Aljannah. Ita na bari da haɗe rai tamkar hadari. Nan mukai mata sallama muka fice. Muna tafe muna tattauna matsalolinmu har muka iso bakin makaranta. To zan shiga kaga yara suna asambili sai kazo ɗaukata ko? " "To shikenan Allah ya amintar mun dake Tutar so sai na zo ƙarfe ɗaya a nan zatai mun kamar yadda aka saba." Da haka mukai sallama na shiga ciki na tsaya a saman baranda kamar sauran malaman sai da aka gama asambili malama Tani take shaidamun shugaban makaranta firinsifal yana nemana a ofishinshi. A hankali nake tafiya har zuwa ofishin firinsifal na shiga da sallamata ya nuna mun wajen zama na zauna. "Malama Hindu abinda yasa na kirawoki shine akwai malamin mu daya samu sauyin wajen aiki yana ɗaukar ƴan sakandare aji biyu. A bisa ƙoƙarin ki da gogewarki wajen iya turanci dama koyarwar shine muka ga ke kika fi cancanta ki maye wannan gurbin na malamin daya tafi, akwai wata malama sai mu kirata ta maye naki gurbin kinga za'a samu ƙarin albashi kuma munsam zaki iya" Nayi farin ciki sosai take na amince da tayin da akayi mun harma na soma ɗaukar ƴan aji biyu a ranar kuma Alhamdullillahi karatu ya tafi yadda ake so kuma na samu haɗin kan yaran gaya. Saida muka fito tara ne muna zaune a rumfar makaranta muna hirarmu da malama Tani, yara ƴan makaranta na ta harkokinsu a haka har muka koma aji. Ana tashi a makaranta na hango mijinyawa a zaune tare da maigadi suna zantawa harna iso wajen, ya karɓe jakata dake cike da littattafan ƴan makaranta muka wuce. Tun a hanya na faɗa mishi alkhairin daya samemu mukaita murna da jin daɗi. Sallar azahar muka yi nan muka zauna zaman cin abinci shinkafa ce da wake jalof harda bushasshen kifi. "Shinkafarnan tayi daɗi wallahi zata kaimu har dare ne mu ci ba sai kinyi girkin dare ba ki huta kema? " Dariya nayi mishi nace. Ai iyakar abincin da muke dashi kenan na girka har safe ma zamu samu amman bamu da ƙwayar hatsi a Kitchen komai yayi ƙarƙaf" Sai muka yi shiru sabida wata dai yau yayi rabi, akwai sauran kwanaki goma sha kafin ayi albashi. Mijinyawa ya kamata mu sake tsara yadda zamu dinga cefanenmu yadda kuɗin da muke samu zai dinga isarmu har zuwa wani watan. Wahalar tana yawa ace komai ya ƙare a rabin wata, yanzu shikenan mun shiga jula jula kenan fa. Kai ya kake ganin zamu yi?" "To Tutar so ke a tunaninki me kike ganin za'ayi kece mace kuma ke kike girkinnan ko ba gaskiya ba, ya za'ayi sai yadda kika ce" Murmushi kawai nayi mishi nace. Ina ganin garin tuwo da fulawa kaɗai zamu iya siya a kayan hatsi kenan Ragowar kuɗin sai mu sai bushasshen kayan miya da su maggi da sauran abinda ya dace. Tuwo da daddare sai muci ɗumamenshi da safe, da rana muci taliyar murji ko da mai da yaji ko jalof, sabida mu guje ma yinwa da ƙarewar abinci zuwa lokacin da Allah zai yanke mana" A haka muka tsayar da matsaya a daddafe muka ƙarashe ƙarshen wata talata kuwa muka wuce kasuwar Galdimari muka siyo duk abinda ya dace mijinyawa da daddare ya gama murje mana taliyarnan tsab washegari da tasha na zuba a robar da muke adana kayan hatsinmu shine rayuwar tayi mana sauƙi abinci yake kaimu wata cur. Uwatale kuwa kullum da nama ko kifi take miyarta sabida Allah ya buɗa ma mijinyawa Babba Kano yake aiki ya samu Ubanggida a kasuwa kuma yana samun alkhairi harma muke jin raɗe_raɗin yana gini acan yana so nan da wani lokacin in ya gama zai ɗauke iyalanshi zuwa Kano sabida yana so su samu ilimi mai zurfi sosai. Duk sanda zai zo yana tawowa da kayayyakin alatu amman bamu fiye samu ba kasancewar Nanno ke raba komai ba ko wanne zuwa bane ma in yayi muke samun tsarabarshi ba. Ya na dai bama ɗan uwan nashi kuɗi to wannan dai muna samu. Uwatale ta sake yin kyau ta samu sukuni har kayan ɗakinta mijinyawa babba ya sake mata, cikine ƙaramima a jikinta sai feleƙe take yi. Damma Allah yasa ina da tattalin sutura da tuni suturuna sun lalace. Amman sunanan gadagau ko yau na saka wasu kayan kamar sababbi haka suke zama amfanin siyan kaya masu tsada yana da yawan gaske. Takalma kaɗai nake fatararsu guda biyu kaɗai gareni masu kyau na fita unguwa haka na zuwa makaranta guda biyu, suma inata manejinsu tunda mukai aure in banda ankon gidanmu da nayi ban sake yin ɗinki ba, ta kai ake bata kaya ba. Gaga_gaga al'amura suka ci gaba da shurawa wasa_wasa lokaci har ya kusan motsowa saura wata ɗaya tak wa'adin da Nanno ta gindaya mana ya cika. Mijinyawa duk ya rame ya fice a hayyacinshi ni dai tuni na sadudu na zubama sarautar Allah idanu duk abinda yayi dani mai kyau ne babu tsimi bare wata dabara. Kuma na roƙeshi ya zaɓamun abinda yake mafi alkhairi Da daddare bayan mun gama cin tuwo nace. Mijinyawa kusan watanni uku kenan inason mu tattauna wata muhimmiyar magana amman nauyinta ne yake hanani furtawa sai nayi kamar na haƙura sai in fasa." Hannayena ya riƙe yana matsawa yana kallon idanuna, nima idanunshi nake kallo tunda nake ban taɓa ganin namijin da kwalli ke zama a idanunshi ya zamemai ado kamar mijinyawa ba. "Me kike son faɗa mun har tsawon wata uku Tutar so? To koma menene ki faɗa zanyi miki in dai zai sama miki nutsuwa da farin ciki" Shiru nayi kaina na kallon kafet ɗin ɗakin namu. So nake mu ɗauko yaro a gidan renon yara mu riƙe a matsayin nina haifa mijinyawa ta wannan ne kaɗai zamu tsallake sharaɗin Nanno kuma nagaji da gorinnan da akeyi mun mijinyawa" Shiru muka yi kusan na minti talatin yayi tsam yana kallona yama rasa me zaice dani. Miƙewa yayi ya fita tsakar gida. Sai gaji da kasko cike da rushi ya ajjiye a gabana ya bankamun hayaƙin makarai tare da kama kaina yana ta mun tofi. Sama da ƙasa saina kasa cewa uffan sai hawaye ne suka cika tab a guraben idanuna, amman basu zubo ba. Lokaci guda fuskata ta kumbura tayi suntum. "Dama nasan kune kuka furta wannan maganar ba dai Hindu na ba. Na roƙeku ku barmu muji da abinda ke damunmu dan Allah" Miƙewa tsaye yayi ya miƙar dani ya kaini gado ya kwantar ya kunna mun kaset na karatun Qur'ani a rediyo mai manyan batura tiger. Idanuna na lumshe ina kukan zuchi zuchiyata tamkar zata tarwatse. Shikenan na rasa mijinyawa kenan sai dai ya zama tarihi a rayuwata kenan?" Haka naita tubkewa yana warwarewa da kanshi. Ban sake yima mijinyawa maganar ba sai ana jibi wa'adi ya cika na sake maimaita mishi maganar. "Wai dama da gaske Hindu kece da kanki kika yi wannan maganar ba makaranki ba? Ni na ɗauka mai hankali ba zaiyi irin wannan maganar ba. Taya za'ayi mu mayar da ɗa da ba namu ba ya zama namu kin taɓa ganin anyi hakane? Hindu kada mu yaudari kanmu dan Allah" To shikenan babu damuwa mijinyawa Allah yasa rabuwar tamu shine mafi a'ala" Na juya na koma ɗaki makarantar da banje ba kenan. Ko da ya dawo da yamma ya samu duk na harhaɗe kayayyakin Kitchen ɗina na ɗuresu a manyan buhunhuna suturuna duk nayi wanki sun bushe na jejjerasu a akwati waɗanda nake ji zan kyautar duk na ware su a gefe guda. Wallahi a daren ko abinci bamu nema ba kusan kwana muka yi akan sallaya, haka washegari ma bansan abinda ke cikin ran mijinyawa ba bai bani dama mun yi magana ko da ta ban kwana bace yana riƙe da carbi Yaya Jamila ta shigo babu ko sallama sassafe fa. "Kazo kai da Hindu inji Nanno. Yau wa'adi ya cika alƙawari shima zai cika duk wani aure ribarshi haihuwa ne ba soyayya ba" Juyawa tayi ta fita fuskarta cike da farin ciki da jin daɗi. Murmushi kawai nayi na zari mayafina na dubi mijinyawa nace. Ya kamata muje ko sabida in samu in tafi da wuri kar dare yayi mun a hanya" Idanunshi masu kyau da tozali ya zuba mun sun yo jawur suna ƙoƙarin zubar da ruwan hawaye. "Wai ke ashe da gaske kin shirya rabuwa dani Hindu
Chapter 68 · 0% Book details