← Book details Tsuron Tsirin Tsandauri Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 53 OF 77

Sashe 53

Tsuron Tsirin Tsandauri Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da rana taliya nayi mana jalof na saka mana soyayyen nama, na saka mayafi na miƙa ma Uwatale tana ciki da ƙawayenta na miƙa mata, saida na tsaida sanwar miya na daka daddawa wake, tafarnuwa na zuba. Da rana dai ƙata bazan ci abinci haka kurum da uwalate ba wallahi. Na darenma dama na gani, da bazan ba tunda ko mijinmu ɗaya ba za'ai mana tilas ba. Na zauna kenan zan ci abinci sai Uwatale ta leƙo wai abincin bazai isheta ba tayi baƙi in zuba ma baƙinta. Harna ɗago zan zazzageta saina fasa. Duk iyakar kawar da kan da zanyi bazan yadda a rainani ko a nemi takani ba, ko a keta mun rigar alfarma ba, ba komai ni Hindu zan iya ɗauka ba ni nasan kaina. Kawai sai nai bismillah na soma cin abinci na dan wallahi in nace magana zanyi saina zagi uwarta da ubanta tukunna, kunga kuwa ai akwai rikici in nayi hakan kuma Mijinyawa nake tausayama. Da taga dai bazan kulata ba saita nufi ɓarayin Nanno ni kuwa nayi rantsuwar ko kaɗani gida za'a sa Mijinyawa yayi sai dai yayi amman bazan taɓa ma ƙawayen Uwatale abinci ba wallahi, ai tunda nace bazan yi ba, bafa zanyin ba ne. Nanno haka ta tako ta sameni ina kan cin abinci na hankalina kwance. "Hindu me ya haɗaki da uwatale ne ta kawo mun ƙararki akan abinci nace da somawa da iyawa, ina fatan kinsan matsayin Uwatale a wajena ko? " Babu abinda ya faru nayi abincin na kai mata nata yanzu nima nake cin nawa" Na nuna ni bansan komai ba ma ai. "Amman kina ganin tayi baƙi ai, ya zaki bata abinci a kwano ƙarami?" Banyi tunanin da baƙi za'a dinga girkin ba Nanno. Na zaci ita zata ma baƙinta abinci tunda wajenta suka zo, ni kuma bani da wanda ma zasu zo wajena balle tayi musu. Baƙinta bai kamata su rataya a wuyana ba" Sai tayi shiru tana nazari. Wannan maganar fa da salon ladabi da ɗaure mutum da jijiyoyin jikinshi na haska mata bazan iya soma abinda zai zame mun lalura ba wallahi, duk abinda bazan iya ba, gara tun wuri in haska su san da zamanshi. "Uwatale muje zan san matakin da zan ɗauka akai wannan yarinyar sai anyi maganinta. Idanunta a buɗe yake da yawa. Ji yadda take mun magana kamar mai karanto labarai" Taja Uwatale suka fita na bisu da harara. Kafin magriba na gama tuwona duk na zuzzuba ma waɗanda suka dace har dana gidan su Uwatale da kaina duk na mimmiƙa ma kowa, na Nanno na haɗa da kwanon gidansu Uwatale na kai mata. Namu kuma na jera a falona na ajjiye dukkan abun buƙata na kunna turaren wuta ragowar gaushin kuma na ɗaura ruwan shayi daya tafasa na juye a filas na mayar dana wankan mijinyawa, ni nayi wanka na turare jikina da turaren jiki dan kore ƙaurin hayaƙin girki a jiki haka naga Innarmu take yi, kuma akwai wata doguwar riga ta musamman wanda da'ita take shiga madafi yin girki tana gamawa zata wanketa in ta shiga wanka tana fitowa ta shanya ta turare jikinta da turarenta mai ƙamshi na jiki dan ƙaurin itace yana da ƙarfi in mace batai da gaske ba sai ya riƙe mata jiki sosai. Amman naji jiki hannayena duk sun sage tuwone gari guda na tuƙa babu matayi, babu kowa banma taɓa abinci mai yawan wannan ba. Sai dai ban samu wata matsala ba tunda muna taya su Innarmu girki, da su jajjage, yanka ganye, ɓare maggi da sauransu dai. Ina kan sallaya har akayi sallar isha nayi jigum ina tunanin ƴan gidanmu na jiyo sallamar mijinyawa ya shigo. Da sauri na tafi na tarboshi harda tsarabarshi ta kankana ƙwallo guda, zama yayi ni kuma na juyo mishi ruwan wanka na taimaka mishi yayi wankan da kaina na zura mishi jallabiyarshi muka fito tare. Ina tsaye a Kitchen ina yanko mana kankana su Uwatale suka shigo muka zauna ni dai tare a kwano ɗaya na zuba mana namu abincin Uwatale kuma ta zuba ma mijinta daban itama daban. Sai cewa tayi. "Nayi tunanin ai a faranti ɗaya zamu ci, kamar yadda muka a ɓarayina ai? " Mijinyawa Babba yace. "Ai hakanma yayi Uwatale" Murmushi nayi nace mata. To ai dake shi ba mijina bane, kema Gawata ba mijinki bane babu yadda za'ayi ace muna cin abinci a faranti guda wannan ba musulunci bane sam. Wata al'adace kawai. Amman ke kici da mijinki nima haka shine dacewa" Bata iya cewa komai ba, ai na wuce da tunaninsu na riga na kashe zancan. Ana cin abinci suna ɗan taɓa hirarsu ni da uwatale bama cewa uffan kusan har aka kammala cin abincin. Mijinyawa dai yana kallona tare da sakarmun murmushi nima haka. Wajajen tara suka tafi ni kuma na tattare kayan na kai Kitchen na dawo muka buɗe shafin hira shine yake tambayata yadda muka yi da Nanno na mishi bayani tas tun daga kan girki da abinda ya haɗamu da uwatale. "Sai haƙuri ki ƙara haƙuri komai zai wuce watarana sai labari kusan haka suke yi a gidan waɗanda amman suka haɗa mijine kawai sai su haɗe girki suyi. Mu din so take yi shaƙuwarmu ta ƙaru kawunanku su haɗe sosai shi yasa" Kada ka damu da ba dan ka jiyo ba zancan ma ai bazan yi maka ba. Yanzu gobe da nayi shikenan zan kuma huta na kwana biyu shikena, ai da daɗi sosai " Jawoni yayi ya gyara mun kwanciyata yace. "Daɗina dake ke bakya fishi Allah yayi albarka. Gobe zan gayyaci abokaina kamar mutum biyar muci abinci tare dasu girkin bazaiyi miki yawa ba? Duk da gobe zan kasance a gida na kama miki aikin ma. Kuma inaso zamu fita dasu Mijinyawa Babba zuwa gidan Yaya jamila zuwa bayan isha in mun kammala cin abincin sai gidajen abokai da zamu ɗan zagaya" Allah ya nuna mana goben da rai da lafiya mijinyawa nawa ni kaɗai" Da haka labarin ya canja salo zuwa eh kun gane ai. Washegari da zai fita na bashi kuɗin kaji uku, da kayan miya nace in zai shigo tunda yace azahar nayi zai shigo sai ya kawo mana, sabida babu ko sisi a hannunshi sai yace in yi amfani da na wajen nawa. Shayi da ɗumamen tuwo na miƙa ma su Uwatale na safe, da rana na dafa jalof ɗin shinkafa da wake ta manja na ajjiye mana namu ni da mijinyawa na ba uwatale nata. Ina zaune ina wanke_wanke mijinyawa ya shigo. Wajen wanke_wanken ya iso ya ajjiye cefanan a gefe, nayi mishi sannu da zuwa ya amsa harda shafar fuskata. "Bari in kwaɓe in zo muyi girkin ki saka sakata a ƙofar gidan" Sakata na saka na dawo sai da muka ci abinci kana na gyara kayan miya ina jajjage yana wankemun kajin daya siyo yasa an fige an yanka daga can. Muna aikinmu muna hirarmu harda dariya abin sha'awa. Sai da la'asar tayi ya tafi masallaci yana dawowa muka ci gaba da aikinmu kafin magriba mun gama komai shi ya shimfiɗa babbar tabarma muka jera kulolin abincin da cokula da kwanuka dukka dai shinkafa da miyar kaji nayi musu ana idar da magriba suka shigo ni kuma ina ɗaki dan na zuba abincin uwatale na miƙa mata nima ina cin nawa a ɗaki, yau dai ba zaman cin abinci. Saida suka gama na fito muka gaisa sukayi godiya tare da yi mun sallama. "Tutar so ki shirya da mun dawo zamu tafi" Kafin ya dawo na shirya muka rankaya gidan Yaya jamila mun kuwa jima a can, daga nan muka ɗan zagaye abokansu gida na ƙarshe gidan Qasimu ne aka kaini wajen Baraka na ganeta sau biyu tana rako maƙota zuwa ganin ɗaki. Yaya Jamila mutuniyarku tai ta habaici da turo maganganu iri_ iri, ni kuwa Hindu nayi biris. Gaga_gaga rayuwar taci gaba da shurawa a haka da daɗi a wajen miji babu sauƙi a wajen matan gida da dangin miji sam, Nanno kuwa ba'a ma magana wallahi. Duk abinda akayi ace kuskurene hatta ruwa da mijinyawa yake jidarmun ya ciccika randuna kullum sai Nanno tayi ƙofari, wata ɗaya da aurenmu Nanno ta damu akan Mijinyawa ya koma kan sana'arshi inma bazai koma Kano ba sai ya nemi abun yi ba kullum yana maƙale dani ba ina bautar dashi yadda nake so ba. Sabida a lokacin mijnyawa Babba ya koma inda yake aiki shi. Da daddare bayan mun gama cin abinci ni dashi tunda Uwatale tunda mijinta ya tafi sai dai in kai mata nata abincin taci ita kaɗai. Ai da sabida kawai a baƙanta mun in bijire yasa basu tuno da cewar mazajen namu ba mazauna bane, kunga ai gara dana biye ma abun, ba ko da taushe faɗa da hauragiya ke zama mafita ba. Sai Mijinyawa yake mun ƙorafi akan baya son tafiya neman kuɗi ya barni bisa sharaɗina, shi yasa amman Azare yake son zuwa zai ci gaba da ciraninshi acan duk sati biyu ya dinga zuwa. Jikina duk ya mutu nasan ko da muna da abinci dole muna da buƙatar aiki rayuwa ba zata ɗore a haka ba, ƴan kuɗaɗen hannun nawa babu yawa duk sun ƙare dama dai tunda nazo da kuɗaɗen muke amfani tunda shi ba kuɗi bane dashi a hannunshi ba. To amman ai Nanno ta fimu gaskiya duk da bana son kayi nesa dani mijinyawa amman dole ka fita nema, sai dai akwai kuɗi ne a hannunka? " "Shine damuwar babu kuɗi a hannuna amman inaso in nemi Aro a hannun Abdulƙadiri tunda tare dashi zamu tafi can Azaren, shi a can yake tashi sana'ar sai in dinga kama mishi kafin in samu jarin ƙashin kaina." A'a ba sai ta kai ga haka ba ina zuwa" Miƙewa nayi na shiga ɗaki na ƙirga kuɗaɗen hannuna duka_duka dubu arba'in ya rage mun. Sai na rabata biyu na kawo mishi rabi yasa hannu ya karɓa ya ƙirga. Sana'a naso in yi da kuɗin, to amman a ƙauyen na rasa gane wacce sana'ace zata karɓeni ma. To gashi kuɗi kam sun ƙare zance. "Naga har dubu ashirin ya zaki kwashe kuɗin ke da zan tafi in barki kuma" Murmushi nayi na shige ƙirjinshi ina kallon idanunshi mai kyau da kwalli nace. Akwai komai na abinci kayan miya
Chapter 53 · 0% Book details