← Book details Tsuron Tsirin Tsandauri Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 69 OF 77

Sashe 69

Tsuron Tsirin Tsandauri Part 1 Complete Hausa Novel · about 1 min read

alƙawarin da mukai ma juna fa? " Alƙawari? Ai ba faɗar Allah bace faɗarmu ce. Muje dan Allah ayi abinda za'ayi tun kafin ka tunzurani" Shiru yayi yana salati zuchiyata wani irin rawa take yi to ya zanyi tunda dai da Allah suke faɗansu ba da ni ba. Sanin kowa ne bazan iya bama kaina haihuwa ba. Allah shike da tararrafin komai da isa da kuma buwayarsa. Fitowa muka yi zuwa tsakar gidan matan gida anata ƙus_ƙus na munafurci har muka shiga ɗakin Nanno. Na zaci taro zan gani sai naga su su ukune kaɗai a ɗakin Nanno, Yaya Jamila, Yaya Zakiya sai kuma mu da muka shigo muka samu waje a gefe guda muka zauna. Sai carbi mijinyawa yake ta ja. Ni ko ina kallon kowa hankalina kwance, ai wanda ya dogara ga Allah ya gagara.
Chapter 69 · 0% Book details