Sashe 73
Tsuron Tsirin Tsandauri Part 1 Complete Hausa Novel · about 2 min read
cikin haka sai ga kira ta whatApp ɗina kamar bazan ɗaga ba dai sai kuma na ɗaga. Da sallama a bakina. Namiji ya amsa a tsanake, ya tambayeni dan Allah nice Hindu ko, na amsa mishi da Eh. "Dama dangane da wannan mar'atussaliha da kika ɗaura labarinta ne maƙasudin kiran. Ni sunana Ibrahim haifaffen garin Kano amman, yanzu ina Abuja ina sana'ar canji. Inaso in babu damuwa ki haɗani da wannan baiwar Allahn inaso in Aureta, kuma zan riƙeta harda yaran nata, amman nima ina da yarana uku mahaifiyarsu shekararta goma sha biyar da rasuwa, amman sai yanzu ne naga wacce zuchiyarsu asin da asin da matata." Wannan rana na daga cikin rana mafi girma da daraja a rayuwata a karon farko da zan haɗa Aure. Take na tura mishi lambarta ita kuma na kirata ta whatApp ɗin mai shagon da suke karɓan kaya ina tura mishi kuɗin kasancewar bata da babbar waya. Nayi mata bayanin zata yi baƙo gashi gashi Wallahi kuka ta fashe dashi. Ba'ayi sati biyu ba duka duka akayi auren ya kwashesu zuwa Abuja wai kunga gidanta? Wani hanin ga Allah baiwane, wannan darasine ga matan da suke tauye hakkin rayuwarsu sabida a nasu tunanin basu san inda zasu faɗa ba. Allah na ɗauki kalmarnan a matsayin rashin tawakkali eh na faɗa ku saka mun gas in kun so".