Sashe 6
Tsuron Tsirin Tsandauri Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Hindu: Na jima sosai ina zurga_zurga tare da murmushi na gaban mamaki. Bawai ban taɓa jin labarin matan da suka amince da mazajensu kuma sukai musu budulci ta hanyar raba tsaraicinsu ga matan waje bane. A.a Ina da youtube chanal da nake wayarma da mata kai duk da bani da yawan mabiya a YouTube ɗin nafi karkata akalata da izuwa Facebook. ina da zaure a shafin Facebook da nake wayarma da mata kai tare da ba da ginannun shawarwari dan taimakon ƴan uwa mata. A whatApp ma ina da zauruka guda biyu shima duk aikin da nake yi kenan zauren ma na kuɗine nera dubu uku ake biya kafin mace ta shiga, babu abinda bana koya musu da hanyoyin kama zuchiyar miji ta hanyar kirsa da maɗe, nice koya magana, nice koya salo _salo na kwanciyar Aure domin duhu da ƙauyanci, da kunya dake kan da yawan matanmu na Arewa yasa na zaɓi wannan hanyar dan ganin an rage yawan zinace_zinacen da mazan wannan zamanin suke yi sabida ƙorafin yayi yawa. Mata in suka kawo mun ƙorafin mazajensu na charting da matan waje suna tura tsaraicinsu, ko kuma mace tace miji inya dawo bata samun hankalinshi, wallahi ni sai inga kamar matan in da laifin mazan sai inga kamar laifin na matan yafi yawa. Ashe akwai ragowar karatun maza da ban buɗe shafin ba, sai yanzu Mijinyawa ya buɗe mun gashi ina biyawa da manyan baƙi. In dai duk kulawar da nake ba mijinyawa bai katangeshi da nuna tsaraicinshi ga wata ba, bai hanashi jin sha'awar wata ba. Babu abinda mace zata iyayi ta katange mijinta face ta miƙa ma Allah shi yayi mata maganinshi babu tsumi babu dabara sai dai mace ta gyara kanta ta kasance ta musamman domin kanta da kanta kada tayi domin burge ɗa namiji dan ba lalle ta burgeshi ba. yarinyar da bata kai mace ba saita ɗauke hankalin magidanci, yarinyar da kika fita da komai da komai fa. Hmm wai maza ku wanne irinenene, daku nake? . Kayan gyaran Aure wallahi bana ƙasata najeriya nake sha ba mafi yawanci, ina dai shan kayan sirrin tsirrai nasu Abokiyar hira da su pinkish kayansu na da inganci sosai. gyaran jiki babu irin wanda banayi, ina amfani da basarakiyar dilka ta Mrs Bukhari wacce take sanya santsi da laushin fata, da hasken fata mai kyau sirrin matan Sudan. ( Nakune mata masu daraja na haɗa muku kuzo ku sameni domin mallakar wannan dilka bata lalacewa ko shekara zata yi duk mai so tayi magana) Man shafawa mai tsada nake shafawa, haka sabulun wankana mai darajane. Turarukan jiki, kulaccham, humrori, turaren wuta na alfarma masu ƙamshin sanyaya rai na Mrs Bukhari dasu nake amfani gidana, duk da mahaifiyata tana da nagartattun turarukan wuta da take yi da kanta amman na gamsu na yadda da nagartar na Mrs Bukhari ɗari bisa ɗari. dukkannin kayan sakawana na gida cike suke da ƙamshin kabbasa turaren turara kaya da na feshi a kaya, sib ɗina kina buɗewa ƙamshi zai daki hancinki. Duk na wajen Mrs Bukhari ne fa. Ina da ƙananun kaya da rigunan bacci masu kyau da bada haɗin kan da duk akeso masu tafiyar da damuwa da sanya fara'a gani da zati na faɗa muku a baya. salon mu'amala kullum a cikin kashe kaina nake dan in faranta ran Mijinyawa. Kullum cikin ƙirƙirar girki nake in zuba kuɗina nayo cefanen da gumina dan kawai yazo ya zauna yaci yana santi. Kuloli kuwa ina dasu da yawan gaske danma ina fitarwa, nike nan cikin sake mishi kulala filet, cokali, kofin shan ruwa aikina kenan. Kullum maganarshi shine Tutar so bakya tsufa kullum kamar amarya nake ji da ganinki. Abu ɗaya nasan ya tsuro dashi shekara ɗaya kenan akan shi yanason in cire wannan tumbin nawa duk da da sigar wasan gaske yayi kalaman kuma bata hanyar zafi ko kaushi yayi furucinba cikin lalama da salama yayi maganar kuma sau ɗaya tak bai kuma ba. Wallahi kullum a cikin siyan ganyayyakin shayi nake na zaizaye kitse da tumbi dan kawai in faranta mishi yaji daɗi kawai, har motsa jiki na koya na rage tumbi dan kawai farin cikinshi. Danginshi sun tsaneni gani suke son da yake yi mini yayi yawa gani suke yi kamar asiri nayi mishi kasancewar ni Kanuri ce cikakkiya sai suke ganin ban barshi haka ba. Ni kaina nasan mijinyawa na sona babu wata iriyar sadaukarwa da baiyi mun ba a rayuwa. Farinciki harda kuɗi yake cirewa ya siyo ya kawo mun domin jin daɗina. Rayuwace babu irin sauyin da bata zuwa dashi. Yau ga sakamakon dagon ƙaunar Mijinyawa na samu. Zama nayi na ɗauki wayar naita haurawa har saida nazo farko, duk da bashi bane farkon maganar tasu ba. A hankali naita bi inajin yadda suke musayar kalaman ƙauna, da irin yadda yake mararinta da kuma irin yadda yake kushemun baiwata a gareta labarin gazawata ko da yaushe yake haska mata, ni kuma nayi imani da Allah babu ta inda na gaza bance ɗari bisa ɗari nake ba amman ni macece wacce ta yadda da kanta sharrin wasu mazanne kawai ya hau kaina nima. Abunda ya buga mun kwanyata yawuna ya ƙafe ƙaf shine hoton wacce na gani ɗin. Itace suke wannan abun da mijinyawa dama, itace take ta nanata mishi tsohuwar matarka mai tumbi da wasu kalmomi na aibantawa. Allahu Akbar duniya tazo ƙarshen ƙarshe wallahi. Saƙwannin duk na kwafe na dawo dasu kan wayata, ba tare dana karashe bi ba, ai wannan hoto dana gani ya ƙonemun jinin jikina ƙarƙaf, ya tsiyayemun man kaina tas, bani da buƙatar ƙarashe bi sam Wayar na kashe na buɗe durowar gefen gadona na jefa. A lokacin ko tsaga jikina akayi ba za'a tadda jini ba. Murmushi wanda yafi garwashi zafi nayi. Da ƙarfina na miƙe na shiga banɗaki na sakarma kaina ruwa ko kayan jikina ban samu zarafin cirewa ba, saina tsinci kaina da murmushi. Idanuna na ɗaga sama nace. Allah ga kayanka nan kai kasan yadda zaka yi dashi. Murmushi na sake yi a karo na barkate na sake kallon sama nace Ya Allah! Zuwa gare Ka nake kai kukan raunin ikona, da ƙarancin dabarata, da kuma walakancina a idon mutane.Ya Mafi jinkan masu jinkai! Kai ne Ubangijin mafiya rauni, kuma Kai ne Ubangijina.Ga wa kake barina? Shin zuwa ga bare na nesa ne da zai riƙa nuna mini fushi? Ko kuwa zuwa ga abokin gaba ne da Ka mallaka masa al'amarina?Idan har ba Ka yi fushi da ni ba, to ban damu da kowace wahala ba. Amma lafiyarka da kariyarka su ne mafi yalwa a gare ni.Ina neman tsari da hasken fuskarka—wanda duffai suka haskaka da shi, kuma al'amarin duniya da lahira ya gyaru a kansa daga saukar fushinka a kaina, ko kuma tabbatuwar fushinka a gare ni.Gare Ka nake tuba da neman gafara Ubangiji har sai Ka yarda. Kuma babu wata dabara ko ƙarfi sai da taimakonka. Ina kaiwa haka na saka hannu na cire kayan jikina na jefasu a bokiti ruwan sanyinnan ya shigeni sosai kana na ɗauro alwala na fito. In nayi sujjada sai infi minti talatin goshina a ƙasa ina magana da Ubangijina ina nuna mishi abinda akaimun. Ga adda'ar da naita nanatawa kema ki riƙeta. Zan yi haƙuri mai kyau (marar gunaguni). Kuma Allah shi ne abin neman taimako akan abin da kuke siffatawa na yaudara da ƙarya. Ita naita nanatawa Haka inna zauna zaman tahiyar da sallama zanyi nake fin minti goma sha ina ƙara nanata ma Allah halin da nake ciki. Babu fa hawaye ko sofane a idona wallahi bana jin zan iya zubar da hawaye sabida bashi da amfanin da zai mun. Ina da jarumta irinta wacce naci sunanta wato Hindu bin utbah matar Abu sufyan mahaifar Mu'awuyya. Kunsan suna akace linzamine ni na gani a karan kankin kaina Ga yadda zuchiyar Hindu ta kasance. Zuciyar Hindu bint Utbah wajen jarumtaka ta kasance mai naci, maras tsoro, da kuma karsashi na ban mamaki, ko kafin ta musulunta ko bayan ta musulunta.Malamai da masana tarihi sun siffanta zuciyarta da abubuwa guda uku: 1. Zuciya Mai Cikar Kamala Da Juriya Hindu ba ta da tsoro ko kaɗan. A al'adar Larabawa, ana ɗaukarta a matsayin mace mai "Zuciyar Maza" saboda yadda ba ta firgita a lokacin tsanani. Ko a lokacin da yaƙin Yarmouk yai ɗumi, kuma manyan jarumai maza suka fara ja da baya saboda yawan sojojin Romawa, zuciyar Hindu ba ta girgiza ba ko kaɗan. 2. Zuciya Mai Juya Akalar Mutane (Leadership)Tana da zuciya mai tasiri da kwarjini. Idan ta yi magana ko ta yi tsawa, maza ba su iya jurewa saboda kwarjinin zuciyarta. Wannan ya sa ta iya tsayar da dakaru maza da suke gudu, ta canza musu tsoro ya koma jarumtaka da kunya. 3. Sauyawar Zuciya Zuwa Ga Gaskiya Babban abin mamaki game da zuciyarta shi ne yadda ta canza lokacin da ta musulunta. Zuciyar da ta kasance cike da gaba da ƙiyayya ga Musulunci ta koma cike da kishin addini da ƙaunar Allah da Manzonsa S A W. Jarumtakar da ta yi amfani da ita da can wajen yaƙar Musulmai, ta dawo tana amfani da ita wajen kare Musulunci. Nima haka nake wallahi. Saida nayi sallar asuba kana na haye gado kaina kamar zai tarwatse ga zazzaɓi_zazzaɓi dake taso mun. Asama'u wacce ita ke bin Azgar ce ta shigo da sallama yarinya nutsattsiya kamila mai ƙoƙarin aiki, tafi Sabira aiki sosai, amman Azgar in ɓangaren girkine ya fisu iyawa. "Ammi kinyi sallah kuwa?" Ta faɗa tana kai hannunta wuyana. "Ammi zazzaɓine a jikinki sosai. Subhanallahi kiyi haƙuri Ammi Allah zai ba Abba lafiya. Mun yi sallah mun roƙa mishi lafiya. Murmushi nayi tare da rufe idanuna. Babu komai Asama'u baccine ba zazzabi ba. Kuje ke da Sabira ku gyara gida, Azgar yayi abincin da zamu tafi dashi asibiti, kuna da lekca ne da safennen?" "A_a Ammi bamu da lekca sai ƙarfe ukun yamma. Bari muje mu soma aikin. Azgar kin mance ai a asibiti ya kwana." Kai kawai na ɗaga mata. Kafin ta fita. Sabira ta gaisheni hannu kawai na ɗaga musu. Cikin minti uku bacci ya kwasheni mai nauyi bani na barka ba sai takwas na safe lokacin Sabira ta tafi sukul. Ogana na soma kira a waya na sanar dashi ina buƙatar hutun sati ɗaya sabida