Sashe 41
Tsuron Tsirin Tsandauri Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Gawata saida ya tabbatar na shige gida kana ya saka kai ya tafi. Washegari muka tashi da tashin hankali mai tsanani wanda tarihi bazai iya mantawa ba abadan. Abokin mijin Yaya Saratu yazo da safe kuma harma ance an bashi ni lamarin daya burkita ciwona naita bige bige da ihu, a ranar dai har waje naci nasarar ficewa a guje bansan ya akayi aka dawo dani gida ba. Wallahi ranar murɗeni makarai sukai ta yi yadda kuka san babu ƙashi a jikina. Sukai rantsuwar ɗaukeni zasu yi a neme ni a rasa tunda anƙi a farantama goɗiyarsu rai. Baba Soja ya dinga faɗa yana jaddadama Innarmu Aure babu fashi an riga an ba Sadisu ni ko gawatane sai an ɗaura wannan Auren da'ita an kaini a mace. Shi bai yadda da makarai ba sam amman tunda sunce zasu ɗaukeni a barsu su ɗaukeni nanne zai tabbatar da lallai makarai suna iya shiga jikin mutum. Kunji tauri da irin rashin tsoron Baba Sojanmu ko? Ranar makarai sun jijjigamun jikina sosai sai da kowa ya tausaya mun Innarmu harta sare ganin irin wahalar da nake sha, ga jikina duk ciwo ko iya tashi zaune bana yi sai su Rayya sun taimaka mun nake iya tashi. Maƙota sai shigowa suke yi domin suji menene matsalar dake damuna. Amman zancan bai sauya zane ba Baba Sojanmu ya kafe baya ko ɗigon tausayina. Mako guda da wannan maganar sai ga sadaki an kawo nawa ya ɗare na kowa harda akwatin nagani inaso. Biki aka tsaida wata biyar masu zuwa da izinin Allah an fasa batun sai mun soma jami'a an ajjiye a gefe, ƴan matan gidanmu da iyayensu sai haushina suke ji. Amare ko wacce tana cikin farin ciki saɓanin ni da a kwance nake yau ina duniyar mutane gobe ina ta aljanu. Tsakanina da Gawata sai wasiƙa wacce Luba ta zama manzo a tsakaninmu ita ke kai saƙwannin dukka. Labarin ɗayane dani dashi a halin damuwa da ciwo kawai muke rai kwakwai mutu kwakwai. Dama_dama shi yana ɗan baza kayan sana'arshi. A wasiƙar daya turomunne yake sanar dani ya dawo bakin titin layinmu da saida Lemo Innarmu tasa an koreshi a ƙofar makaranta tasa anci zarafinshi sosai an watsar mishi da kayan sana'arshi. Takaddar ban haƙuri da lallashi na tura mishi. Biki nata ƙaratowa niko duk na zube a tsaye nice kullum a shan rubutu da yi mun hayaƙi nake, hatta ruwan wankana wallahi na maganine, abinci wannan in zanci dole sai an zuba mun magani. Abun ya wuce yadda kuke tunani a rana sai makarai su bigeni sau biyu uku, sai in kwana ana guda gani dai nice amman kuma bani bace, tun innarmu bata iya bambancewa har tazo ta soma ganewa in bani bace zata ga da kuzari a jikina sosai kuma idanuna juyewa yake yi, in kuma nice babu kuzari a jikina kuma idanuna zasu dawo jawur. Ranar dai Innarmu tana makaranta Baba sojanmu yaje wani bikin wani babba da aka gaiyaci manyan sojin ƙasar. Inna Abida ma bata nan lungunmu babu kowa duk suna makaranta marasa zuwa makaranta kuma sun fita. Sulalewa nayi na fito. Wallahi duk ƴan gidanmu in suka ganni sai su shige ɗaki a guje tsorona suke yi sosai sabida abubuwan da nake yi da yawa sosai, kuma muddin na riƙe mutum ba'a iya ƙwatarshi, mahaukaciya dai na zama tuburan fa. Gashi Baba Sojanmu ya saɓule hannunshi a kaina Innarmu da ƴan uwanta ne suke ta faman nema mun magani shi kuwa ko gezau wallahi. Ina fita na nufi titi samɓal har gaban teburin Gawata yana tsaye yana ba wani lemo. "Tutar so kece kika koma haka?" Ai saiya saki ledar lemon dake hannunshi lemun suka bi titi a guje. Damƙama mai siyan lemon kuɗinshi yayi, ya dawo inda nake a zaune a benci nayi shiru, ashe a lokacin bani bace. "In ka bari Hindu ta Auri Sadisu zaku rasata dukka sai mun ɗauketa sabida kai take so. Kaci gaba da zuwa zance wajenta ko da korarka za'a dinga yi" Iyakar abinda suka ce dashi kenan na kama hanya na dawo gida na kwanta nayi lamo a kan gadonmu. Daga wannan rana kullum sai Gawata ya aiko inzo sai dai a kori ɗan aiken, ko Baba Sojanmu ya fita da kanshi yaita turanci yana yi tamkar zai doki Gawata, sai in su Baba Nagoɗi nananne sai ƙurar ta lafa. Shi kuma wannan jan kunnen da makaraina suka yi mar yake jin tsoron ranar da za'a wayi gari ace an neme ni an rasa. Bari in muku a taƙaice wuya babu wacce bamu sha ba, biki ya rage saura sati biyu tim jikina yayi tsananin da ko idanuna bana iya buɗewa ko'ina a jikina ya kumbura yai suntun. Ranar asabar suka wayi gari babu ni babu dalilina ni kaina bansan a wacce duniyar nake ba. Akai neman duniya ba'a ganni ba. Har kulle Gawata akayi a ofishin ƴan sanda akan sai ya fito dani. Makaranne sukai magana ta jikin Innarmu tunda itama tana dasu kusan na gadon gidansu ne ma ya shafeni, amman gaskiya basu taɓa tashi ba, ace har an yi magana dasu irin haka ba. "Ku bar wahalar da kanku a banza, Hindu mu muka ɗauketa tana hannunmu ba zamu dawo da'ita ba. Mu mun fika taurin kai" Baba Sojanmu yayi dariya kawai yace. "Kuna dai da kalar naku baku san kalar nawa ba. Nifa bana tsoronku bare kuyi mun barazana. Babu yadda za'ayi goɗiyarku ta auri wannan yaron ina da raina. In kun so ku riƙeta ni yafi ye mun" A wajen ya bar Innarmu da makaran yayi ficewarshi. Sai su Baba Dogara Inna Abida ta kirawo suka shiga lamarin da ƙyar suka yadda da sulhu, tare da sharaɗi. A cikin kwana na tara cib da ɓacewata suka dawo dani. Innarmu na makaranta, Baba Sojanmu baya nan ƙofarshi a kulle take da kwaɗo yana buɗewa ya ganni a kwance a gadonshi. Nan ya kikkira su Baba Nagoɗi, Innarmu ma ta dawo ta tarar da lamarin gani a kwance ni dai. Ran da alkadarin komai zai karye kenan. Baba Nagoɗi da yaga irin halin da nake ciki na rai kwakwai mutu kwakwai jikina yayi wani iri, fuskata tamkar ba tawa ba sai yace. "Na soke Auren Sadisu da Hindu, shi wannan yaron ace yazo ina son ganinshi yanzunnan a aika Rayya taje tayi kiranshi yazo maza." Ajjiyar zuchiya Innarmu ta sauke tace. "Alhamdullahi Allah yasa ƙarshen wahalar kenan amman iya wuya Hindu tasha wuya, maganin akeyi amman kamar sake turasu akeyi yadda take da kafiya haka makaranta suke da shegiyar kafiya. Alhamdulillahi tunda Ƴata ta dawo. Nima na amince da Aurenta da mai lemun" Baba Sojanmu dake zaune a kujerarshi shi Baba Nagoɗi da su Baba Dogara duk suna tsaye yace. "Tunda kaine maɗaurin Aurenta kuma ka janye da wanda kayi ma alƙawari shikenan bazan ma musu ba, amman ina da dokokin da zan shinfiɗa kuma dolensu ita da makaran subi sabida ni ba tsoronsu nake ji ba. Ba zasu maidani jani talau ba wallahi dan ka yanke hukuncine a gaban kowa amman da sai dai Hindu ta mutu uban kowa ya huta, ko su dawo su ɗauki abunsu." "Dama wannan taurin naka ne dana gyatumarta duk ta haɗa ta ɗakko shi yasa abun yayi mata yawa, ga makarai dake sake tura abun. Amman ya kamata ace ka tausayama uwar yarinyar da yarinyar harma da ƴan uwanta kullum su Saratu a cikin zirga _zirga suke dan duba jikin nata. Kwana tara yarinya bata gida, kuma da suka tashi dawo da'ita aka kawota ɗakinka aka ajjiyeta, ɗaki a rufe kuma kana da tabbacin kai kaɗai kake da ɗan mabuɗin ɗakin. Ai wannan kaɗai da suka nuna maka ya'isa ka gane makarai gaskiya ne. A dai bata abinda take so ai shikenan kanwa takar tsami ƙwannafi dole ya lafa suma da suke ikrarin zasu raba ta da cikin bil'adama sai su janye tunda kaɗanne daga cikin aikin makarai, ji yadda suka sake mata kamanninta fa. Tunda Qazzafi ya haƙura Sadisu dole ya haƙura Auren bazai haifar da ɗa mai idanu ba, kada azo ana dana sani. Kai na fahimci ba dana sanin da zaka yi a cikin damuwa mu kaɗai zaka barmu" Duk wannan maganar acan sama nake jinta tayi nisa sosai da kunnuwana. Ruwan rubutu Innarmu ta shasshafamun bayan fitarsu, ita da kanta ta mayar dani ɗakinta. Sai zuwa kallona ƴan gidanmu suke yi. Kai gidan yawa bala'i ne. "Shikenan Hindu burinki ya cika kin tanƙwara iyayenki kan abinda kike so. Ai gara a haɗaku kowa ma ya huta, kema da makaran naki ku huta. Shikenan ai marar ilimi zaki aura muna da ranmu da lafiyarmu. Bawai ban amince bane, na amince sabida inaso rayuwar Aurenki tayi kyau. Na sani auren dole ba'ayi ko a Musulunci. Ko batun uba ya nema ma ɗiyarshi budurwa miji da akace. Ana nufin ya zame mata ido, ya nema mata abinda ya dace da'ita a kawo mata ta gani, in yayi mata shikenan,in bai yi mata ba shikenan sai a nema mata wani har sai ta samu wanda yayi matan. To amman ba hakan akeyi ba, iyayenmu na da can sai an kai mace ma gidan auren take ganin mijin, amman zata zauna ta yi biyayya. Amman in mace bata so babu laifi sam danta faɗa hakkinta ne, tunda ita zata zauna shi aure amincewar mutum biyu ne tunda sune zasu yi rayuwar tare. hmmm" Tayi ƙwafa ta fice. Sanyi ne naji yana ratsa jikina takota ina, ina jin guɗa a kaina anayi da shewar mata da yawa sosai harda kaɗe_kaɗe. Cikin minti ashirin idanuna suka buɗe tangararan sai dai a kumbure suke ainun. Innarmu ce ta shigo. "Hinduwa taso iyayenki na nemanki a falon Nagoɗi." A hankali na miƙe nabi bayanta zungui_ zungui har zuwa falon Baba Nagoɗi. Ƙarfin haline kawai amman ji nake inna taka ƙafata tamkar zata ɓalle. Ina kuma jin yadda iska ke shiga har ɓarona, a haka na kai kaina da kaina. Zama nayi nesa da Gawata amman muna fuskantar junanmu yana saye da yadinshi fari ɗinkin ƴar shara da hularshinnan da kuka sanshi da'ita itace ɗaya_ɗaya "To kai ganaral sai ka soma bayaninka da zaran na gama. Gawata kace sunanka ko? " "Eh Baba sunana kenan" "Kana da sana'ar da zaka iya riƙe Hindu da'ita