Sashe 20
Tsuron Tsirin Tsandauri Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
ɗayarma ba musulma bace. Kuma dole ka kutsa kaima kayi taka tambayar ka tura bututun magana domin naɗewa. Nasha wahala ranar sosai, amman dake abinda nake sone wahalar bata dameni ba, kuma gwagwarma shine abun burgewa na farko mafi girma a rayuwata, ni nafi sha'awar abubuwa masu wuya. Al'amura haka suka ci gaba da cukurkuɗewa ana cikin haka Zara'un Inna Abida ta haihu nanma mukaita sunturi, mun gama da wannan Baba Nagoɗi ya kwanta a asibiti shima muka ɗaura, ga aikin rahoto aikine na yawo sosai har gari_gari inta kama sai kaje ƙauyuka kuwa babu inda bana kutsawa duk Mijinyawa fa bai sani ba. Ranar wata asabar sunje Jama'are da yara sun dawo ina falo a zaune ina kallon labarai a NTA labaran tara sai gasu sun shigo. Sannunku da dawowa ya hanya? " A gajiye ya amsa mun. "Hanya Alhamdulillahi mun sameki lafiya? " Lafiya ƙalau ya aka baro su inna da Nanno? " "Kowa lafiya sunce a gaisheki ma" To ina amsawa, ya Asama'u take? " "Lafiya lau take tama samu gurbin karatu." Miƙewa nayi na soma fito da kayan abinci ina jerawa a ƙasa. Duk muka baje a ƙasa tuwon semo nayi da miyar karkashi bushasshe yana son miyar sosai. Tun daga lokacin dana ga wannan aika aikar muka raba kwanon abinci. Muna ci ina hira da yara shi dai na ganshi sanyi ƙalau. Mun jima muna hira a falo dan sai wajajen goman dare ko wannensu ya wuce ɗaki zasu yi wanka su kwanta. "To bari inje in yi wanka ki sameni a ɗakina zamu tattauna muhimmiyar magana" To kadai yi wankan ina falo sai muyi maganar" Kallona yayi yace. "Da gaske guduna dai kike yi daga ni har ɗakina Tutar so. Mijinyawanki nefa wanda kullum dare kina maƙale a ƙirjina" Dariya kawai nayi fur naƙi binshi dole yaje yayi wankan ya fito saye da jallabiya fara. A inda ya barni ko shurawa banyi ba. Zama yayi a ƙasa inda ya tashi. "Hindu" Naji ya ambata. Na tabbatar wannan magana babu wasa a cikinta tunda ya ambaci sunana. "Wata ƙaddarace ta hau kaina nima bansan da maganar ba saida naje Jama'are Nanno ta kawo mun zancan. Akan dai rashin sake haihuwarkine take ta ƙorafi akan yara biyu gashi sun girma shiru abokaina sunata hayayyafa. Shine ta umarceni da ƙarin Aure.... " Sai ya ja fasali, ni kuma ko ɗar banji ba a zuchiyata domin nasan dole sai anzo wajen kuma tunda ya kwaso baragadarsa nasan akan Aure zai sauketa. Murmushi nayi mishi kawai ina saurarenshi ya ƙarashe. Sai kallona yake yi da gaske har cikin zuchiyata banji komai ba ganin hakanne yasa yaci gaba. "To shine dole na amince mata nan da kwana arba'in za'ayi bikin. Amman wallahi Hindu" Sai nayi sauri ɗaga mishi hannu muƙus yayi da bakinshi. Mijinyawa rantsuwa ai ba taka bace babba gareka. Sannan ƙarin Aure ba laifi bane Ubangiji shi ya baku wannan damar, bin umarnin Iyaye wajibine Allah ya sanya Alkhairi. Ni bacci nake ji zanje in kwanta" "Amman baki tambayeni wacece wacce zan Auran ba? " Dariya nayi nace. Akwai buƙatar hakan ko? Ai dake naga Aure dai kaine zaka ƙara nauyinta da komanta ai kamar a kanka yake ba kaina ba ko" Kai ya gyaɗa halamun eh akwai buƙatar in santa ɗin, harna tashi saina koma na zauna. Wallahi saida muka kusan zarce minti goma sai zaiyi magana sai ya fasa, ni kuma idanuna ƙur a kanshi, da ƙyar dai yace. "Asama'unki tace in Aura, kiyi haƙuri dan Allah ban karɓa dan in tozartaki ko inci zarafinki ba wallahi. Matsawa Nanno tayi dole hakan take so ayi. Ni kunya da damuwa duk ta aureni wallahi. Shin da wanne idanu duniya zata kalleni ne? Naso in fahimtar da'ita Asama'u ɗiyace gareni babu Aure a tsakaninmu ubane ni sosai a wajenta, amman ina. Kuma babu macen da zata iya kamoki matsayi a zuchiyata na sani da zafi amman kiyi haƙuri ki taya ni muyi ma Nanno biyayya." Sokiburutsunshi tun ina iya ji har kunnuwana suka dena ji sakamakon hankalina da baya wajenshi. Irin girgizar da zuchiyata tayi har abada bazan mance ba, ga girgizar abinda suke aikatawa, ga sabuwar girgiza. Kuma na ƙudurce daga yau baccina na ƙarshe kenan da zanyi a gidan Mijinyawa. Miƙewa nayi cikin dakiyar zuchiya tare da nuna halin ƙi faɗi cikin halin ko in kula nace. "Allah ya bada zaman lafiya" Juyawa nayi nayi shigewata ɗaki da ƙyar nake ganin hanya. Ina jinshi yana bina tare da ƙoƙarin cin mani yanayi yana kiran sunana. Ina shiga ciki na bugo ƙofata na jingina bayana a jikin ƙofar, ɗakin na juyawa dani. Ji nake kamar in bar gidan a daren in tafi gidanmu. Amman ina ba lokacin bane, ba yanzu na tsara abinda zan yi ba tukunna dai. Tsugunnawa nayi da rarrafe na isa bakin gadona sabida inason lafiyata ji nake yi zan iya faɗuwa. Allah naita ambata kawai ina jina kamar ba ni ba, yarinyar dana ci kashinta naci fitsarinta na koya mata tarbiyya, tasan sirrina ciki da waje itace za'a auromun a haɗani zaman kishi da'ita bayan ya gama kwashe mata albarkatun jikinta, kuma ya gama watsar mun da darajata. Kuma wai ni yake ma ƙaryar umarni aka bashi. Hmmm oh dalilin da yasa aka ɗauketa daga gabana kenan ashe a matsayin kishiya za'a dawo mun da'ita? Kunji sabon shafin da mijinyawa ya buɗemun alhalin ban gama biya wancan ba. Dan Allah zaku ga laifina inna soma buɗe mishi nawa shafukan kuma nayi mishi rinto? Hmmm ambaton Allah shi ya ragemun nauyin ƙirjina sai nake jin kamar zan hau iska tsigar jikina sai buɗewa take yi. A taƙaice saida na sha wahala cikin wannan daren da ƙyar nayi bacci makaraina ina jinsu a kusa_kusa. Amman da gari ya waye saina dawo cikin hayyacina sabida tsabar ƙarfi da tasirin ambaton Allah da salatin ma'aiki Arrasul SAW. Tashi nayi na gabatar da sallah, na rasa wacce adda'a zanyi sabida nayi adda'a a daren jiya kamar babu yau. Sai kawai nace. Allah ga kayanka kai kasan yadda zaka yi dani" Ina kaiwa haka na miƙe na shirya tsab duk da zuchiyata ciwo take yi mun amman fa a fuska babu halamun rauni ko damuwa tattare dani. Dama masu suna Hindu jarumaine kuma suna da bushewar zuchiyata ga kafiya. Bushewar zuchiyarne yasa Hindu matar Abu Sufyan kafin ta musulunta ta saka wahshi ya kashe mata Sayyadina Hamza ta ciro hantarshi ta ci. Fitowa nayi na tadda Mijinyawa a zaune a falo da shirinshi na zuwa office tsaf. Ina kwana" Na furta ban jira amsarshi ba nayi ficewata ina jiyoshi kamar biyoni yake yi dashi da yaran. Sai kawai naga su Uwatale suna leƙowa ana nunani da baki. Wannan abun sai ya zamemun tamkar fitilar data haskamun hanya, take tunanina da ƙudurin dana fito dashi a zuchiyata ya sauya salo. Da sauri na isa harabar gidan kafin su zo harna tashi matota maigadi ya wangalemun get nayi ficewata da mugun gudu. A tsaye nabarsu a wajen in sunga dama kada Allah yasa su je makarantar shima kada yaje aikin. Takwas da rabi na ƙarasa Na'ibawa na ajjiye motata a kusa da Motar Akarami na shiga gidan da sallamata. Anata hada hadar karyawa ko wanne Lungu cike fam da hayaniya. Haka naita shiga ina gaishesu a ɗakin Inna Abida nake jin labarin samarin gidanmu mutum biyu an saka ranar bikinsu wata uku masu zuwa. Murna na taya su dan nasan bana ma ƙasar za'ayi bikin. Innarmu na tarar ita da Akarami yana juya mata masa.