Sashe 77
Tsuron Tsirin Tsandauri Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
nuna mishi har suka iso bakin tangamemen gidan auren Halima. Hon ya matsa mai gadi ya wangale musu get suka shiga da rana ƙata. Halima ce ta leƙo daga babban Kitchen ɗin tsakar gidan nasu ta hango ɗiyarta a bayan mota. Ba shiri ta nufo su. "Mijinyawa ita da bata da lafiya shine kuka yo miƙaƙƙiyar tafiya haka ko ita tace zata zo? " "Kamawa tayi Halima zamu iya shigowa ciki mu yi magana?" Cewar Qasimu. "Zaku iya nan gidan ai ba baƙonku bane, Mijinyawa maigidan ma yana ciki mujenku" "To kafinnan akwai kayayyakin ita Asama'u a baya a sa yara su shigo dashi" Jim Halima tayi jikinta a sanyaye tasa yara suka soma shiga da kayan ciki. Kishiyoyinta nan suka fito suna tambayar baƙi akayine. "Au Asama'u Amarya kece da angon naki? " Cewar uwargidansu Halima. A sanyaye aka gaisa kowa babu laka a jikinshi dai. Suka shiga falon suka tadda mijin Halima yana zaune yana shan shayi da dambun nama yana kallo, ga turaren wuta na tashin hayaƙi a hankali. "Asama'u kece a tafe akace kina asibiti babu lafiya ko? " Cewar Alhajin Halima. Miƙa ma mijinyawa hannu yayi suka gaisa, ya kuma miƙa ma Qasimu ma. Asama'u ta gaishe da mijin gyatumar tata sai falon ya ɗanyi shiru. "Lokacin sallah yayi muje masallaci kafin mu dawo Halima a ajjiye mana abinci" Fita suka yi masallaci suka je suka dawo, sun kuwa samu tuwon shinkafa miyar zogale an ajjiye musu. Sosai mijinyawa ya take cikinshi yasha zoɓo sosai kana yasa akayi kiran Halima ita da mijinta. Qasimu dai jikinshi duk a mace. "Dama ga Asama'u nan na dawo da'ita hannunki. Kamar yadda na ɗauketa tana shekara ɗaya da rabi ne ko biyu na mance dai. Gata na dawo miki da'ita zanci gaba da ɗaukar ɗawainiyarta har illa masha Allah amman ta zauna a hannunki. Qasimu a gabanka na sa hannu na karɓi Asama'u, yanzu a gabanka na dawo ma da Halima ɗiyarta. Sai yayi shiru. Alhaji yace "Bamu gane ba, to mijinyawa Auren kuma fa, ko dai abun yaƙi daɗine? Duk da ba abun daɗi bane a wajen mata ba, ka kuma sansu da kacalcala zance. Ni kaina a lokacin da Halima ta zo mun da zancan auren haƙiƙa na kaɗu" "Hakane, zama kam bazai yiwu ba Alhaji na sauwaƙe mata inta samu yaro daidai ita tayi aurenta" Hannu yasa a aljihu ya ciro takaddar ya miƙa ma Halima. Idanunta sun kaɗa sun yi jawur dasu tasa hannu ta amsa tace. "Amman ka cuci yarinyarnan mijinyawa cuta mai girma. A matsayinka na uba, in mahaifintane ya auri Sabira yai mata irin wannan sakin tozarcin zaka ji daɗi? Yarinya tunda ka aureta babu abinda ya shiga tsakaninku, Hindu ta asirceka, ta shanyek, ta hanaka rawar gaban hantsi, nan Saratu Yayar Hindu tayo tattaki har nan tazo ta zauna ta ci mutuncina yadda take so duk sabida aurannan. Aure kuma ku kuka sasanta kanku babu wanda yayi muku dole, kuma naga ba haramun bane. Yanzu yaya zanyi da Asama'u Alhaji kana ji fa" Mijinyawa baice da'ita komai ba amman yaji zafi sosai da maganganun data yaɓa ma Hindunshi. Ta ɗauki zafi sosai har da yi mishi adda'ar in sha Allah sai an yi ma Sabira abinda yayi ma Asama'u. Ya harzuƙa ainun amman kuma yasan duk shi yaja har Halima ke mishi rashin kunya haka. "Halima batun alkaba'i baima taso ba domin Allah. Ni tun farko da mijinyawa ya ɗauki shawarata da ba'a zo wannan munzilin ba. Babu ta inda Auren Asama'u zai haifar da ɗa mai ido. Ke kanki son zuchiyarki kika bi, amman ai Hibdu tafi ƙarfin haka a wajenki. In kika duba irin riƙon da taima ita Asama'u. A dai karɓa da Haƙuri kawai." "Ya'isa Halima shi aure raine dashi fa. Ni tun farko auren bai kwanta mun ba, kuma naso in yi miki tarin tulin tambayoyi baki bani damar hakan bane. Yarinya ayi mata fatan alkhairi. Shi kuma ayi mishi godiya a bisa ɗaukar ɗawainiyarta da yayi tsawon shekaru" "Naji ya tashi ya fita ko a lahira bana fatan sake haɗa idanu dashi. Kuma kada yayi tunanin sake yin wata hidima da Asama'u tana da gata ba irin yadda take tunani bane. Allah ya isa tsakanina da Hindu" Halima fa ta shaƙa har saida tayi kwakwazon da abokan zaman nata suka san halin da ake ciki. Alhaji ya ja Mijinyawa da Qasimu har cikin motarshi. "Kayi haƙuri kasan Halima ni kaina haƙuri nake yi da'ita. Hatta abokan zamanta haƙurin suke yi da'ita. Dan Allah kuyi haƙuri in da hali ka daure ka mayar da Asama'u ɗakinta mana" "Babu damuwa na fika sanin halaiyar Halima ba tun yanzu ba. Halin dawo da Asama'u babu shi har abada ayi haƙuri kawai" "To shikenan babu komai ka gaida yaran da kowa da kowa" Nan sukai sallama ya fito a motar, mijinyawa da Qasimu kuma suka kama hanya. Sai yake jin kamar an sauke mai wani gingimemen dutsene a kanshi. Ya kashe wannan ɓangaren amman yasan ya bar baya da ƙura ko yaya zasu kwashe da Nanno kuma bai sani ba, ga kuma Hindu daya fi kowa sanin irin taurin kanta da kafiyarta. Duk da haka cikin nishaɗi da nutsuwa yake tuƙinshi har ya shigo kano da daddare sai hira yake zuba ma Qasimu Sai dai me zai biyo baya?
Mrs BUKHARI
_Idan kika sai littafinnan nawa mai suna TSURON TSIRIN TSANDAURI tamkar kinyi sadakane kai tsaye a asusun marayu._
_Littattafaina kuÉ—insu sadaukarwane ga iyayen marayu har zuwa ranar da zan dena rubutu._
_Ko nawa kika cire kika saka marayu zan yima hidima dashi wallahil azeem ko kuÉ—in Data bana cirewa a kuÉ—in littattafaina, marayu kaÉ—ai nake yima hidima._
_Saima ƙarawa da nake yi da kuɗin kasuwancina akan kuɗin da littafi ya samar mun._
_Kuzo ku siya mu samu ladan marayu tare daku, ga lada, ga karatun littafi Hajiya._
_Wannan link ɗin na ƙasa ɗaya ne daga cikin aikin da nake yi da kuɗin wajen hidimtama marayu, shafin gidan Rediyo, da talabijin na ZINARIYA TV jos ne suka ɗaura domin sun kai ziyara a lokacin da aikin tallafin yake gudana._
_Nayi hankane ba dan riya ba sai dan ina cewa marayu nake ma hidima da kuɗin, amman ku baku taɓa gani ba, shi yasa wannan karon na zaɓi ku gani, daga yanzu kuma zaku dinga ganin dukkan aiyukan da nake yi da kuɗaɗen littattafaina, hakan zai ƙara mana ƙarfin guiwa
__Daga É—ari bakwai zuwa sama yadda kike jin zaki iya zubawa baki faÉ—i ba saima romon lada da zamu samu a tare_
_Mu tausayama marayu wallahi marayu suna cikin wani hali na ni ƴasu, har jari ina tallafama da iyayen marayu jarin ƙananun sana'a domin dogaro da kai_
Nagode sosai son so