Sashe 35
Tsuron Tsirin Tsandauri Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Washegari da safe muna É—akinmu muna karyawa su Yaya Saratu suna gwada kayan da aka karÉ“o musu na cin biki daga wajen tela. Ni kuma ina zaune inacin masa da aka saba kamar kullum, shi ne dai abincin karyawan babu ranar fashi kuwa. Jinjin kuma a tsaye take tana karatunta, Akarami kuma yana zaune yana kurÉ“ar shayinshi. Muka jiyo muryar Inna Mairamu ba shiri Innarmu tace. "ÆŠakko zanin gadonnan ku rufe kayannan, maza ke ciro É—ankwalin kanki, saida nace dama ku bari saida daddare ai kun san yanayin gidannan sarai" Da sauri Jinjin dake tsaye ta yayimo zanin gado ta rufe kayan. Babu sallama kuwa Inna Mairamu ta faÉ—o haka akeyi a gidanmu dan son ganin Æ™waf, kai gidan yawa ko babbar masifa. "Ruwayya barka da safiya, ahh amare ana karyawane? " Nan muka gaisheta kana ta miÆ™o mun ledar hannunta. "Duwaf gashi Qazzafi ne ya turo kuÉ—i aka sai miki kayan ango harda ma kuÉ—in É—inki dana liÆ™i a ciki shine na kawo da kaina. Qazzafi dai ya dage wallahi kamar kamar wasa tun da Æ™uruciya, mu mun É—auka duk wasane to abu dai na shirin tabbata" Ƙin karÉ“an ledar nayi sai Akaramine ya karÉ“a yana mun dariyar mugunta. Innarmu tayi jim kafin tace. "Mairamu ni ina ganin da Qazzafi ya bar wannan hidimar ya samu soyayyar Hinduwa tukunna, sabida bana son rigimarki ba iyawa zanyi ba. Kar azo ana kai ruwa rana... " "Haba Ruwayya ai Qazzafi ba Æ™ashin yarwa bane menene a ciki ma dan yayi hidima da Æ™anwarshi? Zasu daidaita ma tunda ai banga wani na zuwa wajenta ba. Karfa ki mance sabida Hinduwa Qazzafi duk falonnan naku yayi dabdalarshi, tunma ina hanawa harna miÆ™a wuya. Kusan kaf Æ´an matan gidannan samarinsu sun sai musu Anko banda ita dake bata da kowa sai Qazzafin dai" Kallonta kawai nayi na kawar da kaina. "To shikenan angode kiyi mishi godiya" "Ai babu komai yima kaine Ruwayya" Daga haka ta fice abunta. Yaya Soja wanmu ne shima ya shigo ya taddamu su Yaya Saratu sai babbaka dariya suke yi akan Qazzafi da irin Æ™arfin halinshi da uwarshi. "Innarmu wannan dariyar da yarannan suke yi ta meye harda Saratu fa? " "Uhm kaga wai Qazzafin NagoÉ—i ne yayo ma Hinduwa anko ya dage ita yake so, ni dai har cikin raina bana son wannan haÉ—in yadda Mairamu take da gadararnan sannan mu ba zaman daÉ—i muke yi ba, waye baisan jaraba da tatarar jarfa a wajen Mairamu ba" Yaya Soja yace. "Ai a irin taurin Hindu da murÉ—aÉ—É—en halinta Soja ne ya dace da'ita ya kaita bariki ta koyi hankali, in allurarshi ta motsa ya jibgeta." Ai kuwa wallahi bana sonshi bazan taÉ“a saka kayan daya kawo ba sai dai aba Jinjin nima yau za'a kawo mun nawa ankon ai, da take cewa bata taÉ“a gani anzo wajena ba zata gani kuwa yau" Dariya suka kwashemun dashi ni kuwa ko gezau naci gaba da cin masata. Saratu ta buÉ—e kayan harda su É—ankunne da sarÆ™a da dubu uku na É—inki sai dubu biyar na manni Æ´an goma_goma sababbi. Ai kuwa Innarmu na gama karyawa ta fita da kayan ta zagaye gidan dashi tas tana nunawa hakan ya sake Æ™ular dani, da wannan É“acin ran nakai har dare. Tun yamma na cancara ado nice harda shafe jikina da humrar Innarmu ba wacce muke shafawa ba. Yaya Saratu ce ta shigo itama taci ado wanda zata Aurane yazo. "Ke kuma sai ina kinyi zuchiya saurayi zai soma zuwa zance ne? Ai kuwa kinma kanki alamnashara in ba haka ba Qazzafi zaki Aura yarinya, gashi da rashin fara'a ko a cikin sojoji wallahi Qazzafi zai yi mugunta. Kuma duk bala'in Innah Mairamu haka zata zama surukarki" Dariya kawai nayi mata na gama shafe_shafena ina zaune ina jiran shigowar yaro. Ga isha ta kusa yau muna da karatu da Baba Sojanmu. "Assalamu Alaikum wai ana kiran Duwaf inji Gawata" Wani daÉ—ine ya lulluÉ“eni É—an halak yaÆ™i ambato ashe yana hanya. Ina jiyo Innarmu daga babban falo tana raÉ—a mun kira. Da sauri na fito riÆ™e da mayafina. "Maza kije ana kiranki kada ki wuce minti goma sha biyar" Maki take yi a littattafan Æ´an makaranta inna Abida ta taÉ“e bakinta tace. "Qazzafin kuma ko yaya za'ayi dashi oho ni Abida. Lallai ashe akwai yaÆ™i da mairamu a cikin gidannan" "Saita tara rundunar yaÆ™inta ku kenan tun yanzu ai Abida sabida Hinduwa dai allurace a cikin ruwa mai rabone kaÉ—ai zai É—auka. Kuma ce miki tayi tana son Qazzafin ne ko ke zaki bashi tunda ai Æ´arki ce ko? " Innarmu mafaÉ—aciyace bata da kawaici bare barin ta kwana kullum cikin rikici ake da'ita kuma tana yawan nuna musu gadara da isa sosai, domin tana jan zarenta kasancewarta mace mai ilimi cikin kishiyoyinta, gata da tattalin miji, kuma tana da kuÉ—inta daidai gwargwado ga koyarwa, ga kasuwancin sutura da take yi. Itace tilo a cikin iyaye mata dake aiki, itace mace tilo dake da ilimin boko, kana itace mace tilo mai mota a gidan. Gaskiya idanu yana kan Innarmu da yawa, koma ince idanun kowa a cikin gidannan a kanmu yake baki É—aya. Ba Æ™aramin hassada, da kishi suke yi da Innarmu ba. Gashi duk surutar da zata siya mana mai tsadace, mune yara na farko a gidan da muka soma saka zinare, hatta É“ulukan hancinmu zinaraine Innarmu ta saka mana, haka kunnenmu. Daga nan matan gidan suka soma siya ma yaransu suma. Akan É“ulin hancinmu kuwa ansha artabu da É—auki babu daÉ—i. Su Innah Abida sune Æ´an gaba_gaba masu cewa. "Æulin hanci duka ramukan hancin biyu sai kace wasu karuwai, wannan ai sai ayi musu mummunan fassara kisa a haÉ—a harda yaranmu." An sha gumurzu danma Baba Sojanmu tsayayyene sosai shi yasa maganar ma ta wuce. Ni dai ratse gidan namu nayi na fita. A raÉ“e a gefe can hagu da gidanmu na hango Gawata a tsaye da ledarshi baÆ™a yana saye, da yadi mai ruwan omo a jikinshi da hularshi tashi ka fiye naci, wasu na kiranta tashi ka fiye Æ™waÆ™wa É—aya_ É—ayar hular da tun sanina dashi da'ita na sanshi. Ina Æ™arasowa na jiyo Æ™amshi turaren Alhaji Abdullahi a jikinshi yana tashi sai murmushi yake faman yi. "Tutar so Allah ya nufa yau gani a Æ™ofar gidanku, ina fatan wata rana ki kasance a cikin nawa gidan. Barkanki da dare, wannan shine karona na farko dana ganki ba'a kayan makaranta ba. Sai kika sake yin kyau zatinki ya fito sosai, ashe yadda nake hasashenki kin wuce haka" Dariya kawai nake yi mishi. Bamu jima muna hira ba yace. "Yana da kyau ki shiga gida, ga kayan ankonki nan da duk abinda za'a buÆ™ata yana ciki kiyi haÆ™uri da kuÉ—in da zaki tsinta a ciki babu yawa a yi haÆ™uri." Mai yawan kenan akace kwabon masoyiya yafi nerar maÆ™iyi kuma ai nasan baka da Æ™arfi. Amman zaka zo mana party da zamu yi ko, ko wacce saurayinta zai zo bana so a barni a baya? " "In kika gayyaceni ban isa inÆ™i zuwa ba. Allah ya nuna mana lokacin zan zo miki Tutar so in haka zai faranta miki kuma zai fitar dake" Albishir É—in da zan zanyi maka daga yau kaci gaba da zuwa gidanmu zance, lokaci yayi da É“oyeka zai iya haifarmun da matsala Gawata. Amman duk sanda zaka zo dan Allah kazo ana idar da magriba sabida bayan isha muna karatu da Baba Sojanmu" Yayi murna sosai fiye da yadda nake tunani. Ana kiran sallah yaimun sallama yace zai tafi in yayi sallah zai koma inda yake kwana sai kuma gobe in yazo. Naso in tambayeshi ina yake kwana dan wallahi bansan a inda yake kwana ba sam. Da murna ta na shiga gidan saina tarar ana É—auki babu daÉ—i da Inna mairamu da Innarmu ga kayan da Qazzafi ya kawo har Innarmu ta watso mata su suna gabanta a barbaje. "Ga tsiyarku nan. Hinduwa ma ba zata taÉ“a auren Qazzafi ba ko da tana sonshi, ai Æ™addarace kaÉ—ai zata sa ai surukunta dake Mairamu, matan da zasu zo a surukanki ma wallahi abun a tausaya musu ne" "Lallai Ruwayya kin samu waje dama ai kin riga kin shanye har Soja ballantana Su Abida da kika maishesu ababen takawarki. In sha Allah sai Qazzafi ya cika burinshi na auren Hinduwa domin É—abbaka zumuncin da burinki kiga ya ruguje. In kuwa bata aureshi ba abadan ba zata samu kamarshi ba in sha Allah. Mata sai girman kai da É—aga ma mutane kai sabida kawai kina koyarwa a kanki aka soma koyarwane, ko a kanki mace ta soma fita aikine" Innarmu tace. "Ko ba'a soma a kaina ba, a gidannan dai a kaina aka soma. Ilimin da nake dashi kuke ma baÆ™in ciki, kuma wallahi na shige da saninku, ko yanzu aka Æ™ara mata Æ´ar boko a gidannan sai dai ace itace ta biyu bata É—aya ba. Wawuya jahila" "Yayi kyau Ruwayya matar wan nawa kike kira da Jaliha ko? " Cewar Baba sojanmu daya iso shi da Baba NagoÉ—i da Baba Lukumanu. "To ita Mairamun ba ita tazo ba duk abinda akayi mata ai ita taja. Ke Hinduwa shige mu tafi ciki" Innarmu taja hannuna muka shige ciki. Ina jiyo Baba Sojanmu na faÉ—a da hargagi a falon an rasa mai tanka mishi. "Allah ya kyauta, Mairamu kwaso kayan muje. Tunda yarinya bata son Qazzafi sai yayi haÆ™uri ai. A gidannan ba'a Auren dole kuma kinsan dai Soja bai isa da Ruwayya ba illar Auren Æ´ar bokon kenan shi ya kasa ganewa burinshi ayi boko ayi boko, duk ya mayar mana da yara Æ´an boko ya hure musu kunne suma bokon suka fi so, gasunan duk a wahale sunata sunturin zuwa makaranta" Cewar Baba Nagodi kenan. Mairamu ta tattare kaya da kuÉ—in tabi mijinta suka tafi. Mu kuma Baba sojanmu ya soma kiran a fito ayi karatu. Littattafaina na É—auka na fice abini. Nan nabar Innarmu na Æ™irga kuÉ—in da Gawata ya zubo a cikin ledar dake na fasa asusuna na Æ™ara kuÉ—in a cikin ledar a zatona ba wasu kuÉ—in kirki ya sako ba, ashe kuwa yayi bajinta. Sai da muka gama karatunmu muka dawo ciki Innarmu tace. "Dubu goma cib ya zuba miki a ciki Hinduwa gaskiya yayi Æ™oÆ™ari sosai ya fitar dake kunya sabida babu Æ´ar da aka