Sashe 47
Tsuron Tsirin Tsandauri Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
sa yaro irin wannan kashe kuɗi haka duk yawanku ace da shayi da madara harda mummuƙi zaku karya da ƙosai? " Innah Abida tace. "In da ma basu kawo ba kinga ko wacce lalitarta a cike take sai mu ciyar da kanmu tunda mu ba mitsiyata bane. Su da suka je namu gidan haka akayi musu ko haka akayi musu? Wa zaici wannan shinkafar" Hatsaniya dai ta ɓalle duk da batai nisa ba su Akarami da suke tsakar gidana sun shiga maganar kuma duk su biyun kayan sojojine a jikinsu. Ai na rage muku sai shigowa kallonsu Akarami akeyi tun sakkowarsu garin sabida an gansu da kakin soja. Anata tambayarsu a waje suna cewa su yayu nane. Haha ƙauye garin su kare shima kare da aka tambayeshi yace kaishi akayi, wannan kakin Sojoji ya sake ɗaga daraja a Jama'are bayan na lefena. Bayan duk an gama karyawa dangin Innarmu suka kamo hannuna muka shiga cikin gidan domin inje in gaishe da Nanno da ragowar matan gidan. Gidan a tumbatse yake sosai kasancewar yau buɗar kai, muna tafe suna gaisawa da jama'ar biki har zuwa shiyyarsu Nanno a falonta suka dureni aka gaggaisa babu fara'a sam a muryar Nanno nasan har a fuskarta ma babu yadda naji muryarta a daddaƙile. Nan dai aka shiga yi mun nasihohi akan in zauna da kowa lafiya. Aka kira Shafa matar babban wansu wanda suke zaune a gidan ta zazzagaya damu tun daga kan kishiyoyin Nanno har izuwa surukan gidan su su tara tare da matar Nawata mutum goma kenan saini ta sha ɗaya. Har ɗakin Amarya aka kaini a cewar Shafa ai itama matar wan mijinace dole in bita in mata biyayya kunji fa. Haka mukai sallama muka shiga tana ɗakin gadonta daga ita sai ƙawayenta wani gadone na ƙarfe mai madubai dunƙulallu na fulani kun ganeshi? Yauwa to shine a ɗakin gadonta yasha zanin gado sule ango ruwan hoda irin bau dinnan kun gane sule ango ai? Wani zanin gado da ake yayinshi da wanda ko jingina akayi a jikin gado zai sulalo ya faɗo ƙasa to shi. Sai sib ɗinta bango guda da wajen kwalliya sai jeren kuloli da kicin waya harda kofuna tarkace dai harda randar shan ruwansu baƙa mai giwa ƙarama, duk fa a uwar ɗaki, na zaune baiga gari ba. "Uwatale ga matar ƙaninki nan mun kawo miki, nasan taku saita fi zama ɗaya ɓarayinku yayi kusa kuma tare aka auroku gashi kune yaran mata a gidan sai matar Rabi'u." Buɗar bakin uwatale tace. "Ayya Amarya Allah ya bamu zaman lafiya da haƙuri da juna. Amman ni ai matar Rabi'u ce ƙawata Yaya Shafa" Anan ai kun gane mai take nufi ko? Nan muka tashi muka koma nawa ɓarayin a lokacin anata shigar da kaya ciki an gaggama malala kafet mai ruwan bombota turarre a ƙasa ciki da waje wasu na jera kujeru wasu na kafa gado har sib an shiga da'ita. A gefe na zauna ni da su Luba. "Hinduwa kinga ƙauyen kuwa jibi gidan fa da zaki zauna kiyi rayuwa ke da aka haifa a maraya, jibi matan gidan ƴan ƙauye fituk dasu ga ɗan karen nisa ke kuwa Hinduwa" Luba kenan ai babu komai babban burin ɗiya mace ta samu miji nagari nagartacce wanda zai riƙeta da mutunci watarana in sha Allah zamu bar ƙauyannan ko Bauchi saimun koma" "Hmmm da kamar wuya jibi fa Shafa take ko wa harma ta tsufa amman ba gasu suna zaune ba sai kece za'a bari ki janye Gawata. Batun ci gaba da karatunki da cikar burinmu na son zama ƴan jarida ma'aikatan tv ko rediyo gaskiya gurine wanda bazai cika miki ba ki haƙura ki watsar da karatu kawai. Kuma sai kinyi da gaskene zaki fita daban a cikin gidannan wallahi in ba haka ba sai kin dawo kamarsu ba tare da kin sani ba. Ni da naga Rabi Nass da tai aure a ƙauye ita da take Kaduna a cikin ƙanƙanin lokaci hatta fatarta saida ta sauya ke kinga wai yaranta ma kuwa hmmm" Duk da haka babu karaya tattare dani ni bana kwan gaba kwan baya gaba gaɗi nake lamurana in eh ne to eh ne haka in a'a ne to a'a ne. Murmushi kawai nayi mata bance mata uffan ba. "Hinduwa zo kiga falonki babu masaka tsinke baifi mutum uku suyi sallah a ciki ba kinsan kujerunki manya ne" Hannuna ta ja muka shige ciki. "Kinga yadda suka yi, kuma uwarɗakin naki ma dake shida da bakwai ne gadonki shima babu waje ko za'a mayar da kujeru biyu ne can gida ko a bar miki haka? " Innah Yahanasu tace. "Tunda sun zauna a bar mata su kawai kayan kallonma sun zauna komai sai a bari haka Allah dai ya bada zaman lafiya kawai, babu wuta ma sai dai in ci gaba ya riskesu za a ja musu. Amman kayan Kitchen da durowar turare guda ɗaya, da su teburin tsakiyar ɗaki dole zamu koma dasu. Hatta zannuwan gado zamu koma da wasu. Ko da yake tunda tana da ɗaki daban a rage kaya a jera a ɗayan ɗakin kawai in yaso ko Bauchi kwa shiga a siyo kafet a malala duk da akwai tarin tulin gara da za'a zuba a ɗakin" "To shikenan Innah a barshi hakan shikenan. Amman batun wani kafet a barshi kawai a tura mata ragowar kayanta shi ɗakin da za'a saka mata garar a ciki kawai. Ƙawayen Amarya ku nemo mana rushi a cikin gida ya kamata asan kanuri aka kawo cikin gidannan tunda an gama dandatsa jere" Ni dai ɗakin na shige na tadda su Qazzafi sunata haɗa zufa suna aikin zaman sib Qazzafi ya ɗago ya zuba mun idanunshi da gaske ina kallon so na a idanunshi asalima tsananin sonne yasa ya biyoni har ɗakin Aurena rakiya. Kaina na kawar na zauna a bakin gado. Da aka gama gyara komai kujera ɗaya ta samu shigowa ƙurya kuma tayi kyau. Nan da nan aka banka turaren wuta namu na gangariya, Ga na Mrs Bukhari ma na siya Amarya package dan turarenta ƙamshinsu na musamman ne, wani irin ƙamshin fadar larabawa nata suke yi, kunsan turare fa iri iri ne wallahi ko Innah Yahanasu data ɗan ɗauki itace ɗaya ana mrs bukhari ta saka a gaushi ta gane kayan kamfani daban dana shago, ta bashi maki sosai kuma ta jinjina ma mrs bukhari, harma nake tsokanarta da cewa ai itama Kanuri ce ta ɓangaren mahaifinta Waɗanda suke siyen kayan ƙamshin mrs bukhari su baku labari wallahi, ƙamshin turarenta ba iya labule da kafet yake kamawa ba hatta bango wallahil azeem yana kama ƙamshi gida ya riƙe ƙamshi ƙaƙas ( in kin siya bai miki ba ki zo in mayar miki da kuɗinki) Su wannan bama yanzu zan soma amfani dasu ba sai ranaku na musamman, zan dai turare uwarɗakina kafin ango ya shigo. Unguwar baki ɗaya ta ɗauki ƙamshin daɗi. Akarami da Qazzafi dai wajajen azahar sukai mana sallama suka tafi Dubu ashirin ashirin suka bani cikin rashin jin daɗin rai na rabuwarmu muka rabu Qazzafi sai rarrashina yake yi idanunshi sun tara ruwa kamar zai zubar mun da hawayen ƙauna, yana ji yana gani kamar wasa ya rasani. Tausayina cike da yanayinsu, ni kuma ina mamakin yadda suke ta tausayamun Innah Yahanasu ana zaune kawai sai ta hau sharar hawaye da an magana sai tace tausayin yadda zasu barni take yi. Allah buwayi