← Book details Tsuron Tsirin Tsandauri Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 58 OF 77

Sashe 58

Tsuron Tsirin Tsandauri Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

yadda na dinga kwatanta mishi ta dinga fitowa tsakar gida ayi hira da'ita sai shima ya dinga kwatanta mun a barta tunda haka tafi so na lura tsoronta yake ji shi kanshi bijirema umarnin shi take yi. Girkin haɗakar da suke yi ma da uwatale na soke shi kowacce tayi abunta, dama uwatale tace tunda ta samu ciki take hassada abincinma bata yi sai ta yi niyya wani sa'in sai dai taci a wajensu Shafa. Ke kuma Hindu in dai kina son zaman Aure na gaske to dole ki riƙa fitowa tsakar gida ana hira dake duk abinda ya tashi ayi dake in ba haka ba wallahi zaki koma inda kika fito ni dai na faɗa miki kenan. Sannan kada ki sake kunna risho a gidannan ko ruwan zafi ban lamince miki ki dafa a risho ba, sabida baki fi kowa ba a cikin surukan gidannan kuma duk a itace suke girkinsu. Ki tashi kije na sallameki ragowar bayanin zan ƙarashe da yarana" Miƙewa nayi ko a kwalar rigata na shige cikin ɗaki ina rantsuwar in dai dole saina fito tsakar gida anyi munafurci dani wallahi sai dai auren igiyar ta tsinke, ta daɗe bata tsinke ba. Kuma ban ba da haƙuri ma kowa ba, sabida babu abinda nayi ma kowa wallahi. Duk da fa ina mugun son mijinyawa kuma gani nake yi dole sai dashi a cikin rayuwata rayuwar zata yi mun kyau. Amman kuma bazan wulaƙanta kaina, ko in yi abinda bazan iya ba. Kitchen na shige na tattaro doyar da bai gama soyawa ba na fito tsakar gidan na hura wuta naci gaba da suyan. Nayi shiru ina sauraren zuchiyata ina tunano ƴan gidanmu yau gashi a sanadina a gabana ana aibanta mun Innata wacce bani da kamarta. Ko dai a bakin Inna Abida suka ji cewar Innarmu ta mallake Baba sojanmu ne, dan naga Inna Abida ta shige dangin Mijinyawa da suka zo sosai. Ni dai harna gama komai na maida sanwar rana mijinyawa bai shigo ba sai wajen sha biyu sai gashi ya shigo ni kuma ina tsakar gida nayi shiru ina tunanin rayuwa da makomar aurenmu in ban samu ciki ba. A lokacin har girkin rana na gama na kwashe a filas. A haka ya shigo ya sameni ya zauna daf dani jikinmu na gugar juna. "Kin karya ina fatan ko? " Ko kusa ya zan karya alhalin kasan in kana nan tare muke karyawa?" "To zuba mana maza mu karya zanje maganar benci da za'a buga mun da rumfar shayi ne da zafi_zafi ake dukan ƙarfe" Saida na zuba mana muka soma ci kana nace. Ka sanar da Nanno ta amince ne da zaman naka kar hakan ya sake zama wata damuwar fa? " "Ba wannan ba sharrin da uwatale tayi miki yafi komai damuna Tutar so dan nayi imani da Allah babu abinda zai sa kiyi hassada da cikin jikinta" Murmushi kawai nayi na tura doya a bakina bance komai ba dan na ƙullace uwatale da Yaya Jamila sosai sun shiga littafina da nake adana mutanen da suke ƙina. Wannan ya wuce sai aka dawo maganar kafa teburin shayin mijinyawa. Nan aka yi mun ca a kaina, wannan ta zageni wannan ta aibata mun iyayena, maganganu harda maƙota akan na shanye mijinyawa baya son fita gari aiki shi yasa ya zaɓi ya zauna anan tare dani. Akan wannan maganar ma ciwona ya tashi yafi a ƙirga a lokacin ne aka haɗa mijinyawa da mai magani dake Azare yake zuwa karɓo mun rubutu da na hayaƙi. Babu dama dare yayi aimun hayaƙinnan babu bacci ranar na dinga ihu da tambotsai kenan, masu ganin makaran na ƙaryane ai dole suka amince na gaskiya ne dan a cikin kwana bakwai saida halittata gabaki ɗaya ta sauya hatta kamannina saida suka canja na dawo wata iri na kumbura idanuna a ciki kamar an huda sakwara. A lokacin mijinyawa shi kanshi babu nutsuwa tattare dashi ishasshen bacci wannan baya samun yi, ya kuma dage akan bazai iya dinga zuwa birni aiki ya barni in ciwona ya tashi babu mai kulawa dani ba. Ana cikin haka kawu da matanshi suka zo dubani da jiki harma ya tawo da magani shima hayaƙin ne dai da na sha da wanka yace in anji daɗinshi sai mu zo ya kaimu. To a wannan zuwanne aka samu masalaha kawu yace Nanno ta ɗauke idanunta akan mijinyawa da matarshi, a halin da nake ciki bai kamata ace ya tsallake ya barni ba tunda bani da kowa a ƙauyannan. Nan dai ala tilas ta haƙura ya kafa teburin shayinshi. Nanma kuma zama a teburin ya gagareshi ciwo babu dama duhun almuru ya ratsa sai ciwo ya tashi har da gudu nake fitowa. Rannan anyi haka da magriba shima na danna da gudu zan fita Mijinyawa babbane ya riƙeni da ƙyar ya shigar dani ɗakina aka tura yaro yai kiran mijinyawa. Nanno sai faɗa take yi wai dama ansan mahaukaciyace ni shi yasa aka liƙa ma ɗanta, ita ta gaji ya ɗaukeni ya mayar dani gaban iyayena aimun jinya mana. Shi kuma bai nuna gajiyawa ko gazawa ba, duk inda magani yake zaije ya karɓo mun ya kawo mun, sai nayi kamar lafiya zata ɗore, sai abu inya tashi motsawa yafi na da. A haka mijinyawa yaji labarin wata macce mai bada maganin jinnu ai kuwa da safe yace mu shirya mu tafi. Tare muka shiga ɗakin Nanno tana zaune tana karyawa. A gefe na zauna na gaisheta, ta amsa harda tambayar jikin nawa. Dan rannan ta shigo tana faɗa, ni kuma ina kan ganiyar abun. Sai na kamo zaninta ta ƙugu. Ba shiri ta sunce zanin ta danna a guje, Allah yasa ma tana da gwari na tsuma ta ciki. Shine ta ɗan sassauta. "Jikin dai gashinan amman bama samun bacci sam yanzu ma Abdul ƙadiri ne zai kaimu can wani ƙauye a cikin ɓoto wajen wata mai magani ko Allah zaisa a dace" "Ya dai kamata kam dan in abun yaƙi dole ta koma gaban iyayenta ayi mata jinyar acan tunda wannan lalurar da'ita ka aureta ba a gidanka ta samu ba. Ni da naje wajen Malam Idi ma nayi mishi bayanin lalurar ita Hindun. A gaskiya cewa yayi ma biri boko akayi mana, ba'a Auren mace da irin wannan ciwon ba tare da amincewar dangin mijin da za'a Aura ba. Da kuma shi mijin da za'a bashi ba. To in ma ba'ayi haka ba. Iyayenta su ne a haƙƙu su nema mata lafiya ba kai ba. Wahalar da kake yi tayi yawa fa. Uwatale ma ta dawo nan ɓarayin namu tana ɗakin Ladi tace firgita take yi cikin dare in makaran matarka suka tashi to abunka da mai juna biyu kar su shiga jikinta su sake ɗan cikin nata su mayar mata da ɗan ruwa. Kasan suna yi ai" Murmushi mijinyawa yayi kawai mukai mata sallama muka nufi ɓoto bisa jagorancin Abdul ƙadiri mahaifin Asama'u fa. Daga ɓoto muka hau mashin saida mukai tafiyar awa uku a acaɓa kafin muka isa ƙauyen akace mun makara sai dai mu karɓi lamba gobe sai mu zo sassafe. Lambar ma lamba ta sha uku muka samu. Kwatsam muna isowa ƙofar gida a Acaɓa muka tarar da motar gidanmu isowarsu kenan Yaya Saratu da Innarmu sai Akarami da Yaya Zubaina, da Jinjin. Nayi farin cikin ganinsu gaya su kuma sun tsorata da ganin yadda na lalace. "Hindu ciwo kika yi ne haka duk kika tsiyaye?" Murmushi nayi ma Innarmu kawai. Mijinyawa sai ɓare_ɓaren jiki yake yi kamar zaima Innarmu sujjada amman ita tani take yi bata ma ta tashi. Hannunta naja muka ɗunguma cikin gidan da sallamarsu suka shiga. "Maraba baƙi muka yi ne da yammancinnan? " Cewar Shafa kenan harda fara'arta kamar gaske. "Baƙine mahaifiyar Hindu ce da yayunta, shi Yaya Akarami ai kun sanshi Soja dashi aka kawo Hindu" Innarmu ta gaishe da matan gidan aka gaisa faram_ faram kamar dai gaske. Mijnyawa yace. "Innarmu muje ku gaisa da Nanno dan Allah" Innarmu bata ce komai ba tabi bayanshi muka wuce ɓarayin Nanno su, Yaya Jamila ma tana nan. "Maraba baƙin birni muka samu ne mijinyawa kaddai surukan naka ne?" Cewar Inna Ladi kenan bayan sun gaggaisa sai mijinyawa yace. "Mahaifiyar Hindu ce da Yayunta" "Allah sarki ga kamanninan sai dai ita doguwa sosai masha Allah. Ku shiga ciki bari a kawo fura" Shiga muka yi ɗakin Nanno itama harda fara'arta ta tarbi Innarmu aka gaggaisa a mutumce sosai. "Dama nazo ganin ɗakine wata nawa da Aure nace ya dai kamata mu biyo sahu muga halin da take ciki, nayi tunanin in tayi wata shidda zai kawota taga gida sai muka ji shiru shine muka biyo sahu" Cewar Innarmu kenan. Nanno tace. "Mu anan dake sai yarinya ta shekare a ɗakinta take zuwa ganin gida, wata ma sai dai a kaita wankan gida ma, to ita ko cikin ma babu tukunna wallahi" Ta ƙarashe tana dariya amman magana ta caka ma Innarmu, ita kuma a matsayinta na wayayya malamar makaranta sai tayi murmushi tace. "Allah sarki ai gara su more ƙuruciyarsu kafin yara su soma zuwa. Mu dake a birni sai yarinya ta shekara uku a ɗakinta ma batai haihuwar fari ba. Yarjejeniya ma akeyi tsakanin mata da mijin, shi yaronki ya san da hakan. Bari muje mu huta mun shawo hanya" Murmushi nayi dan na mugun ji daɗin martanin Innarmu. Garzayawa muka yi ɓarayina sai kallon gidan Innarmu take yi tana taɓe baki. A tsakar gidana ta tsaya ƙiƙam tana ƙarema murhuna kallo kafin ta ɗauke idanta daga murhun ta dawo da kallonta gareni. "Hindu rayuwar da kika jefa kanki a ciki kenan irin rayuwar da soyayya da taurin kai suka zaɓar miki kenan? Jibakki yadda kika rame kika ƙwanjame da jin yadda surukarki take yaɓo maganganu na tabbatar ba zaman daɗi kuke yi ba" Innarmu mu shiga ciki dan Allah gidannan cike yake da munafukai. Mu yi a ciki dan Allah" Gabaki ɗaya jikkunan ƴan uwana duk ya mutu murus wallahi. To ina fatan kafin tafiyar Innarmu Allah yasa kar a rabu dutse a hannun riga ita da Nanno. Dan Innarmu ba kanwar lasa bace sam.
Chapter 58 · 0% Book details