Sashe 16
Tsuron Tsirin Tsandauri Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read
ya wanke mun ita fes yana gogewa sai naji sanyi da tausayinsu kuma. Gaisheni yayi nayi mishi godiya tare da shi mishi albarka. Na shiga motata na fice a gidan. Shikenan zuwa anjima sai suci karensu babu babbaka gidan daga su sai su in sunga dama kada su rabe in suka haɗe. Idanu na lumshe kawai na ƙudure a raina inna dawo zan karɓi wayar Asama'u inga ta inda suka soma wannan alaƙar waye ya soma ra'ayin wani cikinsu. Da wannan tunanin na ƙarasa gidan rediyo na gabatar da aikina tamkar babu matsala tattare dani nice harda daɗa kwantarma da Luba hankali da take faɗamun asabar zata tare a sabon gida asabar ta sama kuma auren Sunusi. Na bata shawarwarin da saida ta saki ranta Alhalin ni ƙirjina da kaina kamar zasu tarwatse haka nake jinshi. Na dawo gidan na tadda Mijinyawa da Azgar da Sabira Asama'u na makaranta. Sai bayan magriba na ɗakko wayar Asama'u daga caji a ɗakinsu, na shiga ɗaki basa nan suna wajensu Yaya Jamila. mijinyawa ma yana can suna hirar zumunci wai gobe zasu koma. Zaman shirshen nayi na shiga manhajar Whatapp ɗin Asama'u saƙonshi ne a farko an rubuta Sikari Shiga nayi ina girgiza kaina na dinga haurawa sama har nazo farko, da dukkan halamu nata saƙwannin cikakkune. Asama'u ita ta soma tura mishi da saƙo kamar haka. _Allah ya sani Abba na daɗe ina jin sha'awa da mafarkin ganina a manne a faffaɗan ƙirjinka ka matseni. A kullum mafarkina kenan kuma ina fatan ya tabbata ya zama gaskiya. Nima ka sammun soyayyarka ko da kwatan_kwatan wanda kake ba Ammi ne. Haza wassalam daga Asama'u mai mafarkinka ko da yaushe_ Yawu na haɗiya mai ɗaci da kauri, lallai yaran zamaninnan idanunsu a mugun buɗe yake in ubantane zata rubuto mishi wannan saƙon, yanzu duk wahalar da nayi da Asama'u ta rasa abinda zata yi mun sai farautar mijina? Duniya tazo ƙarshe. Ga amsar mijinyawa _Haba Asama'u shaiɗan ke ƙawata miki ni kawai aini ubane a gareki har gaba da abada mafarkinki a iyakar duniyar mafarki zai tsaya_ Sai ya tura mata. Sai ta sako mishi gwaigwai ɗin kuka da hawaye. A haka dai taita jero mishi kalamai kusan kullum, har ya soma jin daɗin hira da'ita tun tana batsa yana jin nauyi har ya dena jin nauyi. Sai kawai ya tura mata da hoton mazantakarshi yana nuna mata a cikin halin da yake a daidai lokacin. Shikenan ya buɗe mata ƙofa saiga bidiyonta ta turo mishi tana wanka ruwa da kumfa na sauka a jikinta. Da_ haka_ da haka _dai ashe a Hotel suke haɗuwa ya jagwalgwalata yadda yaso sai dai bai taɓa shigarta ba amman yana saka hannunshi dai. To yanzu roƙonshi da take yi ta nace shine ya kwanta ita da'ita tagaji da jan ran da yake yi mata. Shima kuma yana so amman dai ba'a je can wajen ba. Yana jin nauyi a haka dai har suka haɗa ranar da zasu haɗu Abinda ban gani ba shine shin sun haɗun sun biya buƙatar juna, ko kuma basu haɗun ba? Babu lallai bare tilas in gani a chart. Allah al hakim iyaye saifa mun dage mu dunga bin diddigin yaranmu, mu dasu babu ɗaga ƙafa mu dinga bincikarsu tamkar yadda mai kaya ke buncike ɓarawo, sannan mu dage da adda'a wallahi mu hana idanunmu bacci muita roƙon Allah ya riƙa mana akan tarbiyyarsu. Hotuna da bidiyon tsaraicinsu Allah yayi yawa dasu a cikin wayar. Kwafe komai nayi na tura a cikin wayata, daga wayata na adana a na'urata laptop jiri ne kawai yake tamaule dani ina tsantsar mamakin mijinyawa ashe raguwar zuchiya gareshi baya iya sarrafa zuchiyarshi akan mace kenan, ashe maza haka suke da rashin tsoron Allah da yawansu? Hmm Babu komai ( Dan Allah kuyi haƙuri kalmomin sunyi tsauri da yawa aimun afuwa yanayi ne yazo da hakan)